Bayan Aure Abu Na Gaba Da Ake Tsammani Shine Haihuwa

 Bayan Aure Abu Na Gaba Da Ake Tsammani Shine Haihuwa



Galibi cikin al'ummar mu baƙaƙen fata dake yankin mu na AFRICA ciki harda gida Najeriya da anyi Aure zaka samu cikin ƙwarin guiwa, karsashi da ɗoki Ma'auratan suke na ganin cewa sun kai ga nasarar samun juna biyu atsakanin su, Ba kuma iya juna biyun kaɗai ba... A'ah abinda junan biyun zai samar musu a ƙarshe shine babban burinsu 'wato' a haifo lafiyayyen yaro ko yarinya.

Juna biyun fari ga sabbin ma'aurata nada muhimmanci ta hanyoyi da dama, hasali ma shine babbar alamar farko dake tabbatar da cewa wannan ma'auratan lafiyayyu ne, wato masu haihuwa ne, kowa lafiya yake tsakanin Matar da Mijin.

Sannan cikin fari ka iya samuwa nan da nan bayan aure ko kuma can gaba cikin auren bayan wasu lokatai walau ga mijin da ake tare dashi ko bayan anrabu anyi wani auren.

Sannan cikin fari na bukatar samun kulawa ta musamman daga ƙwararren likita ko ƙwararriyar ma'aikaciyar jinya saboda hatsarinsa, domin su suna iya hango wata matsalar tun kafin tazo yayin goyon cikin ko bayan haihuwa domin a kauce mata. 

Ɓari shine zubewar juna biyu bayan an samesa, kafin yakai sati 28 wato watanni 7, saboda musamman mu anan Nijeriya jariri inde ya sami kulawa ta musamman in aka haifesa a wata na bakwai yana iya rayuwa. Amma idan bai kai wannan lokacin ba ko anhaifesa rayuwarsa abu ne me wahala sakamakon huhunsa bai gama haɗuwa ba balle ya karɓi iska.

______________________________________

BABBAN ABINDA NAKE SON BAYANI AKAI SHINE

Ina so na jawo hankalin mu ne akan batun rashin haihuwa wato INFERTILITY. Wacce kan kasance kode tun farko ya zamto mutum bai taɓa samun juna biyu ba, ko kuma ya taɓa yi abaya amma daga baya shiru ba'a qara ba.

Hakika duk irin yadda ake ganin ana haife-haifen nan akwai da yawa cikin Maza da Mata wanda har yau Allah baisa sun taɓa samun rabo ba!

Wanda da yawa kan rasa kwanciyar hankali da soyayya dalilin wannan.

To amma akwai abin dubawa da nazari kafin a fara zargin cewa angaza samun juna biyu. 

Kafin ace kwai matsala wance ko wane baya haihuwa... Sai an tabbatar an shafe tsawon shekara guda zingir' wato watanni goma sha biyu gyan-gyan ana samun jima'i akai-akai aqalla sau 2 zuwa 3 a sati tare da juna batare da wani shinge ba. Wato da Miji wanda yake mazaunin gida bame tafiye-tafiye zuwa wani gari ko ƙasa ba yai watanni sannan ya dawo, kuma jima'in yi ake batare da ana amfani da kwaroron roba na condom, wani maganin tazarar haihuwa ko riƙa zaro gaban ana zubarwa a waje ba. 

Wato de sai ya zamto kurum cuɗar juna ake tsawon shekara:

- Jima'i sau 2 zuwa 3 a sati ko fin haka

- Mijin da ko yaushe ana tare dashi

- Jima'i batare da amfani da wata kariya ba.

- Babu kuma sanannar matsala tattare dasu. 

To sannan ne aka cika dukkan sharruɗan fara tunanin akwai matsalar haihuwa.

______________________________________

Da yawa wasu mazajensu matafiya ne zuwa kudancin ƙasa neman na abinci, su bar matansu anan arewaci har sai randa suka dawo gida ake samun abubuwa su wakana, kar ku ɗauka wannan baida tasiri wajen ganin angaza samun rabo, ko lafiyar ma'aurata ƙalau hakan na iya kawo cikas, haka koda abaya anga sun taɓa haihuwa ko ta taɓa samun ɓari kuwa.

Bayan Aure a lafiyayyun Ma'aurata:

◾A watanni uku '3' na farko kaso 50% cikin 100 % na samun juna biyu. Wato in anyi Aure 10 to mutum 5 kan samu ciki a watanni uku na farko.

◾A watanni shida na farko bayan aure kaso saba'in 70% na samun ciki. Wato in andaura auren mutum 10 to zuwa wata shida Mata 7 zaka samu sun dauki ciki.

◾Zuwa shekara guda zaka samu kaso casa'in sun dauki ciki. Wato cikin 10 Mata tara yanzu na dauke da ciki. Kurum Mace daya ce zata fuskanci jinkiri.

______________________________________

Saide abin takaici da damuwar har gobe a yankunan mu abu ne a fili dake faruwa zaka ga duk inda aka sami matsalar jinkiri na haihuwa to zaka samu MATAR ake ɗorawa laifin kacokan, aita kyara da tsangwama, wannan yasa ko yaushe Mace ce farkon wacce zaka fara ganin tazo ga likita akan matsalar rashin haihuwa.

Da yawan Mazaje su kan qi zuwa a binkicesu har sai in abin yaci su sosai ko bayan an tabbatar Mace bata da matsalar Komi a tattare da ita wanda yasa lallai-lallai ana zargin ko shine da matsalar tukun zaka gansa. 

Saide abinda baku sani ba a yanzu matsalar rashin haihuwa kaso 50% daga Maza take, haka kaso 50% daga Mata. Wannan tasa bakowa ake son ake tunkara da zancen matsalar haihuwa ba sai kwararrun likitoci gogaggu a aikinsu, domin kwai abubuwan nazarta. 

______________________________________

Wannan tasa ni ayanzu don kazo kana cemun ai Mijinta na haihuwa ko kuwa yana da wata matar dake haihuwa... don haka ba bu bukatar binkitarsa kai tsaye itace da matsalar... kallon mahaukaci zan maka. Yau da gobe tasa Mun goge, mu muka san me muke binkita da abubuwan da muke gani da ta ina ya dace a fara, mukan yi binkice har sai mun tabbatar da komi da kan mu bawai fatar baki ba. 

-----------------------------------------------------------------

WANI ABU DA YA TAƁA FARUWA

Ya kawo Iyalinsa domin a binkici lafiyarta matsayinta na amarya cikin Matansa saboda ganin tunda ta haihu sau ɗaya shekara 6 da suka gabata bata kuma samun ciki ba duk da ba planning suke ba... alhalin ga uwar gidansa nata cigaba da hayayyafa, Infact tana nan da jariri ɗan watanni 4 dake shan nono... Amma ita amarya ba labari, gashi a zamani irin namu da kowacce burinta ace ta tara yara tun ma ba ace Allah yai ma Miji arziƙi ba.

Bayan gabatar da binkice dukkan sakamako sun tabbatar da lafiya ƙalau take, Da aka binkicesa sai aka samu sakamakon ciwon sugar da yake dauke dashi rashin control din sugarsa da kyau yakai ga ya lalata ruwan maniyyinsa da hanyar daukosa, matsalar da akalla sanda ka ganta kasan ta kai shekara 5 zuwa sama, Don haka bazai iya yiwa Mace ciki ba tun tsawon kusan shekaru 5 da suka shude... Nan a matsayina na likita na shiga ruɗu domin in haka ne to ai ga uwar gida na haihuwa! Meke faruwa haka kenan? A yanzu idan na kyalesa zaije gabane ya cigaba da binkice ana bashi gwaje-gwaje yana ɓata kudaden sa a banza don na gamsu dame nagani, bana kokonto, nasan ko nawa ne zai iya kashewa ko yace zai bar Kasar don yana da wadatar yin haka

Haka aka bashi appointment ya dawo satin sama domin shirya ta inda za'a bullo masa, a tsakanin wannan lokacin ne wani assignment yakai likita ga zaman hotel na yan kwanaki biyu anan likita ya tsinkayi uwar gidan Alhaji da saurayinta cikin ɓadda kama, wanda hakan ya tabbatar da zarginsa tare da kawo karshen rudu, domin tabbas kwai yiwuwar dashi take haihuwa ba mijinta ba. Likita ya kwakkwafeta ta kuma tabbatar da kuskuren ta. 

A karshe bayan alhaji ya dawo next appointment sanin girman al'amarin nace nai nazari na gano inda matsala take to amma ina so yai alkawarin zai karɓi abinda zai ji da kyakkyawar fuska cikin haƙuri da dangana, tare da imani da kaddara, ya musamman duba da manyan takarsa gami da gogayyarsa cikin rayuwa wato "maturity". Ƴa kuma tabbatar da ya shirya karbar ko menene bakomi. Sannan aka bayyana masa abinda ke faruwa, kuma ya riƙe alkawari ya haƙura tare da dangana komi ga Allah a gaban likita, bansan bayan an koma gida ya zata kaya ba. 

______________________________________

Shiyasa lamarin haihuwa a wannan zamanin kwai sarkakiya. Inda masu larurar da bana son gani gabana to masu infertility ne.

Matsala ce me bukatar nazari, gata da cin kudi domin tana bukatar binkice daki daki, tare kuma da bukatar haƙuri domin ba abu ne na yanzu-yanzu ba, duk da ana kashe kudi hakan bai nuna dole za'a dace, saboda akarshe bawai kurum a sami cikin ne bukatar mu ba... A'a muna so bayan samun cikin muga ankai ga haihuwar lafiyayyen yaro, sannan ne bukata ta biya. 

Wannan na daga matsalolin da bana sha'awar sam a doso ni dasu a matsayin likita. Bana son case din infertility sam. 

______________________________________

BAYAN SHAFE SHEKARA CIR BA CIKI

Nazarin farko da ya dace ayi shine kwai yiwuwar:

1. Macen nan ta haura shekara 35

2. Matar bata haila akai akai, wataqil saide ko wannan tagani shikenan kuma sai bayan wasu watanni, ko sam sam ma bata yi.

3. Tarihin samun da cuttukan dake shafar al'aura zuwa mahaifa da sauran sassan haihuwa kamar su, masassarar mahaifa, kurarraji, tsiron fibroids, inflammatory disease ds.

4. Ko namiji me lalataccen ruwan maniyyi, watakil bama ya iya samar da maniyyin, ko ga maniyyin amma matacce, ko yana da ciwon sugar da bai samun kulawa wanda ke lalata maniyyin, ko wasu cutar dake lalata ingancin ruwan, ko toshe hanyar fitarsa

5. Sai kuma a nitsa cikin binkice na ilimi bayan kauda dukkan hudun can na farko ba'a sami inda matsala take ba.

Masu wannan matsalar cikin Mata kokari zasui suka likitan Mata wato Gynecologist, cikin Maza kuma suga likitan Maza Urologist. Dukkansu ana samun su ne a manyan asibitocin mu na FMC, Specialist Hospital Ko Teaching Hospital. Wannan shine karma ace za'a bini inbox ana tambaya bani da lokacin amsa wata tambaya, kai tsaye ga likitocin da zaku nema nan ni bashi bane. 

Allah ya bada ƴaƴa masu albarka

Post a Comment

Previous Post Next Post