Wasu Abubuwan Da Baka Gama Saninsu Ba Game Da Nonuwan Macce

 Wasu Abubuwan Da Baka Gama Saninsu Ba Game Da Nonuwan Macce 



Ba duk maza bane suke da kwarewa akan sanin halittan nonuwan mace ba. Wannan ne ma yasa dayawa daga cikin maza basa iya amfani da nonuwan matansu wajen jiyar dasu dadi kamar yadda ya kamata.


Ga wasu abubuwan da kamata ka sani game da su nonuwan mace.


 

1: Kowace mace da irin fasalin nonuwanta.

Maza sukan dauka duk mace, ko akasarin mata irin nonuwansu guda ne. Ba haka bane. Kowace mace da yadda fasalin nata nonuwansuke kamar yadda tafin hannunta daban ne zanensu dana kowa.


2: Nonuwan mata suna kara girma kuma su sake raguwa.


Akasarin maza na daukan cewa yadda nonuwan mace suke haka nan zasu kasance babu wani sauyi. Sam ba haka abun yake ba.


A duk lokacin da mace take shirin yin al'ada nonuwanta sukan kara girma. Hakan idan mace tana da ciki. Bayan ta gaba al'ada ko ta yaye sai kuma su ragu. Wannan yasa akasarin mata idan sun kusa soma al'ada ba dukkaninsu bane suke so a taba musu nonuwansu ba saboda yana musu zafi a dalilin girman nan daya kara.


Nonuwan mace suna iya raguwa a lokacin data rame, amma irin na ciwo bana daidaiton jiki ba.


3: Wani abunda al'ajabi da nonuwan mata yake dasu da maza basu gano ba shine. Kowace mace nonuwanta sun dace da halittar ta.


Dubi wacce take kusa da kai a yanzu. Idan ka dubeta da kyau zaka ga cewa ba domin tsarin da take dashi ba nonuwanta ba zasu dace da ita ba.

Ana samun jimgegiyar mace sai a ganta da kananun nonuwa. Haka nan ana samun wata irinta da manyansu. Kamar Yadda ake samun tsirara da kananan nonuwa da kuma manya. Ko wacce da zaka dubeta da kyau muddin dai halittunta sun gama cika, sai ka ga abunda ke kirjinta sun dace da ita.

4: Bayaga kan nonuwan mace suna kara tsawo da fadi a lokacin da mace ta bukatu da mijinta. Abunda Maza da dama basu sani ba shine. Su kansu nonuwan mace suna kara girma da cika a daidai lokacin da take Jima'i da mijinta. Tana gamsuwa zasu koma yadda suke.

5: Daidai bukatuwar da jariri yake dashi na nonuwan uwarsa, daidai yadda jikinta yake samar dashi idan tana cin mai kyau.

Masana sunce mace zata iya baiwa jaririnta nono na tsawon watanni 6 ba tare da bashi wani abinci ba kuma ruwan nononta na nan.

6: Masana sunce mata suna dauke da kalolin nonuwa sama da guda 1000. Sai dai akwai guda 7 da sune suka fi shahara a kirazan yawancin mata.

Haka suma kan nonuwan mata wato nipples suna da yawa kowanne da kamanninsu. Amma mafi shahara inji masana guda 8 ne.


Ga jerin sunayen irin nonuwan da suka shahara a kirajen mata.


Ustaz Usman ya taba lissafo sunayensu da Hausa.

Round

East West

Side Set

Tear Drop

Slender

Asymmetric

Bell Shape

7: Abunda maza da yawa basu sani ba game da nonuwan mata shine. Wasu matan idan suna shayarwa suka kamuwa da sha'awar Jima'i.

Akwai matan da kai tsaye shan ko tsotson da yaro ke musu ke sasu sha'awa. Wasu kuma hakan na tuna musu mazansu ne sai sha'awa ya taso musu.

8: Yawancin maza suna dauka tarin kitsai ne ke habaka nonuwan mace, sai dai kutsai na hade ne da wani soso ko kulatai mai suna fibrous a turance da suke haduwa su samar da nonuwan mace suyi kyaun gani.

9: Ta inda maza da dama suke canka ba daidai ba shine ta tunanin duk yadda ka taba nonuwan mace zata ji dadi.

Kowace mace da abunda ke tayar mata sha'awa idan an mata wasa dasu. Wasu matan ma kwatakwata basa jin wani sha'awa idan aka taba musu nonuwa.

Don haka kayi kokarin gano yadda matarka take so ka tabamata su. Ba ka kamasu da sha ko murza karma ka samu gyada ba.

10: Duk wata mace nonuwanta guda biyu girmansu ba daya bane. Na dama yanafin na hagu girma akasari.

Da fatan wannan bayanin zai amfani maza musamman masu aure.

Post a Comment

Previous Post Next Post