Alamomin da mutum zai gane akwai Aljani a jikinsa ko kuma an yi masa sihiri.

 Alamomin da mutum zai gane akwai Aljani a jikinsa ko kuma an yi masa sihiri.



1. Rashin son karatun Alƙur'ani ko sauraren shi. 

2. Rashin son yin ibada ko a yita cikin ɓacin rai da kasala. 

3. Yawan ciwon kai mai tsanani ko tsagin kai ko kuma jiri. 

4. Yawan ciwon mara ko baya ko kwankwaso ko kuma ciki ko ƙirji. O

5. Yawan jin tafiyar wani abu a jiki kamar kiyashi ko tsutsa ko kwarkwata tana yawo a kai. 

6. Yawan mafarke mafarke na ban tsoro ko firgirta da surutai a cikin bacci ko kuma kiji wani abu mai nauyi ya danne ki ko ya shaƙe miki wuya.  


Karanta Wannan: 



7. Yawan jin tsoro ko faɗuwar gaba ko wani abu ya ringa yimiki gizo ko kuma kiji kamar ana kiran sunan ki.

8. Yawan jin sanyi ko zafi ko riƙewar ƙafa ko wani sashe na jiki. 

9. Rashin iya bacci da daddare ko yawan jin motsin wani abu ko surutai ko kuma takun tafiya. 

10. Rashin son yin kitso ko kuma a taɓa miki kai. 

11. Yawan ɓacin rai ko jin haushin mutane ba tare da wani dalili ba. 

12. Rashin son shiga cikin mutane ko yawan zargin su ko kuma yawa rigima da su. 

13. Yawan kuka ko dariya ba tare da wani dalili ba. 

14. Yawan jin kamar ana yimiki raɗa a kunne ko a ringa raya miki a zuciya akan ki aikata wani lefin kamar kisan kai ko zina ko kuma sata.

15. Rashin son yin Aure ko korar samari ko kasa tsayar da guda ɗaya ƙwaƙƙwara. 

16. Ɗaukewar Sha'awa ko rashin jin daɗin saduwa da miji ko kuma tsanar shi da wulaƙan tashi ba tare da wani dalili ba. 

17. Yawan kallon mudubi ko Sha'awar kallon tsiraici. 

18. Yawan son kaɗe-kaɗe da raye-raye. 

19. Yawan son dare ko cikin duhun ko yin shuru kamar bakya gurin. 

20. Rikicewar Jinin Al'da ko na Nifasi. 

21. Rashin Haihuwa ko yawan ɓari ko Haihuwar ɗan babu rai ko kuma wasu matsaloli su biyo bayan Haihuwa kamar jijjiga. 

22. Aikata wani abu ba a cikin hankalin ki ba, sai daga baya ki ringa nadama ko mamakin yadda akayi kika aikata.

23 Yankewar jiki a faɗi ƙasa ba a cikin hayyaci ba

Idan agamu da wasu daga cikin wadannan sai a hanzarta Neman mallamai ko kuma wanda ya iya ya karanta ayatul kursiyu a kowane lokaci.

Post a Comment

Previous Post Next Post