Yadda Zaka Goge Hakuranka Suyi Fari Tass
Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu yan uwa na barkan mu da wannan rana,barkan mu da wuni da fatan mun wuni cikin koshin lafiya.
Ba tare da bata lokaci ba ga yadda zaa goge hakuran da sukai baki ko ja ko suka dafe cikin sauki.
A NEMI
1. Citta danya
2. Lemon tsami
3. Gishiri
YADDA ZAA HADA
Da farko zaa bare bawon dake bayan citta,sai a yanki kadan a samu turmi a take ta,sai a kawo gishiri kadan a zuba a kawo lemun tsami shima kadan a hada a zuya sosai.
Sannan a sa burushi ana dangwala ana goge baki dashi sau 1 a rana tsawon kwana 3.
Insha Allah zaa ga sauyi sosai.
Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati.
LIKE AND SHARE.
Post a Comment