Tsotson Farjin Macce A Lokacin Saduwa Halak Ko Haram?

Tsotson Farjin Macce A Lokacin Saduwa Halak Ko Haram?



Tambaya

Assalamu alaikum, M. Na kasance ina tsotsan azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci ?.

Amsa

To 'yar'uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu Malik.


Karanta Wannan: Amfanin Albasa A Jikin Dan Adam A Lokacin Sanyi 

Saidai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar cewa: a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda neman kariya.

Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta: (223), ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.

Allah ne mafi sani.

Duba: Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul Khalil 3\406.

Post a Comment

Previous Post Next Post