Yadda Ake Hada Sabulu Na Musamman Domin Gyaran Fata Da Gyaran Fuska Da Kuma Hadin Dilka.
1) DOMIN KYAWUN FUSKA
A samu:-
1 . Garin zogale
2 . Farar albasa
3 .Sabulun ghana
4 . Sabulun Dettol
5 . Sabulun salo
Yadda za a hada.
Ki samu sabulun ghana dana salo dai dai kai daya sai ki samu dettol shima kamar guda 2 sannan sai ki sami garin zogale cokali 2 sai albasa manya guda 2 duk sai ki hada su a turmi ki kirbe su sannan sai ki juye a roba mai murfi zaki dunga wanke fuskarki da shi yanada kyau sosai yana magance kurajen fuska.
2) HADIN DILKA
1 . Dilka da sukari
2 . Lemon tsami
3 . Man zogale
4 . Turaren Du'aul jannah
Yadda za a hada:-
Zaki zuba duk kayan a cikin ruwa sai ki sa wuta amma kadan har sai ya tafasa yayi kumfa sai ki sauke idan ya huce kirinka dangwala kina shafawa a ko ina a jikinki, ki bari ya bushe, zai fara murmushewa da kansa sai ki karasa murje shi sai kiyi wanka da ruwan dumi, fatarki zatayi kyau
3) SABULU NA MUSAMMAN
A samu:-
1 . Madarar turari
2 . Lalle da dilka
3 . Ganyen magarya
4 . Kur kur
5 . Dudu osun da Detol
6 . Sabulun ghana
a hadasu wuri daya a daka su a turmi mai kyau su hadi jiki sosai sai ki runga wanka da shi.
Post a Comment