Maganin Warin Jiki Mai Kyau Mai Saukin Hadawa

 Maganin Warin Jiki Mai Kyau Mai Saukin Hadawa



Warin jiki na daya daga cikin abubuwan da ke janyo tsana a tsakanin jama’a, musamman lokacin zafi, idan aka hada gumi ko aka yi yawo a rana sai warin jiki ya rika tashi. A kan samu warin jiki ne saboda yanayin gari ko an haifi mutum da shi ko kuma ta irin abincin da ake ci. Kamar masu yawan cin tafarnuwa daga sun motsa sai an ji warinta. Don haka ne a yau na kawo muku hanyoyi mafiya sauki da za ku bi domin magance warin jikin.

Turare: yawan fesa turare na jiki ko na hammata ko na tufafi na magance warin jiki. Amma ku sani yawan amfani da turaren jiki da na hammata na sanya kuraje.

Sabulu da ruwa: hanya mafi inganci wajen magance wannan matsalar ita ce, amfani da tsaftaccen ruwa da sabulu, don yin wanka kamar sau uku a rana, kuma ku dage wajen wanke lungun da ke janyo wari kamar hammata da sauransu.

Wankakken tufafi: kada ku manta duk yadda mutum ya kai ga wanka idan tufafin da yake sanyawa masu datti ne, to lallai ba zai rabu da wari ba. Domin haka ana son ku rika sanya tufafi mai tsabta musamman wanda ake sanyawa a ciki, kamar dan kamfai da rigar mama da sauransu.

Amfani da sinadarin Alam: Idan warin jikinka ya kasance mai tsanani ne, to sai ka rika sanya sinadarin alam a ruwan wankanka kafin ka yi wanka, hakan zai magance maka warin jiki.

Zuma: bayan ka yi wanka za ka zuba kamar cokali daya na zuma a ruwan dumi, sannan ka watsa a jiki, hakan na rage warin jiki.

Shan ruwa: domin rage warin jiki, za ka iya shan kofin ruwa daya da sassafe kafin ka ci wani abu.

Amfani da ruwan Rose: za ka iya diga ruwan rose water a cikin ruwa kafin ka yi wanka, hakan na rage warin jiki da kuma kara wa jikin kamshi.

Post a Comment

Previous Post Next Post