Illolin Da Madigo Lesbian Ke Haifarwa A Jikin Macce
Yana daga cikin babbar musifa a wannan zamani, yaɗuwar madigo tsakanin Zawarawa da ƴammata da matan aure.
Madigo shine mace ta nemi mace ‘yar uwarta, domin taji dadi da ita, ta gamsar da ita kamar yadda namiji zai gamsar da ita.
Madigo wanda a turance ake kira da lesbianism yana nufin saduwa ta hanyar gogayya tsakanin mace-da-mace ta amfani da halittarsu, domin kauda sha’awar junan su. Idan wannan ya kasance a tsakanin namiji da namiji to ya koma luwadi kenan. Wal iyazu billah!
Wannan musifa da bala'i na neman jinsi ya faro ne tun daga zamanin Annabi Lut (AS). Wanda tarihi ya nuna cewa shaidan ne yazo a cikin siffar ‘yan Adam, ya nuna wa mutanen Annabi Lut (AS) yadda zasu rinka neman junan su.
Hadin Karin Girman Azzakari Dannan NAN domin karantawa
A yau, an wayi gari duniyar kimiya da fasaha musamman duniyar yanar gizo (internet), na daya daga cikin hanyoyin da ke koyar da wadannan munanan dabi’u, musamman a social media, inda zaka tarar a can da suna yi a boye, yanzu kuwa sun fito fili har groups su ke da shi daban-daban a Facebook, WhatsApp da sauran su.
Wani abin takaici shine, sai ka tarar har da Musulmai.
Wannan sharrin yahudawa ne, kuma sannu a hankali suna samun nasara a kan mu!
Madigo da luwadi wata mummunar dabi’a ce da ko dabbobi mafi yawa basa neman jinsin su, amma sai gashi ya bayyana ga ‘yan Adam. Allah ya la’anci mai yin sa. Kuma wanda duk Allah ya la’ana to wallahi babu shi babu albarka a rayuwar shi. Kuma babu shi babu samun alkhairin duniya da na lahira har sai ya tuba.
Biyewa sha'awa da son zuciya, da bin bayan dabbobi a surar mutane, har takai, an fara samun auratayya tsakanin jinsi gida mace da mace namiji da namiji, wal iyyazu billahi.
Mala’iku suna da hankali amma basu da sha’awa. Mutane suna da sha’awa kuma suna da hankali. Su kuwa mafi yawan dabbobi suna da sha’awa amma basu da hankali. A nan, a duk lokacin da hankalin dan Adam ya rinjayi sha’awarsa to sai ya koma daga cikin mala’iku,
Post a Comment