Shin kuna cikin masu zubar da bawon Albasa lokacin da zakuyi amfani da ita?
Ga wasu dalilai da zasu dakatar daku yin hakan.
Albasa bakidayanta tana da amfani sosai ga lafiya.
Tana dauke da sinadaran da ke kare jiki daga kamuwa da cututtuka da dama, amma galibin mu muna zubar da bawon Albasa saboda bamu san darajarsa ba.
Akwai fa'idodi masu yawa ga mai amfani da bawon albasa ke samu, domin tana dauke da kaso mai yawa na sinadarin ‘Antioxidants’, wanda aka kiyasta ya fi wanda ake samu a cikin albasar kanta.
Sannan kuma ana iya amfani da shi a matsayin antibiotics da antimicrobial, saboda yana dauke da sinadaran gina jiki masu amfani.
Karanta Wannan: Matsalar Dake Addabar Wasu Samari Da Yan Mata Na Warin Baki
Ana iya amfani da bawon albasa yayin shirya abinci kala daban-daban.
Kasancewar yana da kyakkyawan tushen samarda vitamin A, vitamin C, vitamin E da antioxidants, irin su flavonoids masu yawa da sauransu, waɗanda ke kare zuciya, magance matsalolin tsufa, da rage cholesterol na cikin jini da kuma inganta garkuwar jiki.
Amfanin bawon albasa:
Masana sun yi nuni da cewa bawon albasa yana dauke da sinadarin quercetin, wanda ke taimakawa wajen magance hawan jini da kuma bada kariya daga toshewar jijiyoyin jini.
Bawon cike yake da dietary fiber da kuma phenolic Compounds waɗanda ke taimakawa wajen bada kariya daga cututtukan jijiyoyin jini da bawa zuciya kariya da hanyoyin jini.
Ana iya samun Quercetin da sauran sinadarai masu amfani da ake samu a cikin bawon albasa ta hanyar sanya albasa gaba dayanta a cikin tukunya, sannan a tafasa ta na tsawon mintuna goma, sannan a zuba a cikin kwano domin ci, ko kuma a zuba a cikin shinkafa.
Ana amfani da bawon albasa don magance ciwon makogwaro.
Ana sanya bawon a cikin tukunyar ruwa a tafasa su na tsawon mintuna goma, sannan a yi amfani da su wajen yin kuskura a baki.
Wannan yana taimakawa wajen rage kumburi a cikin makogwaro, ta hanyar anti-inflammatory properties ta take dauke dashi.
Bawon Albasa na da amfani wajen kawar da radadi, ta hanyar tafasa albasar da bawonta gaba daya a cikin tukunyar ruwa na tsawon mintuna 15 zuwa 20.
Ana tace ruwan ana shan sa a matsayin shayi kafin a kwanta barci na kusan mako guda.
Wannan hanya na iya rage radadi a kafafu.
Bawon Albasa Yana ƙara yawan adadin insulin a cikin jiki, don haka magani ne na dabi'a ga masu ciwon sukari ta hanyar sarrafa matakan sukarin jini.
Cin bawon albasa yana taimakawa wajen kawar da matsalar ciwon kai, na yau da kullun ko migraine, kuma an tabbatar da cewa yana iya kawar da rashin barci, gajiya da damuwa, kuma yana ba mutum kuzarin da ya dace don gudanar da ayyukan sa na yau da kullun.
Bawon Albasa yana taimakawa wajen girman gashi sosai, sannan kuma ana iya magance matsalar bushewar gashi da kuma wanda baya girma ta hanyar amfani da wannan bawon.
Ana zuba bawon albasa a tukunyar ruwa a tafasa su, daga nan kuma sai a wanke gashin da sabulun wanke gashi da kuka saba na yau da kullum, sannan daga nan sai a dauraye gashin da wannan ruwan albasa da aka tafasa.
Yana saka gashi yayi laushi kuma ya kwar da dandruff.
Ana daukar bawon albasa a matsayin babban tushen antioxidants, wanda ke da muhimmiyar rawa wajen yakar cutarwar free radicals sakamakon ayyukan cell, da kuma kawar da tasirin su a cikin jiki. Wannan aikin kuma yana kara ƙarfafawa garkuwar jiki, saboda Ƙarin yawan adadin free radicals yana kara rauni ga garkuwar Jiki.
Bawon albasa zai iya inganta ayyukan tsarin narkewar abinci.
Idan kuna fama da matsaloli a cikin wannan tsarin, bawon albasa magani mai kyau, saboda yana ƙara yawan fitar digestive juice, da kuma gyara matsalolin narkewar abinci da cututtukan gaba ɗaya.
Ku karbi wannan a matsayin goran Sallah zuwa ga dukkanin yan uwa musulmi.
Allah ya karbi dukkanin Ibadunmu.
Allah ya maimaita mana.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA
Post a Comment