Dalilin Da Yasa Yawanci Maza Matasa Suke Tashi Daga Barci Da Mikakken Azzakari.

 Dalilin Da Yasa Yawanci Maza Matasa Suke Tashi Daga Barci Da Mikakken Azzakari.



Abinda aka fi sani shine mikewar azzakari (penile erection) tana faruwa ne idan sha’awar namiji ta motsa. A lokacin da sha’awar namiji ta motsa, jakunkunan da suke ajiye sinadarin “testosterone” wadanda suke cikin kwakwalwarsa zasu zubo da sinadarin testosterone din. Hakan zai aika da sako zuwa ga jijiyoyin azzakari cewa ana bukatar su bubbude domin jini yayi ambaliya (rushing) a cikinsu. Nan take sai jijiyoyin subi umurni, kuma sai jinin ya cika su. Daga nan sai azzakarin ya mike tsaye kyam.

Amma ana samun lokutan da azzakarin namiji yake mikewa ba tare da motsawar sha’awar ba. Wannan yana faruwa ne saboda ba kawai a cikin kwakwalwa jakunkunan da suke ajiye sinadarin testosterone suke ba, a’a akwaisu a cikin lakar kashin baya (spinal cord). Don haka mikewar azzakari batare da sha’awa ba yana faruwa ne idan sinadarin testosterone ya zubo daga laka maimakon daga kwakwalwa. Bisa wannan dalilin ne maza masu matsalar laka suke iya samun mikewar azzakari. Sai kaga mutum ya sami matsalar laka wacce ta kwantar dashi shekaru da yawa, amma kwatsam sai kaji ance matarsa tana da ciki. Eh mana, cikinsa ne domin yasan yadda akayi aka sami cikin.

Ita kuwa matsalar mikewar azzakari a lokacin da namiji yake barci, ana kiranta “nocturnal penile erection”, ko "nocturnal penile tumescence", ko "morning wood" a likitance. Tana faruwa ne idan barcinsa ya fara nisa, watau yakai kimanin minti 90. A wannan lokacin ne mutum yake mafarkai, kuma ana kiran matakin da “Rapid Eye Movement (REM) sleep stage”. Daidai wannan lokacin akwai shashin kwakwalwa wanda shi baya barci, kuma shi yake motsa (stimulating) jijiyoyin laka wadanda ake kira “parasympathetic nerves” su kuma su haifar da zubar sinadarin “serotonin”, shi kuma ya haddasa zubar sinadarin testosterone, shi kuma ya haifar da mikewar azzakarin.

Bincike ya nuna cewa mikewar azzakari a cikin barci yana da fai’dar ankarar da namiji akan bukatar ya gaggauta yin fitsari idan ya farka, saboda yawanci idan namiji ya tashi barci da mikakken azzakari zai ji mararsa cike da fitsari. Da zarar yayi fitsarin sai azzakarin ya kwanta. Wannan yasa wasu masanan suke fahimtar cewa idan namiji jiddidin baya tashi barci da mikakken azzakari, to, hakan zai iya zama alamar ciwon sugar (diabetes). Sabanin yadda wasu zasu yi tunani, mikewar azzakari a lokacin da namiji ya tashi daga barci, ba lallai sha'awa ce take sanya hakan ba. Don haka ba matsala bane, tsabar lafiyar azzakari da sauran sassan jiki ce kawai

WalLahu A’lam.

Post a Comment

Previous Post Next Post