Halin Da Zaka Iya shiga Idan Ka Dauki Lokaci Ba Tare Da Jima'i Ba
Ga wanda dama can bai tabayi ba, yanada sauki kamunwa da hadarin rashin yin Jima'i. Amma ga duk namijin daya saba kuma ya jima bai yi ba. Hakan na iya haddasa masa matsaloli a lafiyarsa.
Ga wasu illolin da mazan da suka jima ba Jima'i suke fuskanta akan lafiyarsu.
1:Matsalar Saurin Inzali: Kaman yadda mukayi bayani a baya, rashin saboda da Jima'i na jawo saurin zuwan kai, haka nan yawan Jima'i na magance saurin zuwan kai.
Ga duk namijin daya jima baiyi Jima'i ba zai samu matsalar Saurin Inzali a duk lokacinda ya tashi yin Jima'i.
2: Ciwon Maraina: Akwai wani cuta da likitoci suke kira prostate cancer. Wannan cutar yana shafar mafitsaran namiji ne da kuma haddasa masa cutar gwaiwa.
Binciken masana ya gano duk namijin da zai yi zuwan kai akalla sau 21 a duk wata, bazai kamu da irin wannan cutar na mafitsara ko na gwaiwa ba.
Duk namijin da baya samun yin tsome yadda ya kamata, akwai yiwuwar kamuwa da wannan cutar inji masana.
3: Ciwon Hawan Jini: Rashin samun yin Jima'i yadda ya kamata ga namiji na iya haddasa masa cutar hawan jini. Idan kuma daman yanada shi zai kara ruruta cutar.
Ganin yadda gudanar da Jima'i nasa mutum jininsa ya zagaye jikinsa yadda ya kamata. Haka rashin Jima'i nasa jinin mutum yayi sanyin da zai iya haifar masa da cutar hawan jini.
4: Yana Nakasa Garkuwa Jiki: Daukan lokaci mai tsawo ba tare da tarawa da iyali ba yakan ragewa sinadarin kariya na jikin mutum sunyi rauni, yadda kamar cuta tana iya addaban namiji idan ta kamashi.
Amma duk namijin dayake yi akai akai duk cutar data tinkaroshi bugu guda yake mata ta mace.
5: Ciwon Gabobi: Duk namijin da bai samun yin Jima'i yadda ya kamata a cikin kasala yake a kullum.
Yawan gudanar da Jima'i ga maza na sasu kasancewa cikin kuzari karfin jiki.
Wadannan sune wasu daga cikin illolin rashin samun gudanar da Jima'i ga duk wani namiji.
Don haka ga magidanta Maza ba abun burgewa bane su rika kin Jima'i da matansu akai akai ba.
A darasi na gaba suma mata zasu ci illar da rashin gudanar da Jima'i akai akai ga mazajensu.
Bamuce mara aure yaje ya kama zina ba saboda ya samu lafiyar da Jima'i yake samar wa. Magane da maza masu aure da suke kaucewa yin Jima'i akai akai da su muke magana.
Post a Comment