Gyaran Kafa Maganin Faso Da Kaushi

 Gyaran Kafa Maganin Faso Da Kaushi



 kada ki kuskura kibar kafarki da kaushi.ko faso.zanin gadonki ya dinga kama kafarki.wasu zasu ce akwai faso na.ciwo wasu kuma suce fatarsu ce mai gautsi.to ai ana neman maganin kaushi da fatso.akwaina Hausa.akwai na asibiti.saiki zabi wanda zakiyi amfani dashi.don illar kaushi da faso bata saya anan kadai ba.don yana ragewa mace ni'ima sosai.to ko don wannan a nemi magani.ki kulada abubuwan da zasu kara miki ni'ima da nishadi.

Ga kadan daga abubuwan daake gyara kafa tayi laushi.tayi kyau sosai.wasu matan rashin tsabta ce.yayinda wasu matan hallitace.haka koma dai menene ga mafita.

A sami kofi yana na ruwan khal a hada da lemon tsami.sai a shafe kafar.kullum.sau biyu.a rana .bayan an wanke kafar da minti sha biyar .sai a shafe ta da zaitunza aga abin mamaki.

Ruwa sanyi da gishiri a tsoma kafar a ciki zuwa minti sha biyar.sai a wanke .a shafa zaitun.amma sai kafafun sun bushe.

Hanyoyin Gyaran Faso Da Kaushin Kafa

Fason kafa ya kan zamewa mutane karfen kafa musamman ma a lokacin sanyi, ko a yankunan da suka fi bushewa fiye da wasu.

Wannan ya na faruwa ne saboda fatar kafa ta fi ta sauran sassan jiki bushewa kuma tana bukatar kulawa ta musamman wanda yawancin lokuta ba ta samu.

Rashin kula da faso ka iya ta’azzara shi ta yadda zai iya fara jini, ko ciwo ko kuma kwayoyin cuta su shiga ciki.

Ga wasu hanyoyi biyu masu sauki da za’a iya magance wannan matsala.

Hanya ta daya: Amfani da Ruwan Kal (Farin Vinegar ko Apple Cider Vinger) 

Za a zuba ruwa a cikin babbar roba, sanna a zuba ruwan kal kamar 1/4 na Kofi daya

Sai a jika kafar a ciki na tsahon minti 10 zuwa 15

A yi amfani da Dutsen kaushi wajen gurje fatar da ta jiku, sai a yi amfani da farin ruwa wajen dauraye kafar.

Bayan a goge ta da tawul mai tsafta, sai a shafa man kwakwa, ko Zaitun ko kuma man Kadanya.

Za a maimata sau uku a sati

Hanya ta Biyu: Amfani da baking soda

Za a zuba ruwa a roba mai fadi

Sannan a zuba cokali uku na baking Soda a ciki

A saka kafar a ciki na tsahon minti 15 sannan ayi amfani da sutsen kaushi wajen gurje ta.

A dauraye da farin ruwa a goge ta da Tawul mai tsafta

A shafa mai

Shima ana maimatawa kamar sau uku a sati.

Za a iya samun baking Soda a guraren da ake sayar da kayan hada Cake ko kuma Manyan shaguna ko Supermarket, Shi kuma ruwan Kal an fi samun shi a Supermarket.

Post a Comment

Previous Post Next Post