Abin da ya kamata ka sani game da ƙaba da abubuwan da ke janyo ta.

Abin da ya kamata ka sani game da ƙaba da abubuwan da ke janyo ta. 



A ciki akwai abin da ake kira da "bangon ciki". Bangon ciki ya ƙunshi yaɗi, tsokoki, kitse da kuma fata daga waje. Wannan bangon ciki shi ne yake tare da ƙayan ciki kamar su tunbi, hanta, hanji da sauransu.


Ƙaba, wato "hernia" a turance, tana nufin kutsowar ko bullowar kayan ciki, musamman hanji, ta cikin yaɗi, ta cikin raunanan tsokoki, ta cikin kitse sannan ya tsaya a ƙasan fata. 


Saboda haka, ƙaba tana faruwa ne saboda raunin tsokokin bangon ciki da kuma yunƙuri.


Ƙaba tana iya samun maza da mata, kuma a kowane shekaru. Sai dai, tsofi sun fi fuskantar barazanar samun ƙaba. Haka nan, maza ne kaɗai ke samun irin ƙaba mai sauka cikin jakar maraina.


Sau da yawa, ƙaba ba ta ciwo da farko kuma ba ta da haɗari ga rayuwa. Amma tana iya zama haɗari idan hanji ya ƙulle ko ya saƙale a cikin ƙabar. Domin ƙullewar hanji zai iya janyo ruɓewa ko lalacewar hanji. Idan hakan ta afku, tiyatar gaggawa na zama tilas!


Ƙaba tana iya bayyana ko fitowa a sassan ciki daban-daban kamar:


1. Saman cibiya


2. Ƙasan cibiya


3. Ƙwibin hagu ko dama


4. Marar hagu ko dama


5. Matse-matsin cinyar hagu ko dama


6. Ko kuma idan ƙaban mara ya zarce ko ya sauka zuwa ciki maraina, hakan zai haifar da ƙaban jakar maraina.


Babbar alamar ƙaba ita ce bayyanar bulli a guda daga cikin sassan ciki da aka ambata a sama. Kuma bullin yana bayyana yayin da mutum yake zaune, tsaye ko kuma idan mutum ya yi ayyukan yunƙuri kamar ɗaga nauyi, tari ko atishawa. Sannan bullin ƙabar yana ɓacewa yayin da mutum yake kwance.


Abubuwan da ke iya sabbaba ƙaba sun haɗa da:


1. Tawayar cikar halittar tayi da ta haɗa da bangon ciki.


2. Shekaru


3. Lahani ga bangon ciki daga bugu ko tiyata.


4. Ɗaga nauyi ba daidai ba yayin atisaye.


5. Matsanancin tari tsawon makonni.


6. Juna biyu ko goyon ciki.


7. Ƙiba ko teɓa, da sauransu.


Tiyata ita ce sashihiyar hanyar gyaran ƙaba. Da zarar ka ga bayyanar wani baƙon bulli a ciki, tuntuɓi likita.


Daga ƙarshe, ƙarfafa tsokokin bangon ciki ta hanyar keɓaɓɓen atisaye zai iya rage haɗarin samun ƙaba. Haka nan, bayan tiyatar ƙaba kuma, likitan fisiyo na taimakawa wajen dawowa tare da haɓaka aikin tsokokin bangon ciki domin cin moriyar tiyatar da kuma kiyaye sake fitowar ƙaban.


Post a Comment

Previous Post Next Post