Maganin Karin Ni'ima Yayin Jama'i Da Mijin Ki

 Maganin Karin Ni'ima Yayin Jama'i Da Mijin Ki



Babbar magana ance da makasau bawa domin dai duk matar dake da wannan matsakar lallai auranta yana cikin lilo domin ni’imar mace itace ke baiwa maigida nishadin kusantarta, amma in dai ya jiki baki da ni’ima to kuwa idan ya dosoki da bukata ki tabbatar matsuwa ce.


Irin haka ne ke sanyawa kina ji kina gani namiji ya dinga miki satar kwana, mai tsananin kaunar ki ne zai furta miki wanda yaga kuwa ba zai iya ba yayi ta kyara da hantararki karshe ma ki ga ya sake ki babu laifin tsaye babu na zaune.

Karanta Wannan: Muhimmancin Jigida A Kwankwason Mata

Shike sanya mace duk sanda mijinta zai kusance ta sai ya sha wahala kafin mazakutarsa ta shiga farjinta ba wai matsuwa ba ce, a’a akwai masu irin wannan halittar ta matsuwar amman kuma ai da ni’ima ba’a shan wahala duk sanda za’a kusance su, don haka ‘yar uwa da kin jiki kandas sai ki sani da akwai damuwa ga maigida.


Amman akwai wacce zaki ji tana cewa, ai ni idan ina tafiya ma ruwa har bi naa yake yi, to ki tambaye ta wane irin ne ruwan don wasu fa ruwan karancin wasu sindarai ne a jikinsu wanda bature ke kira da minerals kamar vitamin C, vitamin E, zine arginene, fotic acid, vitamin B1, 2 , 3 and B3 da dai sauransu ne.


Wasu kuma ruwa mai wari na ciwon sanyi gonorrhea- sai ace wai ni’ima akwai cikakken bayaninsu a shafin mata don haka ga macen dake da wannan matsalar ga abubuwan da zata dinga yi domin samun wadatuwar ni’ima a jikinta kamar haka.


1: Aya


2: Dabino


3: Mazarkwaila


4: Hakin daka


5: Nonon shanu ko madara


Idan kin samu wadannan abubuwan ga yadda zaku hada maganin, zaki sami ayari ki tsinceta tas sannan ki wanke ki shanya, idan ta bushe sai ki zuba a turmi ki dakata lukwi, kina gama dakawa sai ki tankadewa da rariya mai laushi.


Saiki daka dabinonki da cukwi da mazar kwaila da hakin daka lukwi ki hada shida dakakkiyar ayar da kika daka, ki samu roba mai kyau mai murfi ku zuba.


Ki dinga sha da madara peak ko kuma fresh milk danyen nono ko yoghurt me kyau, ba a bawa yaro

Post a Comment

Previous Post Next Post