Laushin Fata Da Kuma Qara Mata Taushi Da santsi

 Laushin Fata Da Kuma Qara Mata Taushi Da santsi



Mata da dama na son gyaran fata da jiki. Fata mai laushi da sheki ba ta cika nuna ainihin shekarar mai wannan fatar ba. Matan da ke yawan kulawa da fatarsu sai a ga kamar ba su wani tsufa ba, nan kuwa an dade ana bugawa da su. Kulawa da fatar jiki ga ’ya mace dole ne, domin dada kima a fuskar mai gida da kuma jama’a. A yau na kawo muku hanyoyin da za a bi domin samun fata mai laushi mai sheki.


MATAKAI:


1)- A rage dadewa a cikin rana, domin rana na kodar da fata matuka. Sai dai idan za a rika amfani da man shafawa, wanda ke dauke da sinaren SPF wadda ke kare fata daga kunar rana.


2)- A kasance ana wanke fuska da sabulun wanke fuska a kullum kafin a kwanta bacci, sannan a daina kwanciya da kwalliya a fuska. Sinadaren da aka yi kayan kwalliyar na sanya wa fatar fuska kuraje muddin ba a wanketa ba.


3)- A dage da shan ruwa sosai kamar kofi takwas a rana. Yawan shan ruwa na taimakawa wajen wanke maikon da ke kunshe a fata, wande ke haifar da kuraje.


4)- Amfani da mayuka masu sanya fata laushi da sheki na matukar taimakawa wajen sanya fata sheki da kuma laushi


5)- Yin dilka a kalla sau daya a wata na taimakawa wajen fitar da matattun fatar da ke saman fuska, domin bai wa sababbin fata damar fitowa da kuma yin sheki.


 


6)- Samun isasshen bacci na taimakawa sosai domin fata na son hutu. A rika samun baccin a kalla awa bakwai zuwa takwas da dare zuwa wayewar gari.


7)- Wanka da ruwan kabeji, wanda aka tafasa ya na sanya fata sheki da kuma laushi.


#Alfullaty

Post a Comment

Previous Post Next Post