Wasu Abubuwa Dake Ɗaukewa Macce Sha'awa A Lokucin Saduwa Da Iyali

 Wasu Abubuwa Dake Ɗaukewa Macce Sha'awa A Lokucin Saduwa Da Iyali



1- MATSALOLIN MARA DA MAHAIFA

Kama daga sanyin mara (vaginities/toilet infections, UTI & STDs), yoyon fitsari, 'kululun mahaifa (fibroid), da sauran cututtukan al'aura, na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima'i.

Misali, sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje acikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima'i, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen acikin al'aura ba, saidai su ce su na jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda gugar da ake musu yayin saduwa, sai wurin ya zama rauni.


2- BUDEWA

Budadden gaba ga mace na sanya raguwar jindadi tsakanin ma'aurata. Sau da yawa ma'auratan biyu ba zasu samu gamsuwa ba da kyau, sannan macen baza ta iya jin 'kololuwar dadi ba shi ma namijin haka saboda rashin haduwar fata da fata yadda ya kamata.

3- KACIYAR MATA

Idan aka samu matsala wajen yiwa mace kaciya, ya zamanto an yanke beli da yawa fiye da yanda ya dace. Yin hakan na kashe sha'awar mace idan ta girma. Yanke beli da yawa ko duka matsalace dake hana mace jin dadin jima'i, domin kuwa beli shi ne matattarar jin dadin jima'in mace.

4- MAGUNGUNA 

Yin amfani da magunguna ba bisa ka'ida ba. Yawaita shan magunguna barkatai kan iya ragewa mace sha'awa ko kuma ya sa ta dauke baki daya. Wani lokacin kuma ko da bisa ka'ida aka sha maganin to zai iya yiwuwa daga cikin side effect dinsa shi ne yana dauke sha'awa zuwa wani lokaci.

6- RASHIN ABINCI MAI GINA JIKI. 

Abinci mai gina jiki na nufin abincin da ke dauke da sinadaran da jikin mutum ke bukatarsu, to shi ne mai gina jiki a wajensa. Idan mace ba ta samun ingantaccen abinci to za ta iya samun matsalar rashin sha'awa sosai. 

7- RASHIN FAHIMTAR YANAYIN MACE

Wata matar ba wai sha'awar ce ba ta da ita ba, a'a. Ita kanta ba ta fahimci abinda zai sa mata sha'awar ba ne, shi ma mijinta bai fahimce ta ba, sai a tafi a haka, a matsayin ba ta sha'awa.


8- WASA DA GABA

Post a Comment

Previous Post Next Post