BA Sai An Hau Ruwan Cikin Mace Ba Zaa Gamsar Da Ita Ba
*******************************************************
Mafiya yawan mutane su kan yi mamakin yadda ma'auratan zasu kasance wajen gudanar da kwanciya su na jima'i a lokacin da suka ga namijin jibgege yana auren karamar mace. Ko karamin namiji da auren katuwar mace. Sai kaji masu sharyi na cewa "wannan yaya zai yi da ita. Yaya zata yi da shi.
Mafi yawan mutane sun tafi akan cewa ba a jima'i sai namiji ya kwanta akan mace. Wannan yasa suke ganin idan jibgegen namiji ya kwanta akan ruwan cikin mace mai karamin jiki zai mata illa. Idan kuma karamin namiji ya hau ruwan cikin katuwar mace ba zata ji komai ba. Wannan abun ba haka yake ba.
Haɗin Karin Ni'ima Danna Domin Karantawa
Akwai yanayin kwanciyar jima'i sama da guda dubu daya daban daban wadanda ma'aurata zasu iya yi dai dai da yanayin su.
Baya ga haka shi kwanciyar jima'i ana yin sa ne yadda za a samu gamsuwa. Don haka ba wai dole bane sai namiji ya hau ruwan cikin mace sannan za a ce an samu gamsuwa ba.
Akwai matan da muddin ruwan cikin su zaka hau ko su dubu zaka hau kuma ko awa nawa zaka yi akan ruwan cikinsu baza su taba samun gamsuwa ba. Don haka irin wadannan matan gala kenan basu bukatan a hau ruwan cikin su saboda jima'i.
Akwai ma mazan da basa taba jin dadin jima'i idan dai sai sun hau ruwan cikin mace.
Wannan ya nuna kenan shi jima'i ba hauwan ruwan cikin mace bane samar da gamsuwa da yanayin da ake so shine jima'i.
Duk macen da ta ke da girman jiki gamsar da ita ta hawa ruwan cikinta bai da sauki kuma aiki ne ja. Suna da yanayin jima'i masu sauki da suke bukata domin gamsar dasu cikin sauki.
Haka namiji mai girman jiki kwanciya akan ruwan ciki mace karama ba abu bane da yake jin dadin yin sa ba kuma bai samarwa masu irin wannan yanayin halittan gamsuwa na jima'i.
Suma irin wadannan maza suna da yanayin da suka fi sha'awar yi idan suna auren mata masu kankantar jiki.
Haka suma maza masu girman gaba da kankantar gaba kowanne su akwai yanayin saduwa da suka fi sha'awar yi da iyalansu kuma tanan ne suke samun gamsuwa.
A darasin mu na gaba idan lokaci ya samu zamu kawo yanayin kwanciyar jima'i da suka dace da irin wadannan ma'auratan.
Ustaz Usman
Post a Comment