Ma'aurata Su Kiyaye Yiwa Junansu Wadannan Abubuwan A Lokacin Jima'i:
Dabi'u da halayen da muke aiwatarwa da iyalanmu sunada tasiri wajen gamsar da juna a yayi lokacin mai mahimmanci irin na saduwan aure.
Ga wasu halaye da dabi'un da ma'aurata suke yinsu da basu da kyau.
1: Musamman Maza, suna saduwa da matansu suna duba lokaci na agogo. Wanda hakan na nuna ba maida hankali ko damuwa yayi da abunda suke yi ba.
Maza sunada dabi'ar nuna tamkar alfarma suke yiwa matansu wajen saduwa dasu.
Don haka sai namiji ya rika yiwa matarsa abu da gadara da kuma isa tamkar ita kadai ke son Jima'i ban dashi.
Yawan duba lokaci yayin da ake saduwa da iyalinka tamkar ka zaku da ita ko kuma abunda ke gabanka ya fi biya mata bukata mahimmanci. Koda hakan ne sai ka natsu ka maida hankalinka har lokacinda zaku gama abunda kukeyi. Ya kamata magidanta Maza su fahimci cewa ita mace fa babu mai mata wannan abun sai kai, maida hankali wajen yinsa yadda ya dace kuma wajibi ne.
2: Mata sunfi yin wannan mugun halin. Wasu matan da zaran sun samu gamsuwa sun rika damun mazansu da suyi da wuri suyi zuwan kai su rabu da jikinsu.
Akwai matan da ma idan har suka riga mazansu biyan bukata ture mazan suke yi daga jikinsu koda basuyi zuwan kai ba. Wannan zalunci ne.
Dole ne ki hakura ki jimre har sai lokacin da mijinki yayi zuwan kai domin kansa amma baki yi azalzala masa dole sai yayi zuwan kai da wuri ba saboda ke kin riga kinyi.
Koda namiji ya riga matarsa gabatowa to dole ne sai yayi hakurin da itama zata zo amma ba ya kama surutu ko mita ba.
3: Akwai wasu ma'aurata masu yin tari ko atishawa a fuskan guda a lokacinda suke saduwa.
Masana fannin lafiya sun nuna tari ko atishawa a fuskan juna bai dace domin mai dauke da kwayar mura idan itace yana iya shfawa marashi. Hakan yasa suka bada shawara ma'aurata su kauda fuska a lokacinda guda daga cikin biyun nan ya zo musu a lokacin saduwa.
4: Mata da maza duk suna wannan mugun kwatancen musamman mata zaurawa da mazan da suka taba aure.
Babu kyau, bai kuma dace ba namiji yayi kwatancen da tsohuwar matarsa ko kuma wata matarsa tasa yadda take yi ta gamsar da shi ga matarsa. Kamar yadda bai dace ma ita mace ta cewa mijinta ga yadda tsohon mijinta yake mini ya gamsar dani.
Ba sai kun ambaci wanda ya muku ba ko yake muku. Kai tsaye nunawa matar ka yadda kakeso ta maka ko fadawa mijinki inda kike so ya tabamiki. Ambatar wani tamkar cin fuska ne da kuma nunawa wannan gazawarsa. Don haka ma'aurata a guji yin hakan.
5; Mata sunfi yin wannan iya shegen.
Mace tana saduwa da mijinta bata jin dadin abunda ake mata amma zata kama kukan kissa na karya da sunan tana jin dadin Jima'i.
Ya kamata ki fahimci hakkinki ne mijinki ya gamsar dake ya jiyar dake dadi. Idan yana miki wani abunda ke cutar dake ne ba dadi ba fadamasa kamar yadda shima idan kika masa ba daidai ba bazai hakura ba.
Yin kukan karya da nuna gamsuwa da karya wannan baya taimakawa ma'aurata illa ya ci gaba da illata musu zaman aurensu. Don haka ku daina, idan an miki da dadi yi kukan dadi, idan aka miki ba daidai yi magana domin a gyara.
6: Shima wannan kuskuren mata suka fi duk da ana samun wasu mazan masu kuskure su kira sunan wata maimakon wacce suke saduwa da ita.
Mata zaurawa ana samun kuskuren idan dadi ya kwashesu su ambaci sunan tsohon mijinta maimakon wannan dayake sarrafata. Haka maza masu mace fiye da guda suma ana samunsu da wannan kuskuren.
Tabbas hakan ba karamin bakata rai zai yiwa ma'aurata ba ga duk wanda akayi subul da baka wajen ambatar sunansa aka ambaci na waninsa. Ko kuma na kishiyarta. Don haka sai ma'aurata su kiyaye.
7: Maza sun fi yin wannan mummunar halin.
Maza da dama sukan hana matansu su musu wasa da alauransu, haka suma sukan ki yarda su yiwa matansu wasa.
Mafiyawan irin wadannan mazan koda su fake da addini ko kuma suce suna kyamar matan nasu. Wanda duka hujjoji guda biyu babu na kamawa.
8: Wasu mazan kuma da suke wasa ake musu wasan suna sauri wajen kammala wasan da matan nasu tun lokacin hakan bai yi ba.
Wannan yasa sai namiji yayi zuwan kai da wuri matarsa ko motsawa bata soma yi ba.
Kayi wasa da matarka har sai ta kai makuran da zata maka magana da kanta na bukatanka.
9: Mata da maza duk suna wannan. Abun mamaki ne wai aga ma'aurata suna kyamar su sha bakin junansu.
Wasu mazan duk yadda matansu zasu so su sha musu baki lokacin saduwa basa yarda. Musamman Maza masha ya daba so aji warin bakinsu.
Haka nan ma ake samun wasu matan da suke kyantar bakuman mazansu suki amincewa su sumbacesu a yayin saduwa dasu. Wannan kuskure ne. Sumabata yana daya daga jerin manyan ababen da suke karawa ma'aurata kaunar junansu.
10; Wasu matan suna daukansa abun wasa ko dariya. Tusan gaba ga macen datasan kanta ba abu bane da zai kasance a lokacinda ake saduwa dake ki maida abun wasa ko abun dariya.
Akasarin mazaje sun tsani jin gaban mace na tusa a lokacin saduwa da ita. Don haka idan hakan ya kasance dake a lokacinda kike saduwa da mijinki ki bashi hakuri ku sake yanayin da iska bazai shigeki ba wanda ya shigeki kuma zai fita, ko kuma ki nuna masa a hakura da saduwa har sai ya sace idan ya amince da hakan kinga kin masa abunda yakeso idan kuwa a matsai yake kin nuna masa kulawarki da rashin jin dadinki.
Wadannan sune wasu ababen kiyayewa ga ma'aurata a lokacin Jima'i. Da fatan ma'aurata zasu danne sha'awar su ga halas dinsu kadai.
Post a Comment