Matsanancin Ciwon Ƙugu Bayan Haihuwa Ko Ma Bayan Saduwa Ne Matsalarki?
Shin ko me ye dalili?
Daga cikin matsalolin da kan biyo bayan haihuwa akwai matsalar "buɗewar mahaɗar ƙugu" wanda kan faru sakamakon buɗewar(yagewar) tantanai da ke riƙe da ƙasusuwan ƙugu yayin naƙuda wanda a ke cewa "Obstetric Diastasis Pubic Symphysis" a turancin likita.
Ana tabbatar da samun matsalar "buɗewar mahaɗar ƙugu" yayin da aka sami buɗewar ɓangarori biyu na ƙasusuwan ƙugu a mahaɗarsu fiye da ƙima (=/>1cm), haɗi da ɓallewa ko tsinkewar tantanai da ke riƙe da mahaɗar ƙasusuwan.
Duk da cewa wannan matsala na ci wa matan da suka haihu tuwo a ƙwarya, al'ada ta gudana cewa ciwon ƙugu ko kwankwaso wani abu ne da aka saba da shi, ko kuma al'adar masu haihuwa ce daman. Sai dai abin ba haka yake ba, domin akwai buƙatar duba wannan ƙorafi da waɗanda suka haihu kan zo da shi. Domin bincike ya nuna cewa a duk haihuwa 385 akwai mace guda da kan sami wannan matsala. Sai dai kuma saboda ɓoye ƙorafin ciwon da mata kan yi, ana fargabar cewa adadin matan da kan gamu da matsalar suna da tarin yawa fiye da yadda binciken ya nuna.
Karanta Wannan; Abinda Ke Kawo Lalacewar Budurci Ko Ba. A Sadu Ba, Da Yadda Za'a Gyara
Bugu da ƙari, kaso 45 cikin ɗari na masu juna biyu, da kuma kaso 25 cikin ɗari na matan da suka haihu na da ƙorafin ɗaya daga cikin nau'o'in ciwon ƙugu.
Waɗanda ke da haɗarin samun buɗewar mahaɗar ƙugu yayin haihuwa sun haɗa da:
1. Ɗaukan haihuwar tagwaye ko fiye.
2. Juyewar ko kaikaicewar jariri yayin naƙuda.
3. Rashin daidaito tsakanin faɗin kan jariri da faɗin ƙugun uwa.
4. Matan da aka temaka wa da maƙatar ungozoma (obstetrical forceps) yayin haihuwa.
5. Matan da ke da larurar talewar tantanai fiye da ƙima.
6. Matan da suka faɗa hannun ungozomomin da basu ƙware ba, da sauransu.
Alamomin "buɗewar mahaɗar ƙugu" sun haɗa da:
1. Ciwo a matsematsin cinyoyi, saman gaba, cinya, bayan ƙugu/baya,
2. Ciwo a ƙugu yayin da aka matse cinyoyi,
3. Ciwo da wahala yayin mirginawa/juyawa a gado,
4. Ciwo a ƙugu yayin tsaiwa, tafiya ko hawa bene,
5. Bauɗewar sawaye yayin tafiya, jan ƙafa, da dai sauransu.
Likitoci fisiyo na amfani da na'urorin rage raɗaɗin ciwo don magance matsanancin ciwon da masu wannan larura ke fama da shi, koya musu dabaru cikin ayyukan yau da gobe domin kauce wa jin ciwo ko ta'azzararsa, da kuma ɗora su kan keɓantaccen atisayen da zai ƙarfafa tsokokin ƙugu da ƙafafu.
Har ila yau, idan buɗewar mahaɗar ƙugun ta wuce ƙima ko kuma dukkan tantanai da ke riƙe da mahaɗar ƙugun sun raunata, wannan zai kai ga yin tiyata domin ɗinki ko haɗe mahaɗar.
Wannan ciwo ana warkewa sarai, musamman idan aka sami cikakkiyar kulawar likitocin fisiyo da sauran likitoci.
Daga ƙarshe, sau da yawa mata kan ɓoye wannan ciwo da zaton cewa wannan ciwon al'ada ne da kan zo duk bayan haihuwa. Sai dai ɓoye wannan ciwo da kuma barin sa ba tare da an magance shi ba na iya tsawaita ko kuma ya sake dawowa lokacin renon ciki na gaba.
Saboda haka sanar da likitocin da ke kula da ke irin ciwon ƙugu, ƙafafu, ko wahalar tafiya da kike ciki bayan haihuwa domin
Post a Comment