Bambancin Ruwan Ni'ima Da Kuma Ruwan Ciwon Sanyi

 Bambancin Ruwan Ni'ima Da Kuma Ruwan Ciwon Sanyi 



𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓


Daga Fadakarwa da Tunatarwa.

Mlm yazan gane na banbance ruwan dake zuba a gaban mace. Allah ya biyaka taimakon da kake mana•

𝐀𝐌𝐒𝐀:

_Toh ,kamar yanda kowa yasani gaban mace baya rabuwa da jika ko na ni'ima ko kuma na cuta ya danganta da irin ruwan_


_idan akace farin ruwa ana nufin fari kal me kamar ruwan famfo shine yake zama na ni'ima kuma yanada yauki sannan yanada dandano wani kamar gishiri ya danganta da irin abunda mace kesha._

_saidai mata da yawa farkon saduwa akwai wani farin ruwa me kamar nono dan kadan yana fitowa wannan wani ruwane wanda ba kowacce mace ke samuba domin da yawa mace daga ta fara haifuwa shikenan kuma wannan ruwane na musamman ga wata mace_ 


Karanta Wannan: Dalilin Da Ke Sa Macce Ko Namiji Karancin Sha'awa Da Yadda Za a Magance 

_wani ruwan kuma yauki zakaga yanayi kuma haka kawai mace ko zance tayi da namiji zataganshi kuma me irin wannan ruwan bata taba bushewar gaba kuma daban take acikin mata_

_shikuma ruwa na cuta haka kawai yake zuwa agaban mace kuma bayan farine me kamar majina zakaganshi guda guda wani kuma kamar zare zare kuma ruwan yana iya canja kala daban daban wani yakoma Green wani brown kuma sauda dama warinsa yana zama kamar na danye kifi akwai kuma me warin danyen kwai_

_wani ruwan kuma kamar mace me ciki tana yawan ganinsa musamman bayan gama saduwa ko kuma bayan ta gama fitsari wannan shikuma dattine na mahaifa shima ba matsala bane_

_dalilai da yawa suna saka mata kamuwa da ciwon sanyi saboda idan namiji yanada dashi zai iya sakawa mace ga kuma shiga kowanne toilet ko wajen tsugo a toilet sannan kuma koda mata hudune agida aka samu daya me wannan cutar tana iya sakawa sauran shiyasa mata masu hikima basa rabuwa da riga kafin cutar wato kamar sabulai da ruwan magarya da amfanida gishiri da sauransu.

Allah ta'ala yasa mudace

Post a Comment

Previous Post Next Post