Me yake faruwa dani Nonona guda yafi guda girma?

Me yake faruwa dani Nonona guda yafi guda girma? 



Wannan tambaya ce da yakamata masu wannan matsalar su san amsarta

"Ɗan maraina na ɗaya yafi gudan girma."

"Nonona guda yafi gudan girma."


"Gabana baya da girma idan yana kwance sai idan ya miƙe."


Bincike ya nuna cewa mutane maza da mata nada yawan damuwa dangane da yanayin halittar jikinsu, musamman ɓangaren jikin mu da ba'a bayyanawa saboda tsiraici ne . Sabili da al'ada da kunya, mutane najin kunyar su bayyana damuwarsu ga ƴan uwansu dangane da tsiraicinsu da abinda suke gani na halittarsu wanda suke jin kamar ya sha banban da sauran mutane, wanda kuma suke ganin kamar matsala ce ko tawayar halittarsu. Bugu da ƙari, saboda bama tattaunawa tsakanin abokai da 'yan uwa akan tsiraicin mu, kuma bama ganin tsiraicin juna zaiyi wahala mutum yasan cewa mutane da yawa nada irin damuwarsa , cewa bashi kadai bane ko bake kadai bace mai irin wannan damuwar wacce kuma ba lallai bane matsala ce tare daku ba.


Idan muka tattara wadannan bayanan na ƙorafi a sama , zamu ga cewa ƙorafe-ƙorafen mutane akan abinda yake ci musu tuwo a ƙwarya guda 3 ne kamar haka:


1. Ɗan maraina ɗaya yafi gudan girma

2. Nono ɗaya yafi guda girma

3. Zakarin da baya da girma idan yana kwance sai idan ya miƙe.


1. Ɗan maraina ɗaya yafi gudan girma:


A yanayin halittar ƴaƴan maraina dama can ɗaya yafi guda girma ga mafi yawancin mutane . Mafi akasari ƙwallon maraina na dama yafi na haggu girma da kaɗan. Wasu mutanen kuma ƴaƴan maraina nasu na haggu sunfi na dama girma (the asymmetrical nature of testicles). Wannan ba abinda damuwa bane (it's normal). A lura idan maraina suka saki, na dama ko na haggu yana saukowa ƙasa kaɗan akan gudan wanda yayi sama kaɗan a jakar maraina, wannan saboda nauyin wanda yafi girma ne. Wanda yayi ƙasa kamar a sikeli shine wanda yafi girma. Amma idan akwai ƙululu daka lura dashi a cikin maraina wanda kake ji idan ka taɓa ko wani curin nama , ko kuwa daga baya ne ka lura cewa ɗan marainanka guda yana ciwo ko yana ta ƙara girma fiye da gudan , ko ya shanye, ko ya canza siga ba kamar gudan ba, ko kumburi , to shine ya kamata ka damu , wato kaje asibiti da wuri ko wata cibiyar lafiya domin bincike da neman magani. Bincika lafiyar maraina da kanka akai-akai zai taimaka maka domin sanin lafiyarsu da gujewa cutar ciwon daji ko wani ciwo da ka iya shafarsu ba tare da ka lura ba da wuri. Hakan zai baka damar zuwa asibiti ko wata cibiyar lafiya domin magance wata matsala kafin ta girma ko tayi maka illa. A kula da lafiyar maraina kyau, sune masana'antar maniyyin namiji domin samun haihuwa, kada a saka wando wanda zai matse su ya cutar dasu ko a dinga yawan zauna su, musamman idan suna da girma.


2. Nono ɗaya yafi guda girma:


Kamar dai yanda maza suka damu akan lamarin maraina, basa so ace daya yafi guda girma , suma mata ba'a barsu baya ba wajen irin wannan damuwa ta rashin sani akan yanayin nonuwa, wato tsoron ko matsala ce cewa nono ɗaya yafi gudan girma. A yanayin halitta , mafi yawancin mata nonansu guda yafi ɗayan girma ( the asymmetrical nature of breasts) koda kau kaɗan ne ta yanda ba'a iya lura sosai . Nono ɗaya zai iya fin guda girma ko cikowa, ko yanayin zamansa a ƙirjin mace yasha banban da gudan. 


Wannan abune game gari kuma ba abinda damuwa ba. Amma idan ya kasance kina ganin ɗaya daga cikin waɗannan alamomin to kada kiyi wasa, ki garzaya zuwa asibiti domin gano matsalar da magance ta. 


Alamomin sune: Canjin girman nono or "shape" wanda kika gani baƙo, jin ƙululu ko wuri mai tauri cikin nono fiye da sauran wurare , canjin yanayin fatar nono ko lotsawar nono, kalar ja ga fatar nono, ko ƙuraje akan fatar nono ko kusa da kan nonon, ko shigewar kan nono ciki, ko canzawar wajen zaman kan nono ko canzawar sigarsa, fitar wani ruwa daga nono ba tare da an matsa ba, jin ciwo/zafi ga nono ko hammata a koda yaushe, kumburi ga hammata da sauransu. Bugu da ƙari, akwai fitar ruwa daga nono wanda baya da nasaba da ciwon daji (kansa) , juna-biyu ko shayarwar mace.

Abin lura anan shine: Mama na canzawa lokacin juna-biyu ko shayarwa, ko lokacin al'ada (haila) da yaye , don kada canjin yanayin mama yasa ki jin tsoro. A lokacin juna biyu ko shayarwa, misali, akwai jin ɗan ciwo akan nonuwa, ƙarin girman mama, komawar fatar dake zagaye da kan nono launin baƙa, da kuma samuwar ruwan nono. A lokacin yaye yaro ma , nonuwa na ciwo na wani ɗan lokaci.


Don haka, yana da kyau sosai mace mai aure, budurwa ko zawara ta lura da yanda yanayin mamanta yake da kuma yanda take jinsa don gudun matsalolin lafiya da ka iya shafarsa kamar sankarar mama/kansar nono (breast cancer) ko wani ciwo na daban. Sa'annan a kiyayi shafa magunguna ga mama, musamman magungunan kemical (chemicals) na turawa wanda zamani yazo dasu domin karin girman mama, ko tsaida su tsaye. Suna da hadari ga lafiya. Bugu da ƙari, mace ya kamata ta dinga duba lafiyar mamanta da kanta akai-akai, hakan zaifi sauƙi idan kinje yin wanka a lokacinda jikinki keda santsin ruwa da sabulu , ki dinga laluba mamanki biyu da yatsu domin neman jin ko akwai wani canji a cikin su, ciwo, tauri ko ƙululu da yasha banban da gudan mamanki. Wannan zai taimaka sosai domin ankara da ƙululun ciwon daji (cancerous tumour) da wuri ko wani ƙaululu wanda bana ciwon daji ba (benign/non-cancerous tumour) domin magance matsalar.


3. Zakarin da baya da girma idan yana kwance sai idan yana miƙe:


Wannan ƙorafi ne na uku da muka fi samu daga wajen mutane. Ance rashin sani yafi dare duhu inji masu iya magana; wannan zance haka yake. Rashin sani ne yasa zaka ga mutane na tunanin wai matsala ce cewa zakarinsu baya da girma idan yana kwance (flaccid state) , wai sai ka ga har neman magani suke yi, wai ataimaka masu da magani, amma kuma idan ya miƙe (in erect state) yana da girma da tsayi sosai. Wannan yanayin halitta ne ba matsala bace Malam. To minene abin damuwa tunda idan ya miƙe yana fitowa da wadatarsa? Masana sun kasa maza gida biyu, a yanayin halittar alƙalummansu , wato (1) SHOWERS da (2) GROWERS a yaren turanci. (1) SHOWERS sune maza wanda gabansu yana da girma a lokacinda yake kwance (flaccid state) amma idan ya mike (erect state) baya wuce girmansa na kwance ko baya ƙara girma sosai. (2) GROWERS kuma a gudan ɓangaren, sune wanda zakarinsu baya da girma idan yana kwance (flaccid state) , wani lokacin kamar na yara idan bai tashi ba, amma idan gabansu ya mike (erect state) yana ƙara girma sosai, tsayi da kaurinsa. Wadannan bayanai na nuna cewa SHOWER zakari ne babba a kwance amma baya ƙara girma yanda ake tsammani idan ya mike, shi kuwa GROWER karami ne a kwance amma da zaran ya miƙe zaya bada mamaki dangane da girman da yayi daga ƙaranta, wato tamkar yana shigewa gareji ne kuma ya fito da girma idan ya tashi.


Rubuta wa madina islamic medical center 

Katsina Nigeria

Post a Comment

Previous Post Next Post