Dalilan Dayasa Wasu Mazan Keson Mata Masu Manyan duwawu ( hips )

Dalilan Dayasa Wasu Mazan Keson Mata Masu Manyan duwawu ( hips )



 


Kutiri, mazaunai ko duwawu kamar yadda akafi saninsa da suna, wani bangare na halittan mutum da aka yi mass saboda zama. A kuma tsakiyar marabar duwawun ne Allah Yayi dubura domin tace najasar da mutum ya samar ta hanyar cin abinci da muke kira bahaya a sirrance ko kashi a bayyanai.


Duk wani Dan Adam da Allah Ya halitta yana da mazaune harma da wasu halittun gida dana daji ko dai domin zama kamar ko kuma domin boye ramin duburar kamar yadda nayi bayani a baya.

Wasu daga cikin alamomin da ake bambamta mace dana miji duwawu yana daga ciki, duk kuwa da ana samun wasu mazan da sukeda manyan duwaiwuka kamar na mata wanda hakan a cewar masana akwai matsala.


Duwaiwukan mace yana daga cikin alamun kosawarta ta isa haihuwa bayan tabbatar da bagalaganta. Don haka yana da wuya mace a ganta da manyan duwaiwuka a lokacinda take da karancin shekaru.


Duwaiwuka suna gaba-gaba cikin manyan halittun mace dage fito da kyau dirin halittanta da kyaun siffanta duk kuwa ba kowace mace mace mai duwawu bace ake samunta da kyaun fuska, sai dai akasarin mata masu duwawu sunada kyaun diri kamar yadda bincike ya tabbatar.


Su dai mazaunan matan Allah Yayisu dabam-dabam. Akwai masu tudun da ake musu lakabi da "Kilimanjaro," da akwai "Duwawun kura" da dai sauransu. Sai dai babu siffar mace mai duwawu dayafi dauke hankalin maza harma a da mata irin mace mai duwawun da siffar da ake cewa 'Coca-cola shape". Siffa ne da maza suke sha'awar ganin mace dasu. Duk kuwa da siffar mazaunar mace yana da halaka da asalinta idan danginta sunada shi duk kuwa da ci gaban zamani yazo a yanzu haka ana dashen duwaiwuka da kuma sayarda na roba.


Mazan da aka zanta dasu akan dalilansu na son mata masu duwawu sun nunawa cewa ita mace mai duwawu tana kwantar da zuciyar mai kallonta. "A gaskiya ina matukar sha'awar naga mace da duwawu musamman ina zaune a gida ana juyaminisu ina samun natsuwa da kwanciyar hankali, shi yasa dukkannin matana uku babu laifi sunada mazaunai". Cewar Ibrahim Aliyu.


" Aini banama sanin mace na kusa dani muddin banga duwawunta na motsawa ba, a gaskiya babu ma yadda za a hada siffar mace mai duwawu da marashi ko a yanayin kwalliyarsu". Cewar Habibu Tahir.


"Ita mace mai baiwar duwawu Alhaji tayi, domin ko rungumarta kayi ta baya ka wadata, don haka bani da wani buri a yanzu irin na samu mata mai irin wannan siffar na aura don ko kofa bazan leka sai nayi bakwai, (dariya)". Musa Hamidu.


Shi kuma Aminu Alkali yace" Mata masu manyan kuturi kamar yadda kace basuma cika tsufa ba, ko da sun haura shekaru tsufansu baya nunawa. Haka kuma duk yadda suka maka kwalliya sai kaga dabam Wallahi. Nidai a gaskiya zuciyata tana cike da son naga mace da baya".


Har ila yau bincike ya kara tabbatar da cewa duk wata kabila ta duniya da suke da al'adar sawa a yiwa sarakunansu rawa, tsarin gudanar da rawar bai wuce ko dai a kada kirji yadda nonuwa zasu rika rawa ko girgiza ko kuma a kada kugu yadda za a juya duwaiwu. Don haka mata masu manyan duwawu sune ake zabe domin zuwa gaban manyan bani ko nishadar da sarakuna a lokutan taruruka ko zaman nishadi.


Ko da yake shi shan koko daukan rai ne, ba dukkannin maza bane suke son mace da duwawu ba, ana samun da wasu mazan babu siffar macen da suke so da sha'awa irin matan nan masu duwawun rakumi, su a wajensu irin wannan matan suke kwanta musu a zuciya kuma sune abunda zuciyarsu ke kawar ganin matsayin matarsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post