Yadda Ake Karin Kiba Ayi Bulbul A Ƙara Lafiya, Da Kuma Yadda Ake Ragewa Idan Tayi Yawa.

Yadda Ake Karin Kiba Ayi Bulbul A Ƙara Lafiya, Da Kuma Yadda Ake Ragewa Idan Tayi Yawa. 




Kayan Hadawa

1. Lemon grass.

2. Ginger.

3. Tafarnuwa.

4. Cardamom.

5. Cinnamon.

7. Kanumfari.

8. Garin zogale.

9. Green tea.

10. Zuma.

11. Lemon.

12. Apple cider venegar.


PROCEDURE:


Shima kamar yanda na yi bayanin sauran ne mace zata nemi dukkan abubuwan including tafarnuwa, zata iya saka danye ko kuma busashshe su dahu tare. Kuma bayan ya gama dahuwa ba zaki ji kamshin tafarnuwar ya fito ba sam. A wanke lemon a yake a ciki ko a matse ruwan in an sauke. Sannan in a misali karamin kofin tea ne sai ki zuba tea spoon na apple cider venegar, sai ki kwankwade kina shanyewa da zafi zafinsa zuba zai fara keto miki sai ki dan yi tsalle tsalle ko ki shiga aikin gida kina yi cikin sauri ki yi ta zuba. Haka nan ki sha shi da daddare bayan kin gama komai zaki kwanta.


In kin ji yunwa sai dai kisha fruits ko vegetables amma ban da carbohydrate. Idan kuma kina da ulcer ko jikinki baya son lemon kamar ni to ba sai kin sanya ba, sai ki nemi irin green tea mai haďe da lemon. Sannan zogale in baki samu ready made ba to ki sa a samo miki danyen sai ki shanya shi a inuwa kada ki shanya shi a rana nan da nan zai bushe. 



KADA KIYI KIBA


Bana manta lokacin da nake siririya, kullum in na kalli kai na naga ƙashin wuya da yayi mun sarqa, wuyana kuwa siriri kamar tolo tolo ya hango albasa siriri duk sai raina yabi ya ɓaci.


Ni burina in ga na yi kiba na zama bul-bul. Haka aikuwa na dauki aniyar sai na yi kibar nan ko da bala'i. Na shiga loda wa cikina kayan dadi, na shiga cin abinci. Kullum in na kalli kai na a madubi sai in ce a'a bai yi ba ya kamata na ďan kara. Wayen gari na yi naga na fara yin kiba out of control, still kuma ina son abu na. In fact na tsani ka ce mun ya kamata na rage To ban fara sanin illar kiba ba sai da shekaru na yarinyata suka fara wucewa, lokacin ne sai jikina ya fara amsawa. Ciwuka kuma suka ce Salamu Alaikum.


Yawancin doctors zasu ce na gode Allah ina da tsayi bacin haka da akwai matsala. Ina kira ga yan'uwana maza da mata mu sani wallahi cin abubuwan da zasu cutar damu nan gaba ba dadi bane. Mafiya yawa kullum kudin mu na wurin cin su Pizza, Shawarma da Ice cream.


Bama damuwa da yawan sugar da kitsen da muke tarawa jikin mu. Sai mu wayi gari mun yi kibar da rage sa zai mana wahala. Matsalar kiba yanda ka yi ta cikin sauki ba haka kake rage ta cikin sauki ba. In kin yi mugun dage wa ne ki zama yanda kike so maybe cikin 6 month. In kuwa baki dage ba sai ki fi shekara kina aikin abu ďaya. Sannan abune na naci kullum kullum. Kudin da kika kashe kika yi ta cin dadi sai kin kashe ninkin ba ninkin wurin rage kiba. Zaku ga kuna yi kamar baku yi. In ma kina siyan magunguna wadanda FDA ta yi approving amfani dasu irin su Alli da Green Coffee kudi ne mai yawa zaki kashe kafin ki kai adadin da kike so.


Gara ma Garcinia Cambogia bai kai Alli ba. In kin je kin takura kina ta shan abubuwan rage wa kuma daga baya kika ajiye komai to kiban in ta tashi dawowa sai ta ninka ta da. Rage kiba gradual process ne, shine in ta tafi wata ta tafi kenan. Amma in kika takura da yawa to ko ta tafi zata dawo. Ko da kun yi gadon kiba ne a gidanku to kada ki bar jikinki baki motsa sa. Kuma ko ke siririya ce zai iya yiwuwa kina da kitse a jikinki. In har kina son rayuwa mai lafiya ki kiyaye me kike ci kuma ki rinka motsa jinin ki.


Rage kiba cikin sati ďaya da brands suke alkarwarta muku ba zai yiwu ba. Za dai ki iya ganin changes in 1week amma ba ki rage yanda kike so. In ma kin rage a sati daya to akwai matsala ga lafiyarki. Yan mata da suke damun kansu akan kiba, eh da dadi ki zama kina da cika, amma ki bari kiyi aure ki haihu tukuna.


In kin ga still baki yi kiba ba to ke ba mai jikin kiba bace, zaki iya cin abubuwan da zaki dan murmure. Amma wlh rike sirantanki tafi alkhairi Ko kin fi so kiyi komai da kyar? Dinki ma ba ko wanne zaki yi ba don kada ya fito miki da tumbi, ruwa a cokali ya ishi mai hankali wanka.

Post a Comment

Previous Post Next Post