Dalilan Da Suka Sa Namiji Zai Yiwa Matarsa Kukan Dadi A Lokacin Saduwa

 Dalilan Da Suka Sa Namiji Zai Yiwa Matarsa Kukan Dadi A Lokacin Saduwa 



Kaman yadda muka yi bayani a baya, yadda ba duk nata suke yin kukan dadi a lokacin saduwa da mazajesu ba, haka nan mazan ba duk suka yi ba saboda wasu dalilan da muka kawosu a darasin mu na farko.


Sai dai kuma wannan kukan yanada matukar mahimmanci ga ma'aurata, domin shi kuka ne da yake dauke da sako daga shi namiji zuwa ga matarsa ko ita mace zuwa ga mijinta, don haka ne ya dace maza su rika yiwa matasu kukan dadi saboda wadannan dalilan kamar haka:


1: Yana Motsa Mace: Mace ko da batada sha'awar saduwa da mijinta da zaran taji ya soma wannan gurnanin tun a lokacin wasannin motsa sha'awa take kamuwa da kuma bukatuwa.

Akwai matan da sauraran sautin sumbatu kawai yana iya sasu samu biyan bukata ba tare da an taba su bare kuma ace ana tabata ana mata sambatu.


2: Yana Isar Da Sako: Shi wannan kukan yakan kaiwa mace sako cikin sauki ba tare da furuci ba.

A lokacin da mace ta tabawa namiji inda yake so zata ji sautinsa ya sauya daga yadda ya soma. Idan ta sake taba inda yafi inda ta soma tabawa zata ji sumbatun, kukan ko gurnanin ya kara tsayi. Haka nan taba inda bai dace ba zata fahimci hakan daga sautin mijinta.

Don haka yiwa mace kukan dadi yake da amfani domin cikin sauki kana aika mata sako ne yadda zata taba ka da abunda baka so ta maka koda bazaka furta mata ba.


3: Yana Kara Armashi: Ma'aurata na kara samun wani kuzari da annashuwa na daban a lokacinda suke yiwa junansu koken dadi a yayin saduwa.

Da ma'aurata zasu yiwa junansu gum ko saduwan nasu bazai yi armashi ba.


4: Yana Tabbatar Da Soyayya: Ta hanyar sumbatun dadi mace na iya fahimtar irin son da mijinta yake mata da kuma matsayin dadin da take jiyar da shi a wannan lokacin.

Da namiji zai yi Jima'i kwantar da sha'awa ba na kauna da soyayya ba irin wanda zai biya kudinsa, da wani sai idan yazo zuwan kai ne mace zata iya jin muryarsa, wani ma ko a lokacin bazai ce komai ba saboda ba yayi bane saboda soyayyar da yake yiwa wacce ba, yayi da domin sha'awar dake damunsa.

Amma idan namiji yana saduwa da macen da yake sonta na aure ta wannan hanyar ce zata fahimci irin son da yake mata.


5: Hanyar Isar Da Sako Ne: A lokacin wannan sumbatun mutum na iya yin batutuwan da bazai iya yinsu ana zaune babu hakan ba.

A lokacin ne namiji yake tabbatarwa matarsa irin son da yake mata, irin tsaftar da take da shi. Irin ni'imar da Allah Ya mata da yadda take gamsar da shi ba tare da yaji nauyin fada ko kunyar fada ba.

Wasu ma a irin wannan sumbatun suke yin wasu alkawuran da wasu suke cikawa, wasu kuma ayi ta musu dasu da gardama suce basu ma san da zancen ba.


Tabbas yiwa mace kukan dadi yana da alfanu sosai, hakan ma yasa wasu malamai na Jima'i sukace duk abunda ma'aurata zasu furta a wannan lokacin koda na laifi ne, baza a hukuntasu da shi ba.


A darasin mu na gaba. Zamu yi bayanin yadda zaki sa mijinki ya miki kukan dadi a lokutan ku na Jima'i.

Post a Comment

Previous Post Next Post