Wata Sabuwar Hanyar Magance Warin Hammata A Lokacin Zafi:

 Wata Sabuwar Hanyar  Magance Warin Hammata A Lokacin Zafi: 



Akwai abubuwa da dama da ke haifar da warin hammata, musamman ma lokacin zafi. Yawan sanya kaya matsatsu ko kuma kaya sau biyu a lokacin zafi, duk sukan haifar da irin warin hammata. Idan mutum kuma ya kasance mai yawan shan giya, ba wuya zai yi warin hammata.

Don haka ne a yau na kawo muku hanyoyi da za a bi domin rabuwa da wannan matsala:

A samu lemun tsami a raba biyu a goga a hammata bayan an yi wanka. Ko kuma a matse ruwan sannan a samu tawul a rika tsomawa, a rinka shafawa a hammata bayan an yi wanka kafin a sanya tufafi. A rika yin haka don magance wannan matsala. 


Karanta Wannan: Cututtukan Da Gwanda Take Magani Fisabilillah 

‘Rose water’ na taimakawa wajen magance warin hammata. Don haka sai a rika diga ruwan a cikin ruwan wanka, sannan a shafa a hammata bayan an yi wanka.

A matse ruwan tumatiri sannan a shafa a hammata na tsawon mintuna 15 sannan a shiga wanka. Amma irin wannan zai dan dauki lokaci kamar mako daya kafin a rabu da warin hammata.

Amfani da alumu “alum “na taimakawa matuka. Sai a tsaoma alum a ruwa, sannan a shafa ruwan a hammata a bari ruwan ya bushe. Yin hakan na magance warin hammata.

Hodar jarirai na magance warin hammata, domin tana dauke da kamshi sai a rinka shafawa a hammata a kullum bayan an fito daga wanka.

Post a Comment

Previous Post Next Post