Yadda Ake Hacking WhatsApp da kuma yadda Zakare kanka sannan kayi recovering from Hack din.
Victims na WhatsApp Hack ne suka nemi da nayi wannan rubutun da bada shawari akan matsalar da ta zamo ruwan dare yanzu wato hacking whatsApp account. Ba wai zan koya yadda ake hacking whatsApp bane, a'a! Zan dai bada haske akan yadda hackers din suke yi sannan kuma na gaya muku yadda zaku kare kan ku da kuma yadda za kuyi taking over na account din ku.
Hanya ta farko:
Hackers ba zasu iya hacking whatsapp din ka ba sai idan sun san number ka. Ta yadda suke samun number ka shine ta hanyar amfani da whatsapp groups wanda kuke ciki tare. Anan suke fara samun number ka. Bayan sun dauki number ka, sai ku yi kokarin dora ta akan wani whatsapp din dake kan wayar su. To amma suna bukatar OTP. Yadda suke samu shine, suna amfani da wani App da ake downloading a playstore wanda yake baka damar duplucating apps, ta haka sai suyo floading system din sai ta zama confuse, sai su samu OTP din ka. Kuma kai baza kayi ma recieving ba balle ka gani. Next thing sai kaji ana kiran ka ana cewa hackers suna tambayar kudi da sunan ka.
Hanya ta Biyu:
Bayan sun bi wasu daga cikin hanyoyin da nayi bayanu a sama, idan anzo wajen OTP sai su kira ka da sassafe, ko wajen dare, lokacin ko kana kokarin kwanciya ko baka tashi ba. Sai suce maka suna wani group tare da kai, su admin ne, suna son suyi resetting group policy don haka za'a mayar da kai group. So suna so ka karanto musu Codes da whatsapp suka turo maka. Kai kuma idan baka lura ba sai kawai ka karanto musu. Shikenan sai whatsapp din ka yayi signing out. Anyi hacking.
Kare kan ka:
Haryar da tafi kowacce sauki wajen kare kanka daga irin wannan, shine ta hanyar amfani da Two-Step Verification. Yana nan idan ka shiga whatsapp sai kaje Settings - Sai kaje - Accounts - Zaka ga Two Step Verification. Da shigar ka sai kayi clicking Turn on, sai ka shiga da key wanda kaikadai ka sani. Shikenan.
Ko da hacker yayi wancen process din, da ya fara zai ga two steps verification. Dole sai dai ya hakura. Shikenan kayi maganin sa.
Bayan anyi hacking din ka, ya zaka kwato account din ka?
Idan hacker din yana da basira yasan me yake, yana kwace account din ka zai shiga two step verification shima don ya rufe ka, ya kuma hana ka samun damar kwabar number ka. To kai kuma yadda za kayi sai kayi maza ka shiga settings din wayar ka kayi abu kamar haka:
1. Ka shiga setting, sai kayi kasa, kowace waya tana da wajen Apps, wato inda duk wani application yake zaune da settings nashi.
2. Bayan ka shiga Apps, kaza ga jerin gwanon options, sai ka nemi App Management. Anan ne zaka ga kowane App da bayanan sa da settings nasa.
3. Sai ka nemi WhatsApp. Kana bude settings din na whatsapp, sai kayi kasa, zaka ga Storage Usage. Sai ka shiga. Bayan ka shiga, zaka ga options kamar haka: Total, App, Data, Clear Data, Cache, Clear Cache.
4. Sai ka dannan akan clear Data da kuma Clear Cache daya bayan daya. Idan ya saka maka completed. Sai kayi sauri ka fita. Ka koma Home. Ainihim inda Home Page naka yake. Sai ka sake bude WhastApp App din ka. Zaka ga komai ya goge, ya dawo sabo. Sai kaga Welcome.
5. Anan ne sai kayi adding number ka da aka sace, Immediately zaka ga sun nuna maka inda zaka shigar da codes. To anan gizo yake saka. Domin mostly zai wuya ka yi recieving codes saboda hacker yayi blocking codes din.
6. To abinda za kayi shine, sai ka jira har sai agogo gefen ka ya gama counting 60 seconds. Anan zaka ga wani option ya rubuta "Didnt Recieve Code?". Sai kayi selecting.
7. Anan ne sai ka zabi su kira ka kai tsaye, ko su maka SMS kai tsaye. Ko da shi hacker yayi blocking. Wannan zai overiding wancen request din. Shikenan sai ka shiga da code. Kayi securing account din ka.
8. Daga nan sai ka wuce settings kaje kayi setting two steps verification don hana hakan afkuwa.
Yana da kyau ka sani cewa, according to CSO a wata mujallar su ta Octber 2022, sun ce, 70-80% na WhatsApp hack laifin mai waya ne. Domin mutane da yawa ana amfani da technique din social engineering wajen sace musu tunanin da yaudarar su. Don haka sai mun gyara. Su ka kuma kara da cewa, there is no remedy for stupudity. Sai idan mutum ya nemi ilimin kare kansa.
Post a Comment