Me Ke Kawo Matsalar Cin-Ruwa A Kafa?

 Me Ke Kawo Matsalar Cin-Ruwa A Kafa?



Dokta Auwal Bala


A irin wannan lokaci na damina ana yawan samun korafin matsalar cin-ruwa. Cin-ruwa wani nau’in ciwon fata ne da kwayoyin cuta kan kawo a kafafu.


Wato ke nan ba ruwa ne ke cin fatar mutum ba, a’a kwayoyin cuta ne ke cin fatar mutum.


Amma dai an fi samun matsalar a masu tu’ammuli da ruwa, kuma an fi samun matsalar a irin wannan lokaci na damina saboda yawan danshi, tunda kwayar cutar tana son danshi sosai.


Su wadannan kwayoyin cuta da ake kira fungus wadanda suka fi rayuwa a wuri mai danshi kamar wurin wanka da jikin tawul ko kayan wanka ko cikin takalma masu danshi, su suke kawo wannan ciwo.


Ciwon na da wuyar sha’ani in ya fara damun mutum, kuma wani kan dauki wannan kwayar cuta in ya yi amfani da kayan wanka ko takalman mai wannan ciwo.


Yaya alamun cin-ruwa suke?


Cin-ruwa ya fi shafar mutanen da suke mu’amala da ruwa kamar masu sana’ar wanki ko mata masu yawan aiki da ruwa a cikin gida ko mutane masu yawan gumi ko zufa a kafa musamman in sun sa takalmi kafa ciki (sau-ciki).


Ya fi kama kafafuwa a tsakanin ’yan yatsu musamman na biyun karshe. Yakan kama kafa daya ko ma duk biyun.


Wani lokaci har tsakanin yatsun hannu akan gan shi.

Karanta Wannan: Haɗin Ƙarin Ni'ima Da Kuma Yadda Za'a Rabu Da Infection Mai Saukin Hadawa Ne 

Za'a ga wurin ya cabe yana fitar da farin ruwa yana saba har a zo fatar wurin ta cinye, wurin ya yi rami.


Wani zubin yakan yi zogi ko kumburi.


Hanyoyin kariya daga cinruwa


Idan aka kiyaye da tsabtar jiki da ta gidan wanka da kayan wanka da ta takalma, aka kuma bi hanyoyi da za a zayyana a kasa, to ba shakka za a yi adabo da wannan ciwo


A rika tafasa kayan wanka kamar soso da tawul a ruwan zafi akalla sau daya a wata domin kashe kwayoyin cutar

A rika shanya wadannan kayan wankan kuma a rana a kullum bayan an yi wanka domin rana tana kashe wadannan kwayoyin cuta


Mai wannan ciwo mai sana’ar wanki walau na kaya ko na mota su rika sa takalma irin na ruwa na roba yayin aiki don gudun jikewar kafa


A rika wanke gidan wanka a gida da sinadarai masu karfi akalla sau daya a mako, na jama’a kuma a kullum, sannan a rika budewa suna shan rana


Idan akwai yawan zufa a kafa to sai mutum ya rika yawan tsane kafar, ko ya rika barbada hoda a tsakanin ’yan yatsun, ko ya yi amfani da safa mara kauri kafin ya sa takalmi kafa-ciki. In aka cire a shanya safar da takalmin a rana


Mai yawan samun ciwon ya guji takalmi sau-ciki gaba daya, domin ita ce hanyar warkewa ba tare da ciwon ya dawo ba

Kada a yi amfani da kayan wanka ko tawul din mai cin-ruwa don gudun yada ciwon

Ga mai wannan ciwo, in an je wanka a wanke tsakanin ’yan yatsu sosai a kuma tsane wurin da tishu mai tsabta

Da zarar an ga matsalar to a je a ga likitan fata wanda zai ba da maganin da ya dace, don akwai magungunan shafawa iri-iri na wannan ciwo, ita ma hanyar kariya ce.

Post a Comment

Previous Post Next Post