Wasu Kalamai Guda 12 Da Duk Mace Nason Jinsu Daga Bakunan Masoyansu:
Baya ga kudi, babu abunda mace take so irin kalamai na kambawa da kodata.
Kana iya yiwa mace kyautan kudi ta ki maka godiya, amma kalma guda zaka fadamata taji duk duniyan nan babu irinka.
Mace takan baiwa namiji da ya iya kalamai kokacinta fiye da namijin daya fi bata kudi. Kalamai sunkanyi saurin saka mace farin ciki fiye da kudi. Don haka maza da yawa suna kasa shawo kan wasu matan da suke sone saboda rashin sanin kalaman da zasu kambamasu da su.
Ga wasu kalmomin guda 12 muddin zaka furtawa mace su a lokacin da ya dace, tabbas zaka samu hankalinta da soyayyar ta cikin karamin lokaci.
1: Ka Yaba Basirarta: Duk mace tana son jin mai sonta ya gano wani basira datake da shi kuma ya kambamata akan sa.
Don haka gano baiwa ko basiran da Allah Yayiwa macen da kake so zugata da shi zaka ga irin farin cikin da zaka sata.
2: Ka Yaba Tarbiyarta: Mace nason jin mai sonta ya yaba da tarbiyar datake da shi. Hakan na nuna mata mai sonta ya gamsu da irin tarbiyan da iyayenta suka mata kenan. Hakan kuma na sata jin dadi da kaunar mai yabon nata.
3: Ka Nuna Mata Ita Dabance: Kayi kokarin nuna mata ba dai-dai take da sauran mata ba. Nuna mata irin dace da sa'ar da kayi wajen samunta.
Bata misali da wani abunda kasan ba duk mata ake samunsu da shi ba amma ita tana da shi. Mata suna son jin sunada wani abunda ba kowa yake da shi ba.
4:Ka Yaba Halittar Ta: Mace duk muninta tana son ya bi kyauta. Haka duk kyaunta tana so taji an maimaita mata kalmar tana da kyau.
Sanar wa wacce kake so irin kyaun data ke da shi a idanuwanka. Tabbatar mata irin dacen da akayi wajen samun masoyiya mai irin kyauta. Nuna mata zakuwarka na son ganin ta haifa maka kyauwawan yara irinta.
Muddin zaka yiwa mace kalaman irin kyaun da Allah Ya mata. A wannan ranar babu kyautar da zaka mata da yafi wannan a wajenta.
5: Yaba irin Iya Kwalliyar Ta: Mata suna burin jin an kambama kwalkiyarsu. Don haka sanarwa taka irin yadda ado da kwaliyar ta suke rudaka.
Fahimtar da ita irin yadda daurin adikonta yake sa kake kara yiwa Allah Hamdala. Duk randa ta fito taji baka ce komai game da kwalliyar ta ba. A wannan ranar ka kula zakaga bata cikin walwala. Idan kuwa macece mai magana sai ta tambayeka kodai bata yi kyau bane yau.
6: Fadamata Yadda Kake Ji Idan Kana Tare Da Ita: Nunawa wacce kake so irin shauki, nishadi da sarautar da kake ji idan kana tare da ita.
Mata suna son jin cewa da akwai wani abu na musamman da mai sonsu yake ji idan yana tare dasu. Sanarda ita irin girman annashuwan da kasancewa tare da ita yake saka.
7: Fadamata Irin Rayuwar Da Kake Fatan Yi Da Ita Idan Kunyi Aure: Furta mata, ko bayyana mata irin yadda kake burin zaku yi rayuwarku a matsayin miji da mata bayan aurenku yakan sa mace taji ta matsu ta ganta a gidanka.
Nuna mata irin tanadin da kayiwa rayuwarku na aure. Tabbatar mata da rayuwace zakuyi ta masoya na har abada ba na uban gida da 'yar aiki ba.
8: Nuna Mata Yadda Haduwar Ku Ya Sauya Maka Rayuwa: Ka sanar da ita halin da kake ciki kamin soma soyayya da ita.
Sanar mata yadda haduwar ku yasa ka fahimci zahirin abunda ake nufi da kalmar so. Tabbatar mata da irin farin cikin da take sake tun bayan haduwar ku a matsayin masoya.
9: Zo Mata Da Neman Shawaranta: Zowa wacce kake nema da aure neman shawara koda kuwa ka riga da ka yanke hukunci a zancen da ka zo mata da shi.
Nuna mata shawaranta kadai kake so domin aiwatar da wannan abun. Muddin zaka yiwa mace hakan to insha Allah babu Mai shiga tsakaninku cikin sauki. Mace na son ganin ace da shawaranta aka aiwatar da wani abu.
10: Tabbatar Mata Yadda 'Yan Uwanka Da Abokanka Suke Sonta: Duk mace na son ganin ta samu karbuwa wajen yan uwa da kuma abokan wanda zata aura. Hakan na kara bata tabbacin cewa zata samu kwanciyar hankali a gidan mijinta.
11: Ya Ba Mata ka Kuma Sa Mata Albarka A Duk Abunda Ta Maka Na Jin Dadi: Ka kasance mai yawan yabawa da kuma mata fatan alheri a duk lokacinda tayi wani abun da ya saka farin ciki komai kankantarsa.
12: Sanar Da Ita Yadda Murmushinta Yake Debe Maka Kewa. Dariyarta Yake Saka Farin Ciki. Farin Cikinta Yake Maganin Matsalolinka
Muddin namiji zai dabi'antu da yiwa wacce yake so wadannan kalaman. Ba kasafai mace zata iya tsayawa da wani ba shi ba na mintuna 3 ta saurareshi.
Gayu sai ayi kokari
Post a Comment