Matsalolin Zafin Tafin Hannu Ko Kafa Wato (Numbness) A Takaice.

 Matsalolin Zafin Tafin Hannu Ko Kafa Wato (Numbness) A Takaice.



Barkanmu da yamma da fatan kowa ya wuni lfy Allah ya kawo Mana zama lfy a kasarmu Amen.


Matsalar zafin tafin hannu ko kafa, kamar yanda nai bayani lokacin Daya gabata ba kasafai wannan yanayin ke zama alama ta matsala ba, akwai sauran dalilai wadanda zasu iya haifar Mana da wannan alamomin.


Bayan wannan na zakulo wasu dalilai Yan kadan wadanda zasu kawo Mana zafin tafin kafa ko hannaye ko Duka lokaci Daya.


1- VITAMIN DEFICIENCY:- Karancin sanadaran gina jiki, idan jiki baya samun wadatattun sanadaran Gina jiki wadanda jiki kanshi ke samarwa da Kuma wadanda muke Anfani dasu acikin kayan abinci Wanda muke Anfani dasu Yana Daya daga cikin alamomin dake haifar da wannan kamar sanadarin Vitamin D, Ascorbic Acid, Vitamin B2, Vitamin B12 da Sauran su.


2- DIABETES:- Matsala ko alamomin ciwon sugar Yana daga cikin abunda ke haifar da wannan ko Yana daga cikin alamomin farko farko na matsalar hauhawan Sugar jik.


3- KIDNEY FAILURE:- Matsalolin Koda, Idan MUTUM yacika samun wannan matsalar ya bibiyi aikin Kodar sa ta hanyar Awo da Kuma fahimtar sauran alamomin Koda a jiki, kada tinanin ya tsaya ga matsalar zafin tafin kafa ko hannu kadai. Kamar yanda mukai ta bayanin matsalolin Koda da alamomin ta a gidannan.


4- CERTAIN MEDICATIONS:-Anfani da magunguna na bature suna gaba gaba wajen haifar da wannan yanayin na zafin tafin kafa ko hannuwa.


5- Auto Immune Disease


6- Toxins


7- INFECTION


8- ALCOHOLISM


ABUN LURA.........Idan ana samun wannan yanayin ta hanyar bincike da tatsar sauran bayanai ke tabbatar da abunda ke haifar da wannan lalurar. Anfani da magani Kai tsaye bazai magance matsalar ba.


Kabir Danwuri Yusuf

Post a Comment

Previous Post Next Post