BASMA KO NASMA ???
By: Mubarak A. Kamba
Zamani Writers Association
(We’re Are Here To Educate, Motivate and Entertain Our Readers.)
Sadaukarwa Ne Ga Dukan Members Na Haɗakar Marubutan Jahar Kebbi (HAMJAK)
Page: 01
Makarantar Tausayi Islam Madarasatul Al’umma, babbar makaranta ce, wacce manyan mallamai ke koyarwa a cikinta. A kowacce shekara su kan yaye dalibanta da suka haddace littafi mai girma wato alqur’ani, tsarkakken littafi. Bikin wannan shekarar ya bambanta da na kowacce shekara, domin a wannan shekarar za su yaye dalibai Hamsin (50) ne, sabanin kowacce shekara Talatin (30) su ke yayewa. A don haka sai suka yi tunanin gudanar da bikin a cikin birnin Sokoto. A Shehu Usman Dan Fodiyo Library ne zasu gudanar da bikin nasu. A ranar da za ayi wannan bikin, duk mallaman da ke fadin wannan kasar ta Nigeria sun halarci taron sai dai wasu yan tsirari da ba su samu damar zuwa ba. Ba Mallaman Kasar Nigeria kadai ba, har ma da wasu manyan Mallamai a duk fadin duniya. Tun daga labarawan Madina, larabawan Makkah da kuma na Kasar Qatar, kai a ko ina ma a fadin duniya.
Wajen gudanar da bikin ya cika sosai da tarin al’ummar Manzon Allah (S. A. W). kowane sashen idan ka duba zaka ga gungun yayan Bil’Adam a wajen. An kawata wajen sosai da abubuwan kyalkyali, da manyan-manyan kujeri na alfarma. Wani wurin kuwa idan ka duba sai kaga taron yan kasuwa masu siyar da littafai, kayan mata irin su turamen zannuwa, sarkuna da agogonni daban-daban. Wasu kuwa yadukkan maza da huluna suke siyarwa. Yayin da kowa keta zumudin ganin an fara wannan bikin can aka ga wani balarabe cikin wata farar jallabiya sanye da jan Arab, da bakin makawuya akansa. Ya hadu sosai tun daga kasa har zuwa sama ya ratso taron al’umma ya fito yana taka manbari har ya isa. Bayan mai gabatarwa ya bada umarni da ya zo ya bude musu taro da addu’a. ‘’zamu saurari addu’a daga bakin alaramma Sudais Ibn Sooraj’’. Mallam Bashir Abdulkarim ya fada. Kafin nan taron al’umma suka ɗauki kabbara tare da ambaton Sallallahu Aalihi Wassalam. Ana cikin kabbara balaraben nan ya fara jan ƙira’a cikin muryarsa mai zaƙin gaske. Suratul fatiha ce ya karanta, amma kasancewarsa mai zaƙin murya da kuma bin dokokin karatu, idan kana saurarensa sai kaji kamar kada ka daina saurara.
Bayan ya gama karantawa ɗaya daga cikin mallaman makarantar ya fito ya fassara tare da rokon ubangiji Allah yasa su gama taron lafiya. Daga nan aka soma musabuƙar da aka zo yi.
Ɗalibin farko ya zo ya karanta Suratul Fatiha, na biyu kuwa ya zo ya karanta Suratul Falaq. Haka dai aka cigaba da karatu har aka zo kan ɗaliba ta ƙarshe. Ita ce Basma Ahmad. Ta kasance mai matuƙar basira da zaƙin murya. A cikin al'qur'ani kuma babu wata sura ko ma aya wacce ta rage mata bata haddaceta ba. Wannan ƙwarewarta ta ne yasa wasu ɗaliban suke mata hassada, yayin da wasu ke matuƙar ƙaunarta, duk da kuwa wasu sun san irin lalurar da Allah ya ɗora mata. Takarwata mambari a hankali sauran jama'a da Mallaman da suka santa da ɗaliban dake ƙaunarta suka ɗau kabbara tun kafin ta fara karatun. Sauran Larabawan da suka zo daga wani wurin suka bada dukan hankalinsu domin yadda tasha kabbara suna kyautata zaton ba a kan banza ba ne. Lokacin da Basma ta karɓi amsa sauti ta faro ƙira'a zaka rantse da Allah ƴar larabawa ce. Daga larabawan waɗanda suka shirya taron har waɗanda suka zo kallo suka rufeta da kabbara har sai da ta kasa cigaba da karatun. A dalilin haka ne yasa wani ɗalibi mai Suna Najib Nura yayi na ɗaya ita kuma ta zo a ta biyu. Wasu na ganin hakan ya zama da yaudara wasu kuma suka ɗauki hakan a matsayin adalci. Bayan da aka gama aka zo basu kyauta. Basma tafi kowa samun kyauta daga hannun larabawa da kuma sauran manyan Mallaman da suka zo taron. Kafin bata kyautar mai gabatarwa ya tambayeta, "Basma matsayinki na mahaddaciya ƙur'ani littafi mai girma da daraja a yanzu mene ne burinki?" Kafin ta amsa wannan tambayar ba ƙaramin rass ta ji a zuciyarta ba. Sai da ta yi ajiyar zuciya sai kuma hawayen da take yi, sannan cikin juriya ta samu damar fara yin magana. "Ba don irin lalurar dake tare dani ba, da nace maka a halin yanzu bani da burin da ya wuce na kasance uwar wasu kamar yadda wasu suka zamo iyayena." Daga nan bata ƙara furta ko uffan ba.
Waɗanda suka fahimceta ƴan tsagin hassada suka bushe da dariya, yayin da masu ƙaunarta suka ji wani iri a ransu. A haka ta sauko daga kan mambari jiki ba ƙwari ko kaɗan bata ji daɗin tambayar ba, kawai dai ta amsa ne ba yadda ta iya. Haka aka yiwa kowa tambaya, kafin a baka kyauta sai an tambayeka burinka a nan gaba. Tun a wurin wasu suka samu cikar burinsu yayin da wasu kuwa aka yi musu fatan nasara. Daga haka dai har aka gama taron aka watse.
_____________________________________________
Ranta a mugun ɓace ta wuce ɗakinta, daidai lokacin da yayyenta da ƙanninta tare da mahaifiyarsu ke zaune suna fira. Nasma kenan wacce kowa yafi so a cikin gidansu. Su sha ɗaya ne mahaifiyarsu ta haifa, ita ce ta uku a cikin mata, sauran kuwa dukan su maza ne. Ganin yanayinta na ba daɗi nwe yasa kowa dakatawa daga surutun da yake yi, firar da ake yi ta katse. Mahaifiyarta Rukayya ta tsorata sosai. Bata tsaya wata-wata ba, tabi bayanta suka shiga ɗakin tare. Shigarsu ɗakin kenan ta ce,
"Nasma yau ma kin ƙara shiga sha'anin Bil'adam ko?" Tana ƙare mata kallo. Ba tare da Nasma ta furta ko uffan ba ta fashe da wani matsanancin kuka tana ƙara dafe bangon ɗakin nata, tana jin wani irin haushi wanda ya ƙara gigita dukan ƴan uwan nata da suka biyo bayanta don jin abinda ke faruwa.
Post a Comment