Yadda Za A Kula Da Lebe Lokacin Hunturu:

 Yadda Za A Kula Da Lebe Lokacin Hunturu:



Yanayin leben mutum kamar yanayin fatarsa yake don haka akwai leben da ke saurin bushewa akwai kuma wanda kan jima da lema a jikinsa.


Bushewar lebe babbar matsala ce da ke janyo lebe ya rika saba ta hanyar fitar da busasshiyar fata ko ma leben ya tsattsage wanda zai zama illa ga lafiyar mutum baya ga janyo wa mutum kyama daga duk wanda suka yi ido hudu da shi.


Kada a rika tattaba lebe ko kuma a rika lasar lebe.


1- A rika cin abinci mai gina jiki, acikin abinci akoi sinadaran vitamin da suke taimakawa lebe.


2- A rika shan ruwa sosai, rashin shan ruwa yakan kawo bushewar lebe.


Karanta Wannan: Tsotsan Farjin Macce A Lokacin Saduwa Halak Ko Haram?

3- Idan za a kwanta barci a goge jambaki sai dai a shafa basilin wanda zai bar leben a jike.


4- A rika yawan shafa mai a leben wanda aka tanada don lebe.


5- A daina ciccire fatan lebe ta hanyar cizar leben ko farce.


5- A kauracewa taba sigari kwata kwata domin yakan saka lebe ta bushe.

Post a Comment

Previous Post Next Post