Hadin Maganin Ganye Da Kuma Yayan Tafasa Domin Dawo Da Kinarki Ya Macce
Tafasa wacce muka sani a kasar Hausa wata karamar bishiya ce dake da ganye launin kore da fure da kananin 'ya'ya a jikinta.
Ita dai wannan bishiyar ana samunta a wurare da dama a kasashen Africa ciki harda Nigeria musamman a jihohin arewa.
A kasar India masu maganin Ayurvedic Herbal Medicines sun dauki lokaci mai tsawo suna amfani da tafasa dan yin maganin wasu ke6a66un rashin lafiyoyi kamar haka :
Maganin makafta ko matsalar data shafi ta gani.A baya ga wannan matsala ta barazanar makafta,tafasa na kara lafiyar ido kama daga manya,har zuwa tsofaffi.
A dan haka sai a zan ka yin miyan tafasa ana ci ga abinci.
Wani bincike da wasu masana tsirran itatuwa suka yi sun tabbatar da cewa Tafasa na maganin wasu cutukan da ke shafuwar babbar hanzanya (colon) da kuma taurin bahaya (constipation).
Tafasa tana maganin zafin ciki (internal heat) da kuma wanke dattin ciki da ya cushe.
Tafasa tana rage kiba dan haka wannan wata damace ga masu tumbi wadanda ke bukatar rage nauyi.sai a nemi ganyen tafasa a dake a tareda gero ayi gumba a dama ayi kunu a fake sha.
Ana amfani da sayyun tafasa idan suka bushe sai a dake su koma gari dan maganin cizon maciji.
Ana amfani da garin ganyen tafasa dan warkarda gyambon ciki waton ulcers.
Tafasa na maganin tsutsotsin ciki(intestinal worms)
tafasa na maganin cutukan fata kamar su kazuwa da makero da kuraje masu kaikayi ga jiki.
Tafasa na saukarda yawan zafin jiki da hauhawar jini.
Tafasa na daukeda sinadiri mai suna chrysophanic acid da sinadirin anthrone masu kashe kwayar cuta ta fungi.
Ganyen Tafasa na inganta lafiyar hanta.(improves liver function)
Ana amfani da ganyen tafasa ga yara kanani masu fitarda hakora (childhood teething)
ganyen tafasa na maganin zazza6i da ciwon ga6o6in jiki.sai anemo ganyen a tafasa ayi suraci da ruwan ko ayi wanka dasu da sanyin safiya ko yamma.
Ganyen tafasa na flushin din wasu sinadirran dake gur6ata ciki (toxins)
Diyan tafasa na maganin cutukan sanyi kaar na tari da mura musamman ga wadanda basa jimirin sauyin yanayi kamar a lokacin sanyi.
Wanda yaci wani abu ko ya sha wani abu dake da alaqa da poison zai iya amfani garin diyan tafasa inshaAllahu take zai amaiye wannan gubar a cikin lokaci kuma ba zata illata shi ba da amincewar Allah.
Ganyen tafasa na maganin malaria.
Ganyen tafasa na warkarda cutukan jini(blood disoders)
ganyen tafasa na maganin cutukan ciki.
Ana amfani da garin diyan tafasa a markade da mai sai a shafawa rauni ko wata jimuwa ko kuma kunar wuta.
Mai fama da basir mai haifarda zubar jini (bloody diarrhoea) sai ya tafasa ganyen tafasa ya marmasa gishiri a ruwan ya rinka tsuguno a ciki na mintuna goma ko fiye a duk sanda yaje bahaya.
Mai fama da tari sai ya ya markade ganyen a ruwan zafi ya zanka sha.
Nauyi ko ciwon mara a lokacin al'ada sai ayi amfani da tafasa.
GARGADI
mai fama da gudawa ba zai sha tafasa ba.
Mace mai ciki ta kiyayi yanda ake amfani da tafasa.
Mai ciwon hanta shi ma ya kiyaye.
Post a Comment