Kalaman Soyayya Masu Dadi Wanda Yakamata Kuna Turawa Masoyanku

Kalaman Soyayya Masu Dadi Wanda Yakamata Kuna Turawa Masoyanku 




Wannan ne yasa Muka tsara muku Kalaman Soyayya Masu Dadi da Ratsa jiki.

Gasu anan kasa Asha Karatu Lafiya.

Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai!

Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki tagaskiya a gareni!

Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata!

Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na farko da nike roqo samu!

Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi!

Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi

farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata!

Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.

SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da

cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin

zuciya ta.

Ina son ka, me ya sanya ka ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka?

Tabbas kaine mutum na farko da haduwa da shin ya kore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da SADAUKI. Salim, ka yi nasara ka yi nasarar jan ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine na mallakawa linzamin zuciyata, kaine mutum na farko da na taba furtawa kalmar SO kuma a yanzuma zan kara mai-maitawa a gare ka ina son ka.

Ka amince mu yi tsaftatacciyar soyayya. Sai yanzu na gano cewa a duniya babu abun da ya kai samun masoyi dad’i, a duk lokacin da na rasaka ban san halin da zan shigaba, daga karshe ina mai sanar da kai cewa buri na yanzu bai wuce na ganin ranar da zaka zamo ango ni kuma na zamo mata a gare ka ba, ina alfahari da kai a duk inda na kasance, ka huta lafiya daga mai son ganin farin cikin ka a koda yaushe

Babban burina naga bayyanar fitar murmushi akan wannan kyakkyawar fuskar taki,yakuma zamana nine sanadin hakan.

Banason Allah yakawo lokacinda zaki fushi dani sosai,domin kaina bazai iya daukaba.

Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata! So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina!

Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke!

Hakika Allah ya wadataki da abinda mata dayawa suke nema sun rasa.

Bashakka mata irinku kadanne, ke, da ace na’iya rubuta labari,to da’akan kyawun fuskarki zan rubuta littafin mai suna KYAUTA DAGA ALLAH.

Kitallafi rayuwata data tsunduma cikin tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar data shagala akan tsanananin soyayarki,kada rintsi ko zugar mahassada yasa ki gujeni ko kuma kirage son dakike mani.

Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki

SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.

Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki! 

Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.

Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?

Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama.

Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke.

Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!

A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.

A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.

Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.

Kasan cuwar mu na ‘yan adam a doran ƙasa, Allah ya halicce mu ne don mu bauta masa kuma shi ne ya sanya soyayya da sha’awa a tsakaninmu. Saboda haka samarin da suke ƙoƙarin ganin mallakan zuciyar ‘ya mace ko kuma samun zuciyarta ba tare da wata mishkila ba, ga wasu hanyoyin guda takwas da ake bi don sace zuciyar budurwa.

1. TSARI: Duk wata ‘ya mace tana son ta ga namiji mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba. Abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha maras kan gado ba.

2. KYAU DA KWALLIYA: Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna soyayya da saurayi saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya kamar ɗawisu.

3. KALAMAI: Yana da kyau namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin duk wata ‘ya mace, rashin iya kalami kan janyo rashin masoyi. Maimakon haka sai ka zama tamkar ɗan bora a soyayya. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zaka birge budurwa.

4. KIRKI DA KULAWA: Namiji yakan tafiyar da zuciyar ya mace dalilin kasancewa mai kulawa da kirki. Misali duk bayan wani lokaci ko sa’ar da ba ta fi rana ɗaya ba, ko kwana biyu a ce kana zuwa ganin ta ko kuma kana kiran ta, idan ya yi yawa ne a ce kun haɗu sau uku. Musamman ma a irin wanan lokacin da wayar hannu ta zama ruwan dare. Wani lokacin idan haɗuwa ta yi ƙaranci sai ka kirata a waya. Amma fa ka sani yawan zuwa gun mace ko masoyiyarka ce wani zubin nasa gundura. Ma’ana za ta ji duk ta gaji da ganin ka, musamman idan ya zama soyayyar taku ba ta yi ƙarfi ba.

5. KAR KA RIƘA YAWAN YI MATA MAGANA GABAN ƘAWAYE: Ka guji yawan kula yarinya cikin sahun ƙawayenta ko kuma cikin jama’a. Hakan zai karama kima, sannan da nesan ta kanka ga barin wulakanci. Wata kila lokacin da ka je mata cikin jama’a ko ƙawayen ta, ta ji tana son ka. To amma watakila a lokacin shigar da ka yi bai yi mata ba. Hakan zai sa ta guje ka, wanda yin haka a soyayya wulakanci ne ga masoyi.

Mafi kyawu shi ne ka jira ta keɓance ko kuma ta koma gida. Idan ba haka ba, to sai dai idan sun kai koda su biyar ne, to kuma ya zama dole ku kasance ku biyar koda sauran ba sa san ‘yan matan. Saboda su kasance masu ɗauke masu hankali a lokacin da kuke hira kuma suma sauran ‘yan matan yin haka zai nuna cewa wadda kake so ba ta fita daban a cikin su ba. Duk abin da sauran ƙawayenta suka ce a kanka da shi za ta yi amfani.

6. BARKWANCI: Idan ka kasance mai raha ga masoyiyarka to nan da nan za ka sace zuciyarta. Misali ka riƙa ce mata a duk lokacin da ka zo hira da ita, amincin so gareki ya tauraruwan zuciyata, ɗaya tamkar da goma cikin sahun mataye, a do da kyau siffarki ce, murmushinki ke sanya zukata fara’a. gimbiya adon ‘yan mata. Da sauran su. Kana mai ambaton haka cikin murmushi da shauƙi irin na soyaya kuma dole ne hirarku ta kasance mai amfani ba ka yi ta zuba ba, har sai ka gundure ta. Yawan magana ba shi da tasiri a soyayya muddin ba magana ne masu ɗauke hankali da san ji ko rashin gundura ba.

7. KUƊI DA KULAWA: Mata suna son samun saurayi mai tashen kudi da kulawa cikin bukatunsu a koyaushe. Idan ta samu wanda ya haɗa waɗannan abubuwa kuma ya tafiyar da su yadda ya kamata, to abu ne mai sauƙi ya sace zuciyar budurwa. Akwai mazan da suke roƙon ‘yan matansu kuɗi; wannan ba soyayya ba ce, sai a kira shi a kwaɗayi.

8. KYAUTATAWA: Sai dai kuma duk da na yi bayani kan cewa kwaɗayi bashi da kyau a soyayya, hakan ba shi yake nuna ba za ka kyautatawa masoyiyarka ba. Hasali ma idan kai haka, to za ka ƙara ƙarfin shaƙuwa ne tsakanin ku da juna. Sai dai idan za a yi kyautaa duba me masoyiya take da buƙata a daidai wannan lokaci. Misali, kar ka kawo mata hoda a lokacin da take buƙatar turare, atamfa, yayin da ita kuma leshi take so.

Sanin haƙiƙanin abin da budurwa ke so, ko da ku fara soyayya da ita, ko ba ku fara ba, yana taimakawa ƙwarai wajen sace zuciyarta

Samfurin Kalaman Soyayya

Masoyiyata, ina son ki fiye da yadda kike so na. Ina son kasancewa tare da ke domin kina farantawa zuciyata.

Kallon ki kaɗai kan sanya in samu kuzari, duk wata kasala da lalaci in ji ta gushe. Ke ce farin cikina. Ina nan riƙe da amanar soyayyarki har ƙarshen rayuwata. Na saka a raina ba zan taɓa mantawa da ke ba.

Sonki tamkar wani fure ne da idanuwana suke ƙawatu wa da kallonsa, hanci ya ji daddaɗan ƙamshi, ruhi kuma ya samu nutsuwa. Idan rayuwa ba za ta yiwu ba tare da ruwa da iska ba, haka ni ma ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba.

Jin daɗi da walwala ba za su taɓa samuwa a tattare da ni ba matuƙar babu soyayyarki a cikin zuciyata.

Kin zama tauraruwa da ke haska ilahirin bishiyoyi da furannin da suke lambun zuciyata.

Post a Comment

Previous Post Next Post