Abubuwan Dake Cutar Da Maniyyin Dan-Adam

Abubuwan Dake Cutar Da Maniyyin Dan-Adam



Lafiyar ruwan maniyyi nada mahimmanci wajen samar da ciki da haihuwar ya'ya.

Yana iya yiwuwa namiji ya samar da ruwan maniyyi da yawa, amma idan wadannan ruwan maniyyin sun lalace ko kuma suka samu nakasu, hakan na iya haifar da raguwar damar samar da ciki ga maza. Don haka, yana da mahimmanci a san abubuwan da ke cutar da maniyyi sannan kuma suke haifar da ƙarancin samuwar shi, don kauracewa matsalolin rashin samun haihuwa. 

Daga cikin abubuwan da ke haifar da lalacewar maniyyi sun haɗa da:

1). Zafi fiye da kima:

Ya'yan maraina suna buƙatar yanayin zafin su ya sauka kasa kaɗan fiye da yanayin zafin jiki na yau da kullun don samar da maniyyi daidai gwargwado, sannan kuma yanayin zafin ya'yan maraina yana kasancewa daga digiri biyu, uku, ko huɗu a ma'aunin Fahrenheit, idan ya kasance a sama da haka, to zai kawo cikas ga tsarin samar da maniyyi.

Don haka ya zama dole a bar wannan wuri a sanyaye tare da nisantar duk wani abu da zai iya haifar da hauhawar zafin ya'yan maraina domin samun lafiya da yawan ruwan maniyyi.

2). Sanya matsattsun gajeren wando:

Haka kuma, daga cikin abubuwan da ke cutar da lafiyar ruwan maniyyi sun hada da namijin da yake sanya matsattsun gajeren wando na tsawon lokaci, wanda hakan kan iya haifar da matsala wajen samar da ruwan maniyyi mai yawa.

Dalilin haka kuwa shi ne, matsattsen gajeren wando yana sa ya'yan maraina su kasance kusa da jiki, wanda hakan kuma yake haifar da Yanayin zafinsu ya karu. 

Don haka, yana da kyau don kula da lafiyar ruwan maniyyi mutum ya zaɓi gajeren wandon da ya dace da girmansa wanda bazai matse masa ya'yan marainan saba.

3). Sanya gajeren wando wanda bana auduga ba (non cotton underwear):

Sanya gajeren wando wanda aka hada daga nylon ko sauran zaren roba makamancin sa, yana haifar da karuwar zafi ga ya'yan maraina, ko da kuwa bai matse su ba, saboda waɗannan nau'ikan yadin suna ɗaukar zafi fiye da na auduga, kuma suna sanya yankin al'aura ya zama da danshi, yayin da suke hana iska shiga da fita daga cikin yankin al'aura wanda zai iya cutar da lafiyar maniyyi sannan kuma yana ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan Infections da ke girma a cikin guri mai danshi.

4). Cin wasu nau'ikan abinci:

Akwai dangantaka ta kud-da-kud tsakanin abin da mutum yake ci da lafiyar maniyyinsa.

Misali, naman da aka sarrafa (processed meat) da abinci mai dauke da wadataccen kitse mai yawa ana iya la'akari dasu a cikin abubuwan da ke cutar da lafiyar maniyyi.

Cin naman da aka sarrafa na iya rage yawan samar da ruwan maniyyi da tasirin motsinsa.

Hakanan kuma, maniyyi na iya lalacewa sakamakon yadda mutum yake shan madara wanda ke dauke da kitse mai yawa, saboda yana haifar da raguwar motsin maniyyi da sanya maniyyi ya zama mara amfani.

A don haka, ana ba da shawarar mutum yaci lafiyayyen abinci, musamman kayan lambu, 'ya'yan itatuwa, kifi, da nuts, domin suna da matukar fa'ida wajen kiyaye lafiyar maniyyi.

5). Tashin hankali da damuwa:

Tashin hankali da damuwa dukan su suna da illa ga lafiyar maniyyi.

Damuwa na iya haifar da sakin steroid hormones, kamar glucocorticoids, wanda zai iya rage matakin testosterone da kuma samar da ruwan maniyyi.

6). Shakar wasu daga cikin nau'ikan sinadaran chemicals:

Shakar wasu sinadaran chemicals masu dauke guba da yawa da suke kewaye damu yana lalata maniyyi.

 Waɗannan chemicals masu cutarwa sun haɗa da:

Turare masu dauke da phthalates.

Wasu daga cikin nau'ikan maganin kashe kwari.

 Organic Mercury

 Polychlorinated biphenyl.

Benzene.

Cigaba da shakar wadannan chemicals kan iya haifar da matsala wajen samar da ruwan maniyyi wanda kan haifar da raguwar samar da maniyyi ga namiji.

7). Cututtuka masu cutar da lafiyar maniyyi:

Daga cikin abubuwan da ke cutar da lafiyar maniyyi sun hada da mutumin da ke fama da wasu cututtuka da matsalolin lafiya, wadanda suka hada hada da:

Kiba:

Kiba tana da alaƙa da ƙarancin ingancin maniyyi, sannan kuma tana ƙara yuwuwar namiji ya samar da maniyyi mara amfani.

Ba ma wannan kadai ba, kiba na iya sa namiji ya sha fama da matsalolin jima'i da dama, wadanda suka hada da matsalar rashin karfin mazakuta, kuma hakan na faruwa ne sakamakon kiba da ke rage yawan samar da sinadarin testosterone.

 Cututtukan Infections:

Yawancin cututtuka Infections suna shafar tsarin samar da maniyyi da kuma ingancin abin da aka samar.

Waɗannan cututtuka sun haɗa da:

Epididymitis.

 Kumburin ya'yan maraina.

Gonorrhea.

Chlamydia.

8). Magungunan da ke cutar da lafiyar maniyyi:

Daga cikin abubuwan da ke cutar da lafiyar maniyyin mutum sun haɗa da shan wasu nau'ikan magunguna wadanda da suka hada da: Yin amfani da magungunan kashe radadi (painkiller) na tsawon lokaci. 

Magungunan magance damuwa.

Chemotherapy na masu cutar daji

Wasu daga cikin nau'ikan antibiotics. 

Wadannan magunguna na iya yin illa ga samar da maniyyi, motsinsa, da yawan sa, baya ga cutar da ci gaba da samar da ruwan maniyyi, da kuma yin illa ga iyawar maniyyi wajen samar da ciki.

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.

Post a Comment

Previous Post Next Post