Maganin Ciwon Mara Da Maganin Haɗin Karin Ni'ima Da Haɗin Matsin Ciki Da Wajen Gaban Macce.

 Maganin Ciwon Mara Da Maganin Haɗin Karin Ni'ima Da Haɗin Matsin Ciki Da Wajen Gaban Macce.



Kamar yadda nayi rubutu dazu game da wadannan suka wada magunguna da muke kawowa da kuma wanda ake so mu kawo wasu sunyi tambaya game da na ciwon mara na mata to gashi nan.


   Wannan ciwo kusan yana addabar mata da yawa 'yan mata da matan Aure kusan wasu duk lokacin Al'ada idan zata zo suna yawan samun viwon mara wasu ma Al'adar tasu tana rikicewa ko jinin ya rika zuwa kadan kadan ko yazo yaki tsayawa.


To duk mai fama da irin wannan damuwa insha Allah indai aka bi wannan hanya insha Allah zaa samu waraka.


ABINDA ZAA NEMA.


1. Garin Habbatussauda

2.Garin Tafarnuwa

3. Garin Zogale

4. Garin Kusdul hindi


YADDA ZAA HADA 


Zaa samu gatin kowanne kamar chokali 5 sai a hade waje daya a rika diban chokali 1 ana dafawa da ruwa kofi 2 idan ya dawu sai a sauke a tace a sha kofi daya safe daya yamma,zaa iya saka zuma ko sukari kafin a shah


FA'IDODIN HABBATUS SAUDA (3)

**********************************

12). Binciken Manyan Likitocin zamani ya tabbatar da cewar: Habbatus Sauda tana Qarfafa Garkuwar Jiki. don haka ana kyakyawan zaton cewar masu fama da chutar AIDS idan suna amfani da ita (mai ko gari) zasu samu Qarin lafiya sosai ajikinsu.


Asamu zuma mai yawa (kamar kofi 3) asanya garin H/sauda cokali 7 garin Zaitun cokali 4. Garin zogale cokali 3. Asanya citta da kayan Kamshi aciki. sannan agauraya arika shan cokali 2 safe da rana da yamma kafin cin abinci.


Wannan fa'ida zatayi amfani ga masu fama da cutar AIDS, cutar SIKILA, TYPOID FEVER, etc.


13. Habbatus Sauda tana maganin kurarrajin Baki dana Makogoro idan ana kurkura bakin da ita kuma ana hadiyanta bayan an dumamata kadan. 


14. HABBATUS SAUDA tana maganin matsalar TSAKUWAR MARA, APPENDITIXS, da sauransu. idan ana shanta da zuma.


15. Habbatus sauda tana magance matsalar rashin haihuwa. Matar da take da wannan matsalar, ta rika soya 'ya'yan Habbatus sauda tana gaurayawa da zuma tana taunasu tana cinyewa. Kamar cokali biyu safe da yamma kullum. 


In sha Allahu koda tana da dattin mahaifa ko rikicewar jinin Al'ada, komai zai daidaita. 


16. Habbatus Sauda tana maganin basur. Idan aka hadata (garinta) da garin ganyen sabara, ana tafasawa ana shan ruwan, Kofi guda kullum da safe. 


LIKE AND SHARE.

Post a Comment

Previous Post Next Post