Maganin Wanke Dattin Ciki Da Dattin Mara Na Maza Da Mata Ta Hanyar Amfani Da Abubuwa Guda 10 Kamar Haka

 Maganin Wanke Dattin Ciki Da Dattin Mara Na Maza Da Mata Ta Hanyar Amfani Da Abubuwa Guda 10 Kamar Haka



da zan Lissafosu Guda 10 wadanda duka baza suyi wahalar samowa ba gasu kamar Haka\


1. Asalin Ganyen Zaytun a dakashi ya dawo Gari sosai, a kalla ana son cikin babban Chokali uku

2. Tsohuwar Tsamiya ba danyar ba, in ance Tsohuwar Tsamiya itace wacce zaka ga tayi Brown ko jah kuma tana da Danko sosai itace tsohuwar Tsamiya Guda bakwai

3. Jar Gauta wacce ta Bushe kuma wacce Bata Dagargaje ba guda 7

4. Lemon Tsami Guda 7 shima mekyau ba Busashshe ba

5. Garin Sanamaki/Fulasko Ana samunsa a Islamic chemist, A kalla ya kai kimanin Chokali uku 3 babban Chokali

6. Tafarnuwa mekyau Kwallo Uku, kuma a bare busashshen Bawonta a yayyanka ta kanana-Kanana

7. Albasa Fara Babba mekyau guda daya bajaba 

8. Dabino Mekyau a kalla guda 20 a baresu a cire Kwallon, a kuma cire Dattin ciki har wannan Leda-Ledar farin a cireshi

9. Ganyen Zogale busashshe kuma garin a kalla ya kai cikin chokali uku babban chokalin cin shinkafa

10. Zobo, Eh zobo dai da aka sani Wanda ake jikawa yayi jah a sa siga a sha shi nake nufi, a daka garinsa shima a kalla ya kai cikin chokalin cin shinkafa uku

Sai a nemi Ruwa mekyau a kalla ya kai kimanin Liter Biyu, ko uku, Sai a juye wadannan ABUBUWAN da aka lissafo guda 10 din a cikin wani abu me dan girma Wanda zai dauke su, sai a barshi sai ya kwana tukunna a ciki sannan sai a juye a tukunya a dafa su su tafasa sai a tace azubashi a cikin wani Abu mekyau Wanda bazai lalata shi ba, sai a dinga sha bayan an ci abinci kullum sau biyu a yini

Ana son in aka ci abinci aka sha a tsaye sai a zauna a bubbude kafafuwa a saki jiki ana Numfashi ta yadda mara da ciki zasu sakata su wala maganin ya ratsasu sosai tsawon mintuna Goma sai a cigaba da harkokin da aka saba, da yamma ma a kara yin haka, in ana azumine kuma ana sha lokacin Sahur da lokacin bude baki (Iftihar) ana daukar kwana bakwai ne a cikin kowanne wata ana yin Service, inshaaAllahu dukkan Dattin dake cikin mara ko ciki ko tsutsar ciki, ko Rubabben Maniyyin da ke Dankarewa a marar Maza ko Rana ko wani Cuta wacce take Mara ko Ciki InshaaAllahu wannan Maganin zai wankosu Gabadaya, zai dinga Pitar da su ta Fitsari ko ta kashi (Bayangida) Saidai idan Mutum yana da Ulcer ana son in ya sha sai ya kara da ruwan sanyi inshaaAllahu Ulcer din baza ta tashi ba


Wannan Maganin ba iya dattin ciki da mara kadai yake Magancewa ba, Yana wanko Har dattin da kan zama Barazana ga Huhu ko Hanta ko Qoda, Sannan yana Wanko Mahaifa ga Mata kuma yana wanke Jijiyoyin Zakari na Dah Namiji Mace me Ciki Zata iya amfani da wannan magani ba matsala inshaaAllahu, Kuma ana iya bawa yara Kanana amma yadda zasu sha daidai yadda zai dauki cikinsu ne, ya danganta da shekaru ko girman yaron, mata zasu fini Fahimtar me nake nufi a nan,


Wati idan Namiji ko mace Babba Baligi ko baliga zai sha Cikin karamin Kofi toh Wanda bai Balaga ba indai yana iya cin abinci zai sha rabin karamin Kofi kenan, amma in YARO bai fara cin abinci ba ba a bashi, domin ana sha ne bayan an ci abinci an koshi.

Allah yasa mudace dalilin Annabi Muhammad S a w.

Post a Comment

Previous Post Next Post