Amfani Goma Da Gyada Take yi A Jikin Dan Adam

Amfani Goma Da Gyada Take yi A Jikin Dan Adam 



an uwa assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan Allah ya amshi ibadunmu, yasa muna daga cikin Wanda za a yantasu acikin Wannan wata Mai tarin Albarka 

Abin mamaki 

Mafi yawa daga cikin mutane ba su da masaniya kan amfanin da gyada ke yi a jikin Dan Adam 

Gyada da muka raina tana dauke da sinadarai na nutrition kamar haka: 


Karanta Wannan: Dalilin Da Ke Kawo Zubar Maziyyi Ko Digan Fitsari Da Yadda Za A Magance Shi

- Calories

- Protein

- Fat

- Carbohydrate

- Calcium

- Phosphorus

- Iron

- Thiamine (B1)

- Riboflavine(B2)

- Niacin

Ga amfanin gyada a jikin dan Adam kamar haka 

1. Gyada na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawan zuciya.

2. Gyada na dauke da sinadarin ‘vitamin B3’ wanda ke taimakawa wajen hana mutum mantuwa.

3. Yana dauke da sinadarin ‘Phylosterols wanda ke kare mutum daga kamuwa da cutar daji.

4. Yana kuma kare mutum daga kamuwa da cutar siga.

5. Ana samun sinadarin ‘Folate’ wanda ke bunkasa kiwon lafiyan mata masu ciki.

6. Gyada na kara karfi a jiki.

7. Yana bunkasa girman jikin mutum musamman yara domin yana dauke da sinadarin ‘Protein’.

8. Gyada na gyara fatar jikin mutum da hana saurin tsufa saboda akawai sinadarin ‘vitamin E’ a ciki.

9. Gyada na faranta wa mutum rai musamman masu yawan fushi.

A turawa Yan uwa domin suma su amfana 

Post a Comment

Previous Post Next Post