Masu Fama Da Yawan Sha'awa Wannan Rubutun Naku Ne Ku Karanta Maza Da Mata.
Samari da yan mata zawarawa hadda matan Aure
Ya Allah kabawa wanda ya samu halin karanta
wannan rubutu ikon yin sharing zuwa ga sauran groups.
Samari da yan' mata suna yawan turawa malamai tambayoyi iri daban daban akan yadda suke fama da tsananin sha'awa.
Wasu daga ciki sukan ce suna istimna'i wato wasa da al'aura wai don su gujewa aikata zina, bayan zinar suke aikatawa.
Istimna'i (wasa da al’aura) ya haramtu ta kowace irin siga kuma yinsa zai jawo azaba da ukuba ranar alkiyama matukar dai mai aikatawa bai tuba ba ya daina.
Karanta Wannan: Amfanin Dankalin Hausa A Jikin Dan Adam
Fitar da maniyyi ta kowace irin siga haramun ne saidai ta hanyar aure kawai.
Akwai Bala'o'i masu tarin yawa dangane ta masu wasa da al'aura.
Idan ka" kasance ko kin kasan ce kina fama da matsananciyar sha'awa kuma babu halin yin aure to akwai hanyoyi masu tarin yawa da zaku bi don gujewa fadawa tarkon shaidan.
Ga wasu daga cikin jerin su.
• Ku guji zama a daki ku kadai, ba tare da mutun yana wani aikin dazai ja hankalin sa ba.
• Ku guji yawan sanya sha'awar jima'i acikin ran ku.
• Kuyi iya qoqarin daza kuy wajen kawar da kai daga shafukan da suke yada hotuna masu nuna tsiraici.
• Yawan yin azumin nafila yana mutuqar taimakawa wajen nesanta mutun daga wannan dabi'a.
• Kadena yiwa kowace irin mace kallon sha'awa, haka kema kidena yiwa kowane irin namiji kallon sha'awa.
Mutun zai iya rayuwa cikin qoshin lafiya batare da yana fitar da maniyyi ba har zuwa sanda zaiyi aure, muddin dai mutun yana tunawa da azabobi da Allah ya tanada ga wadan da suka kasa riqe sha'awar su.
Sha'awa irin ta samari da yan mata daga shaidan take, domin tana daya daga cikin manyan tarkunan sa da yake halakar da mutane dasu.
Amma dukkani wanda ya ji tsaoran tsayuwa da ubangijinsa ya hana zuciyarsa abin da take so daga sha’awa da istimna’i lallai aljanna ita ce makomarsa matsuguninsa da izinin Allah madaukaki
Rubutawa batayi mana wahala ba muna fatan sharing zuwa groups bazai yimuku wahala ba👏
Mun-gode🤝
Post a Comment