Amfanin Magarya Guda Goma Sha Shida Ga Lafiyar Dan Adam
1. Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature.
2. Miki ko kuraje a kan fatar jiki ko wani sashe na gangar jiki: sai a tafasa garin magarya da ruwan khal sai a wanke mikin ko kurjin da kyau da wadannan ruwan sai a marmasa garin magarya kadan a kan mikin bayan ya wuni a haka sai a saka ruwan dumi a wanke maganin sai a sake maimaitawa. In sha Allahu za a samu sauki.
3. Cututtukan ciki -kama daga kumburin cikin da baya da alaka da cin wani abinci ko abin sha, zafin ciki da yawan tsuwar hanjin ciki akai akai sanadiyyar wasu kwayoyin cuta na bacteria sai a nemi ganyen magarya mai kyau a sabe sai a saka ruwan dumi a tace da kyau a sha kashi daya daga cikin kashi uku na karamin kofi. Haka za a maimaita da yamma.
4. Saurin warke ciwo. Anan, idan ana fama da jinya ko a lokacin da ake farfadowa daga wata rashin lafiya wacce ta kontar da kai a sanda kake jin jikinka ba karfi ko kaji baka son cin komai saboda baka jin dandanonsa. To sai ka nemi garin diyan magarya kamar cokali uku kanani sai ka sanya zuma ka kwaba ka sha. Za ka rinka yin haka a kalla sau biyu ga wuni a cikin kankanin lokaci za ka ji karfi da kuma dadin jikinka. Ko kuma mafi sauki ka nemi diyan magarya ka dunga sha. A hakika suna kumshe da dimbin sinadirran bitamin C wanda yake hura garkuwar jiki fiye da wanda ke a cikin bitamin C din da muke siya a kemis din saida magani.
Karanta Wannan: Hanyoyi Biyar Na Ɗaukar Ciki Ba Tare Da Saduwa Ba
5. Ganyen magarya na da karfin yakar cututtukan fata, kama daga makero da kazzuwa da kurajen fata na ba gaira ko ake kallon kamar na iska ne. To za a kwaba garin sai a shafa da man kade ba baseline ba a inda matsalar ta shafa. Idan maganin ya dauki lokaci sai a wanke da ruwan dumi. Ko mafi sauki a nemi sabulun magarya mai kyau bana yaudara ba tunga amfani da shi.
6. Yana tsaftace jini – sabili da yana dauke da sinadiran saponin, alkanoide da kuma triterpenoid da ke gyara jinin jikin dan’adam.
-Yawan gajiya da ciwon jiki ko yaushe, sai a rinka sabe ganyen a danyensa a sanya a cikin ruwan dumi a tace da kyau a sha.
7. Ganyen magarya na tsaida gudawar da ta tsananta sanadiyar lalacewar ciki, ko dai matsalar daga abinci ne ko cin karo da wata kwayar cuta ta bacteria, a nan banda gudawa a sanadin ciwon tsida. Za a sha cokali daya karami na 5ml ga koko ko ruwan zafi.
6. Karya sihirin maye: A gargajiyance wannan magani ne da aka sha jarrabawa kuma ake samun dace. Idan maye ya kama mutum to sai a nemo busashen ganyen magarya a hada da wani turaren wuta da ba zamu fadi sunansa a nan ba saboda wasu dalillai to sai a zo a tirarawa wanda maye ya kama a nan take mayen zai sake shi.
7. Ana karya sihiri ta amfani da ganyen magarya sai dai ilimin yanda ake amfani da ganyen magarya a karya sihiri ya sha banban.
8. Mata masu karamcin sha’awar saduwa sai su dunga shan ganyen da madara 5ml a kullum.
9. Ganyen magarya na maganin damuwa da hauhawan jini saboda kumshe yake da ninki ba ninki na sinadiran potassium.
10. Ganyen magarya na maganin gyambon ciki.
11. Ganyen magarya na kare cututtukan hanta dana koda.
12. Yana daidaita nauyin jikin mutum.
13. Garin diyan magarya na karawa garkuwar jiki kuzari.
14. Ana gauraya garin diyan magarya dana dabino rabin cokali sai a sanya ruwa a tafasa a sanya zuma kadan a sha dan magance yawan mantuwa da ta yi tsanani musamman a sanda za a kwanta.
15. Matan da suka haifu za su iya hada ganyen magarya da garin diyan bagaruwa su tafasa sai su rinka tsarki da ruwan. Amma kada a cusa garinsa, wannan zai taimaka su samu dai-daituwa da kuma sake hadewa.
16. Ana tsutsar diyan magarya dan maganin kurajen da ke tsiro ga harshe ko a cikin baki.
Post a Comment