Hadin Zai Taimaka Miki Jikinki Yana Kamshi Kamar Turare

Hadin Zai Taimaka Miki Jikinki Yana Kamshi Kamar Turare




Da farko a zuba lalle a tukunya a sa ruwa, a dora a wuta ya dahu sosai, sai a sauke, a tace, sannan a cire garin lalle gefe sai a mayar da ruwan kan wuta, a rage wuta sai a kawo madarar turare na sandal bakhur, damarar Ledus da madara Musk, sannan a bari ya tafasa sosai, sannan a sauke, in ya huce ki nemi jarka ko galan mai cin lita hudu ki juye a ciki, duk sanda ki ka yi wanka, in kin gama sai ki kawo wannan hadin ki zuba kadan a bokiti, sai ki kara ruwa kadan sai ki dauraye jikinki da shi, kar ki goge jiki ki bar shi ya bushe, za ki sha mamakin yadda kamshin zai zauna a jikinki.

Sannan kuma ku zamto masu yawan mu’amalla da turare a koda yaushe, in har kun san baku da hanyar wadannan to ku zama masu yawan sa turaruka a wurare shida kullum a jikin ku.

Bayan kunnenku

Dantse

Sharaba

 Wuya

kasan nono da sauransu.

Gaban ku kuma ku dan samu auduga ku jikata da madarar misk (Aisha) sai a dinga matsi dashi, haka zaisa shima gabanki (farji) ya dinga diban kamshi duk lokacin da maigida yakai ga wurin.

Macen da take so ta riqa yin qamshi mai xaukar hankali sai ta nemi:

Kafi amarya qamshi

Garin ambar.

Garin miski.

Garin kaninfari.

Kafun-kafun.

Sai ta cakuxasu a cikin baslilin (Vaseline) ta ringa shafawa. Duk inda kika je to gurin zai dinga qamshi ba za'a so ki tashi ba.


KULA DA KIBAR JIKI


Kula da kibar jikinki abu ne mai tasirin gaske wajen kara miki lafiya da kyau. Sannan tara kitse a jiki na daga cikin manyan abubuwan da suke haifar da manyan cututtuka kamar cutar suga [diabetes], hawan jini [hypertension] da dai sauransu.

Hanyoyin rage kiba da samun lafiyayyen jiki:

Cin nama kadan. Ka maida nama ya zama kadan cikin abincinka maimakon ya zama da yawa.

Ka nemi madara mara mai ko kitse da yawa. Ka rage abinci da ya kunshi nono ko madara mai yawa; maimakon haka, yi amfani da mara kitse da yawa.

Lura da ciye-ciyen ki. Ka zabi kayan ciye-ciye marasa mai da yawa. A maimakon haka ka rika cin karas , busassun abinci, da ganyaye a madadin masu mai da yawa kamarsu soyayyen dankali.

Rage mai da ya jike sharaf a girki. Yi amfani da ruwan mai a madadin busashshe.

Ki rage amfani da manja da mankoko. Yawancin wannan mai yana jike ne, amma yawancin wannan suna dauke da kitse sosai. Yi amfani da man suya, da sauransu.

Rage abinci mai kitse. Yi kokari kaci abinci dake da mai kasan 200 mg a kowacce rana. Rage cin kwai zuwa guda hudu a sati.

Ki kara yawan abinci mai bada karfin jiki. Kara abinci mai kawo karfi – kamarsu ‘ya’yan itace da kayan gona, da abinci masu kwaya da ya hada da wake busasshe, da suke da abubuwan Karin karfi

Kici ‘ya’yan itace da ganyaye. Domin kiyaye zuciyar ka, kaci ‘ya’yan itace da ganyaye.

Kayi amfani da kwayoyin hatsi. Kwayoyin hatsi na rage cututtukan zuciya. Suna cikin kayan lafiya na jiki, kuma hanyar samun abinci mai gina jiki, amma yi hankali domin suna kawo kiba.

Kara yawan kifi cikin abincinki. Kasashe masu yawan cin kifi suna da raguwar mutuwa daga kowacce damuwa, haka ma daga cutar zuciya.

 Akwai wata ‘’yar na’ura ko damarar ‘tummy trimmer’ da mata ke amfani da ita domin rage kibar tumbi; idan an sanya wannan abu za a rage yawan ci, sannan a rage kibar tumbi.

WARIN JIKI

Warin jiki na daya daga cikin abubuwan da ke janyo tsana a tsakanin jama’a, musamman lokacin zafi, idan aka hada gumi ko aka yi yawo a rana sai warin jiki ya rika tashi. Akan samu warin jiki ne saboda yanayin gari ko an haifi mutum da shi ko kuma ta irin abincin da ake ci. Kamar masu yawan cin tafarnuwa daga sun motsa sai an ji warinta.


Hanyoyi mafiya sauki da za ki bi don magance warin jikin:


Turare: Yawan fesa turare na jiki ko na hammata ko na tufafi na magance warin jiki. Amma ki sani yawan amfani da turaren jiki da ko na hammata na sanya kuraje fesowa. 

Sabulu da ruwa: Hanya mafi inganci wajen magance wannan matsalar ita ce, amfani da tsaftataccen ruwa da sabulu, don yin wanka kamar sau uku a rana, kuma ki dage wajen wanke lungun da ke janyo wari kamar hammata da sauransu.

Wankakken tufafi: Kada ki manta duk yadda mutum ya kai ga wanka idan tufafin da yake sanyawa masu datti ne, to lallai ba zai rabu da wari ba. Don haka ana son ki rika sanya tufafi mai tsabta musamman wanda ake sanyawa a ciki, kamar dan kamfai da rigar mama da sauransu.

Amfani da sinadarin alam: Idan warin jikinki ya kasance mai tsanani ne, to sai ki rika sanya sinadarin alam a ruwan wankanki kafin ki yi wanka, hakan zai magance miki warin jiki.

Zuma: Bayan kin yi wanka za ki zuba kamar cokali daya na zuma a ruwan dumi, sannan ki watsa a jiki, hakan na rage warin jiki.

Shan ruwa: Domin rage warin jiki, za ki iya shan kofin ruwa daya da sassafe kafin ki ci wani abu..

 Amfani da ruwan Rose: Za ki iya diga ruwan rose water a cikin ruwa kafin ki yi wanka, hakan na rage warin jiki da kuma kara wa jikin kamshi.

Post a Comment

Previous Post Next Post