Amfanin Kabewa Da Lafiyar Jikin Dan Adam
Kofin dafaffiyar kabewa (gram 245) ya ƙunshi
1, Calories: 49
2, Fat: 0.2 grams
3, Protein: 2 grams
4, Carbohydrates: 12 grams
5, Fiber: 3 grams
6, Vitamin A: 245% na Abubuwan Rarraba Kullum (RDI)
7, Vitamin C: 19% na RDI
8, Potassium: 16% na RDI
9, Copper: 11% na RDI
10, Manganese: 11% na RDI
11, Vitamin B2: 11% na RDI
12, Vitamin E: 10% na RDI
13, Iron: 8% na RDI
14, Ƙananan adadin magnesium, phosphorus, zinc, folate da yawancin bitamin B.
Bayan cike da bitamin da ma'adanai, kabewa kuma yana da Yawan adadin Abinda kuzari Yake Bukara saboda yana Kunshe da kashi 94% na ruwa.
Har ila yau yana da yawa a cikin beta-carotene, carotenoid wanda jikinka ya juya zuwa bitamin A.
Haka kuma, 'ya'yan kabewa Ana ci, Suna gina jiki kuma suna da alaƙa da fa'idodin kiwon lafiya da yawa.
Kabewa ya ƙunshi abubuwan da ake amfani da su na antioxidants alpha-carotene, beta-carotene, beta-cryptoxanthin da sauransu da yawa, waɗanda zasu iya kare ƙwayoyin ku daga lalacewa ta hanyar radicals kyauta.
Kabewa yana da yawan bitamin A da C, wanda zai iya taimakawa wajen bunkasa tsarin rigakafi. Samun bitamin E, Da baƙin ƙarfe ( Zinc ) da folate na iya ƙarfafa rigakafi.
Hakanan masana sun bayyana cewa, kabewa na kunshe da wannan sanadaran amma ba su taka kara sun karya ba, sanadaran sune, magnesium da phosphorus da zinc da kuma folate. Sai dai duk da haka cin kabewar zai iya samarwa mutum wani adadi na wadannan sandarai wadanda suna da tasiri ga lafiyar jikin bil'adama.
Daga cikin amfanin kabewa ga lafiyar dan adama akwai:
1. Inganta Lafiyar Zuciya
Sinadaran potassium da Vitamin C da na Fiber, da Allah ya albarkaci kabewa da su, na taimakawa wajen baiwa zuciya riga kafin kamuwa daga cututtukan da kan shafi zuciya. Hakanan akwai wani sanadari na maganesium da ta ke da shi. Sai dai kamar yadda masanan su ka bayyana ana samun wannan sanadari a Ya'yan kabewar, saboda haka mutum zai samu wannan alfanu na amfanin kabewa ne idan zai ci Ya'yanta musamman ace mutum ya samu 1/3 wato (daya bisa uku) na kofi, ya ci a kowacce rana. Babu wata matsala wajen cin 'ya'yan kabewa, saboda ba su da wani dandano marar dadi, hasali ma gardi ne da su.
2. Bunkasa Garkuwar Jikin Dan-adam
Allah Ya yi wa kabewa baiwa da wani sandarin 'beta carotene' da jikinmu ke mai da shi ya koma sanadarin Vitamin A, bayan mun ci kabewa ke nan. To shi wannan sandari ya na kara karfin garkuwar jiki.
Tun a farkon wannan makala mun bayyana cewa, Allah Ya yiwa kabewa baiwar sanadaran da ake kira da zinc da iron da folate da kuma Vitamin E, a turance. Su wadannan sandarai na ba da gagarumar gudunmawa wajen inganta lafiyarmu ta hanyar bunkasa wa ko karawa garkuwar jikinmu karfi. Mun san kuma ita garkuwar jikinmu ce ke da alhakin bai wa jiki kariya daga kwayoyin cutar da ke kawo wa jiki farmaki.
3. Saurin Warkewar Rauni.
Kabewa na kunshe da sanadarin Vitamin C mai yawan gaske a cikinta, kamar yadda mu ka fada a sama. Shi wannan sanadari na Vitamin C, na taimaka wa wajen kara adadin kwayoyin halittar jini da ake kira "White blood cell" da turanci wanda shi kuma ke kara karfafa tsarin garkuwar jiki da za ta haifar saurin warkewar rauni.
4. lafiyar Ido
Idan mai karatu bai manta ba a sama mun yi maganar sanadarin 'beta-carotene' da jiki ke samar da Vitamin A daga gare shi. Baya ga aikin Vitamin A da mu ka ambaata a sama, hakanan Vitamin A na taimaka wa wajen inganta lafiyar ido kuma ya kara karfin gani.
Bincike ya nuna cewa, rashin sanadarin vitamin A ko karancinsa a jiki ne ke haddasa, raunin gani ko ma mutum ya makance baki daya. Sakamakon haka tun da kabewa na da wannan sanadari ba shakka za ta taimaka wajen inganta lafiyar ido da karewa mutum daga makanta ko raunin gani.
Hakanan dai kabewa na da sandaran Vitamin C da E ma su yawan, wadanda ke wani aiki mai ban sha'awa a jiki, inda za su iya bai wa kwayoyin halittar ido kariya daga lalacewa.
5. Kabewa Na Rage Kiba/Teba
Duk da cewa, kabewa na dauke da snadaran gina jiki ma su yawa, amma duk da haka ta na da karancin sandarin 'Calories', saboda haka ne ya sa, masana ke lissafa kabewa cikin dangin abince mai rage kiba. Masana sun ce, mutum zai iya cin kabewa da yawa, kuma cin ta da yawan ba zai haifar ma sa da girman tumbi ba.
6. Gyaran Fata
Ba shakka kabewa na gyara fatar jiki ta shi laushi da haske. Baya ga haka wasu da su ka san aikin kabewa kan fata na yi mata kirari da "Mai da tsohuwa yarinya", saboda yadda matukar mutum ya lizamci shan kabewa, to shekarunsa ba za su nuna a jikinsa ba.
7. Kuzarin Jiki
Har ila yau, daga cikin amfanin kabewa ga lafiyar dan adam akwai samarwa da jiki kuzari. Idan ka na son samun wannan fa'ida ta kabewa ga yadda za ka/ki yi. Ka samu kabewa ka fere ta ka yayyanka sannan ka markada ta sai ka hada da Goba ko Ayaba ka tace ka dinga sha lokaci zuwa lokaci. Wannan hadin na taimakawa wajen kara kuzari ga jiki da maganin gajiya
8. Karfin Mazakuta
Ba shakka yawan shan kabewa na kara wa namiji karfin mazakuta sannan yana inganta maniyyi da kara yawansa a jikinmu. Baya ga haka an bayyana cewa, shan kabewa na hana saurin kawowa yayin saduwar aure.
Kabewa yana cike da abubuwan gina jiki kuma duk da haka yana da ƙasa da adadin kuzari 50 a kowace kofi (gram 245). Wannan ya sa ya zama abinci mai gina jiki. Hakanan tushen fiber ne mai kyau, wanda zai iya inganta sha'awar ku.
9, Kabewa shine tushen tushen potassium, bitamin C, fiber da antioxidants, waɗanda aka danganta su da fa'idodin lafiyar zuciya.
Post a Comment