Nau'in Azzakarin Da Mata Keso A Wajen Saduwa
Sufa Mata Ba Tsawo, Kauri Ko Girman Azzakari Bane Ya Damesu Ba
Maza da yawa sun shiga damuwa tare da zullumin halittar su na azzakari, wanda hakan yasa wasu mazan suka kasa zaune bare tsaye domin ganin sun shiga duniyar nemo maganin da zai karawa azzakarinsu tsayi, girma ko kauri, wai don dai kada matan da zasu aura ko suke aure su kawo musu raini. Allah gafarta Malam lamarin ba a tsawo ko girman azzakarinka yake ba bare kuma kauri, Alhajin Allah babban abunda mace ke bukata da azzakarinka shine iya sarrafashi da sanin makaman aiki dashi, kalas.
Kamin na daura daga nan, yana da kyau nayiwa maza bayanin abunda bincike ya tabbatar akan tsayi, girma da kuma kaurin azzakari.
Duk namijin da azzakarinsa tsawonsa ya kasa kaiwa centimeter 12 zuwa 17, ma'ana inci 4 zuwa 7 idan azzakari ya mike to sune mazan da ake musu ganin gaban su yayi kankanta. Shi kuwa kaurin azzakari a cewar masana idan ya wuce centimeter 3 ya wuce kima.
Da yake yanzu mun fahimci ma'aunin da ya kamata tsawo da kaurin azzakari ya kamata ya zama, to abun sani a gaba shine ko wanne mata suka fi bukata a lokacin saduwa. Akasarin mata musamman wadanda suka taba auren sama da namiji daya koman da suka buga bariki zasu tabbatar maka da cewa sam kauri ko tsawo ba shi bane abunda suke bukata amma yadda aka sarrafa su har suka samu biyan bukata shine abunda yafi mahimmanci a gunsu. Sai dai fa duk da haka ana samun matan da muddin ba ji sukayi azzakari ya cika musu gabansu ba yayi tab da gidinsu, basu sanin ana jima'i dasu, wasu matan babu abunda suke bukata ga azzakari irin suga girmansa ya kai na jaki idan zasu samu wannan shine abun bukatarsu. Amma da yake irin wadannan matan basu da yawa a cikin halittu na mata, kamar yadda bincike ya tabbatar, cikin mata dubu idan aka tarasu bai wuce kashi days bane suke da irin wannan bukatar.
Daya daga cikin ribar da ake samu wajen auren macen da kaine zaka soma kwanciyar aure da ita shine yadda zata dauru akan yadda ka horas da ita jima'ince koda kuwa da yatsarka kake gamsar da ita baka taba zura azzakarinta cikinta ba haka zata dauka shine abunda ake nufi jin dadin har sai lokacinda ta samu sauyin hakan. Don haka anan abunda kake bukata da guntun gatarinka shine ka gano hanyoyin da zaka iya gamsar da matarka dasu a lokacin jima'i ta hanyoyin kwanciyan yanayin kwanciyar jima'i (Styles) da kuma wassannin motsa sha'awa, (foreplay).
Da akwai yayanin kwanciyar da duk kankantar azzakarinka idan kuka yi dole matarka ta jika, kamar yadda akwai yanayin kwanciyar da idan kayi zaka jiwa mace ciwo ne ba dadinsa zata ji ba saboda girman gaban naka. Ba kamar yadda wasu mazan suke tunanin ba, azzakari mai tsawo bai cika gamsar da mata ba sai dai ya cutar dasu a yayin jima'i. Domin sau tari yana wuce matsayarsa har ya rika tabo abunda ake kira pelvis a turance wanda hakan kuma yakan cutar da mata. Shi yasa koda namiji mai halittar girman azzakari ne abunda ake bukata shi ne yabi matarsa a hankali na kuma tsawon lokaci har sai ta saba ba kawai rana daya dare guda ba a antaya mata abunda bazata iya dauka ba a nan take.
Awannan rubutun ba zan yi magana bane akan yanayin kwanciyar jima'i daya kamaci masu kankanta da girman azzakari ba, amma ina son maza magidanta su fahimci wani abu. Idan ka kasa mata kashi 10, kashi 7 na cikinsu basa samu saduwa ta hanyar shigar azzakari cikin farjinsu kadai, dole sai an hada da wasu tabe-tabe da latse-laste kamin su samu gamsu. Don haka ka zage karfinka kanata surfafar matarka sadoda kana takamar kana da zabgegiyar azzakari ba tare da sanin hanyoyi masu saukin da zasu sa ta kawo da wuri ba kana batawa kanka lokacine tare da gajiyar da kanka gara ma ka shiga filling kwallo ka yi zagaya.
Yana da mahimmancin maza magidanta suma san yadda farjin mace yake komawa a yayin da take bukatar jima'i wanda hakan shima na iya tabbatarwa masu kankanta mazaguta abunfa batanan take ba.
A lokacin da mace ta kamu da sha'awar jima'i, gaba daya jinin jikinta zai koma ne yana gudana a bangaren farjinta kamar yadda inda namiji shima ya kamu da sha'awa jini ke dawowa jijiyoyin azzakarinsa haka ita ma mace. A wannan yanayin gabanta ba budewa yake yi ba, dada tsukewa yake yi kamar yadda bincike ya nuns, don haka idan mijinta mai girma ko kaurin azzakari ne yazo shiganta a hakan ba tare da ya sarrafata sosai ta jike ba, dole ne ya cutar da ita, kuma idan sabuwar shiga ce daga nan ta soma gudun kwanciyar aure dashi.
Idan kuwa mai karamin azzakari ne, to yana shiga yana budewa dai-dai da kaurin azzakari da kuma tsawonsa. Shi kenan a haka zata saba har sai idan an samu wani canjin mijin. Ga mata masu dabaru irin na jima'i idan suna saduwa da mazansu masu kankantar mazakuta basa yadda suyi yanayin kwanciyar da gabansu zai bude sosai, kuma suna matsai gabansu ne a lokacin da namiji ke cikinsu, su kuma rikeshi gam domin yajishi a matsai.
Duk da haka akwai maza da ake samu kankantar gabansu na cuta ne, wanda za a ga na farko akwai wanda azzakarinsa yake kankancewa ya koma kamar na karamin yaro musamman bayan sun gama jima'i ko a lokacin da basu da sha'awa, to irin wadannan da sauransu sai dai yana da kyau su ga likita.
Akwai wanda lokacinda basa sha"awa gabanua baya kankancewa amma koda yaji sha"awa baya kara girma ma'ana sai dai kawai ya kumbura. Shima wannan yaga likita duk da yake da sauransa.
wasu kuma azzakarinsu yana kankancewa lokacinda suka ji sha awa koma basu ji gashi nan dai, sai jifa jifa yake harbawa, babu shakka akwai matsala tartare da irin wadannan mazan suna bukatar ganin likita a guje.
Duk da yake kamin ma a samu ci gaba na zamani da yanzu haka yazo da kwayoyi da na'urori da magungunan kara tsawo da girman azzakari, a baya akwai masu magunguna na gargajiya da suke wannan aikin har yanzu kuma. Sai dai shawarar da zan baiwa maza magidanta shi ne girma ko kauri ba shine mafita ba, shi wannan halittar da kake ganin na farji, akwai baiwa da hikima da Allah Yayi kawai kadai yi abunda zaka iya yi ka hakura, kana iya zuwa ka karo ta mutu ko kuma ku rabu ka samu wata da kake matukar so ita kuwa bazata iya zama da kai ba. Baya ga illolin da za iya samu tattare da yin wannan aikin na kara maka gaba. Maimakon hakan ka bata lokacinka kawai wajen binciko abubuwan dake saukin kuma saurin gamsar da matarka kawai ba tare shan wasu kwayoyin da zasu cutar da kai nan gaba ko a yanzu haka.
Shi dai Bahaushe na cewa "Guntun Gatarinka, Yafi Sari Ka Bani".
Akwai tambaya ko neman karin bayani?
#Tsangayarmalam
Post a Comment