Matsalar Ciwon Nono Abinda Ke Haifar Dashi Da Kuma Ingantaccen Maganinsa

Matsalar Ciwon Nono Abinda Ke Haifar Dashi Da Kuma Ingantaccen Maganinsa



Koda yake kaso tamanin da biyar cikin dari (85%) na mata masu ciwon nono masu shayarwa ne amma ana samun wadanda basa shayarwa suna kamuwa da ciwon sakamakon amfani da magungunan turawa musamman na shafawa dan haka abu na farko da zakiyi dan kiyaye kanki daga ciwon nono shine rabuwa da magungunan.


Me shayarwa akwai hanyoyi da zatabi domin riga kafin kamuwa daga cutar misali yin bacci da nono a bakin yaro,

kodai kwanciya da rigar nono (brezia) ko kuma kwanciya rubda ciki. mace me manyan nono lokacinda take shayarwa ana bukatar ta rage duk wani abu dayake jijjiga nono kamar tsalle ko daurin kirji wadannan suna saka nono shan wahala daga bisani yayi ciwo.


Bawa yaro nono daya abar daya yana kawo kankancewar daya sai kaga nono daya yafi daya ko kuma yawan kwanciya akan daya wannan shima dole mace ta kiyaye idan kuma hakan ta faru sai acigaba da maganin gyaran nono ahankali zai dawo kafin ki sake wani shayarwar.

sannan dole ki kiyaye da bawa yaro nono koda kina bada reno ki tabbatar yaronki yanasha kullum


Domin rashin shan nonon yana kawo ruwan yayi yawa daga karshe yayi ciwo wannan shine kuskuren da wasu mata keyi idan sun bada reno sai ayi kwanaki ana bawa yaro madara kuma daga baya adawo bashi nono.


DANWURI

Post a Comment

Previous Post Next Post