Cututtukan Da Gwanda Take Magani
IDANKA KARANTA WANNAN KAYI KOKARI KA TURAWA SAURAN YAN UWA DOMIN SU AMFANAI BAKI DAYA.
A sakamakon yanayi da damuna da muke ciki wanda akan samu yawaitar sauraye,wanda sanadiyyar haka jama'a suna kamuwa da ciwon zazzabin cizon sauro da kuma TYPOID.
Insha Allah wannan fa'ida tana magance matsalar TYPOID da maleria cikin kankanin lokaci,kuma koda TYPOID din ya dade a jikin mutum zai fita da yardar Allah.
ALAMOMIN ZAZZABIN TYPOID
Rashin cin abinci.
Ciwon kai.
Zazzaɓi ya kai digiri 104 na Fahrenheit.
Rashin nutsuwa.
Gudawa.
Yadda cutar ke yaduwa
1. Kwayar cutar Salmonella ta typhi za ta kasance a makewayin gidan mai cutar. Idan ba sa wanke hannayensu da kyau daga baya, za su iya gurɓata duk abincin da suka taɓa. Duk wanda ya ci wannan abincin shima yana iya kamuwa da cutar.
2 . Haka kuma, idan mai dauke da cutar ya riƙe abinci ba tare da ya wanke hannayensa yadda ya kamata ba bayan ya gama fitsarin, zai iya yada cutar ga wani wanda ya ci gurbataccen abincin.
3. Mutanen da ke shan gurɓataccen ruwa ko cin abincin da aka wanke a cikin gurɓataccen ruwa na iya kamuwa da zazzaɓin taifod.
ABINDA ZAA NEMA DOMIN MAGANCE WANNAN CUTA
1. Ganyen gwanda
2. Ruwa
YADDA ZA'A HADA:
Da farko zaa samu ganyen gwanda guda daya kacal ruwa litre daya sai a tafasa ganyen gwandar da ruwan bayan ya tafasa a sauke a barshi ya huce,sai a kasa ruwan gida 3 asha kashi 1 safe 1 rana 1 yamma 1 dare,tsawon sati 1 insha Allah za'a dace.
Wallahu a'alamu
Post a Comment