Ingantaccen Maganin Basir Kowane Iri Ne Hadin Gawasa Za a Rabu Dashi Insha Allahu
Gawasa wani abinci ne mai daɗin ƙamshi ga daɗi wanda kasan wasu da dama sun santa musamman mutanen karkara, ga ƴan birni kuwa ba kowa ne yasan ta ba amma da zarar suma sunyi tambaya za’a gaya musu.
Kamar yadda masan cewa wasu da dama sun san amfanin ta ga lafiyar jiki wasu kuma cinta kawai suke don daɗin da take dashi.
A yau zamu duba da binciken amfanin Gawasa ga lafiyar jikin dan Adam ina fata mai karatu zai karanta maƙalar tamu cikin nutsuwa domin zamu taɓa bangarori kamar.
Yadda za’ayi amfani da ita wajen ƙara karfin maza kuta.
Yadda za’ayi amfani da ita wajen magance cutar hakarkari.
Yadda za’ayi amfani da ita wajen magance cutar basir
Yadda za’ayi amfani da ita wajen ƙara karfin maza kuta.
Abin Buƙata:
Namijin Goro,
Ɗan Cikin Gawasa.
Yadda Za’ayi Amfani Dashi:
Idan kuna buƙatar Gawasa tayi muku amfani wajen ƙara karfin maza, zaku samu Gawasar ku bayan kun cinye ta baki daya saiku ɗauki ƙwallon nata ku fasashi da abu mai ƙarfi.
Bayan ya fasu akwai wani ɗa a cikinsa mai laushin gaske yanda garɗi irin na Gyaɗa, saiku ciri ɗan kusamu namijin goro ku dinga cin sa dashi.
Insha Allahu zakuyi mamaki sosai da yadda zakuji daɗin wannan haɗi.
Yadda za’ayi amfani da ita wajen magance cutar hakarkari.
Abin Bukata:
Man Shanu,
Ƙwallon Gawasa.
Yadda Za’ayi Amfani Dashi:
Domin magance ciwon hakarkari sauki samu Gawasar taku bayan kun cinye jikin nata sai yazama iya kwallon saiku kona shi ya konu sosai.
Sai ku daka shi sosai a turmi yadaku, ku kawo wata ƙaramar roba ta man shafawa ku zuba a ciki ku kawo man shanu ku haɗa ku juya ya juyu sosai a dinga shafawa a hakarkarin dake ciwon.
Insha Allahu za’a rabu da ciwon hakarkarin da yardar Allah.
Yadda za’ayi amfani da ita wajen magance cutar basir.
Gawasa
Dan uwa idan basir na damun ka sai a nemi Gawasar ko dai a cita haka ko kuma a kan kari jikin nata a busar dashi a daka a dinga shansa a kunu.
Ko kuma kasamu sassaƙen Gawasar ka dinga sha shima Insha Allahu za’a rabu da basir.
Masha Allah Bissallam, Allah yasa wannan bayani ya amfanar daku Amin.
Post a Comment