Babbar Matsalar Rashin Cin Abinci A Kananan Yara
Duk masu yara kanana za su san cewa a yara wadanda suka kai munzalin cin abinci sosai wato daga shekaru biyu zuwa biyar, akwai masu son abinci akwai kuma marasa so. Marasa son abincin ba wai don wata rashin lafiya ba, a’a akan samu haka kawai yara su ki cin abinci sai dai neman abubuwan kwadayi. Wadannan abubuwan kwadayi kamar alewa da cakulet da askirim da sauransu, ba za a lissafasu a matsayin abinci ba tunda ba su da sinadaran cikin abinci cikakku da ake samu a abinci. In an samu wani abin amfani bai wuce sukari da madara ba. Wasu yaran kuma idan an zuba abinci sai dai su tsinci abin da ransu yake so, su bar sauran. Wadannan ma suna cikin wadanda ba su son cin abinci, wadanda masana ciyayyar abinci wato nutritionists ke kira ‘picky eaters’. Wasu kuma sai su yi ta dirkar ruwa ko lemo ko madara a tsakanin cin abincin har ciki ya cika ba a ci komai ba.
To da dama irin wannan matsala na ci wa iyaye tuwo a kwarya. Ko ta ya ya ake maganin irin wannan matsala? A da akan samu kakanni da wasu iyayenma suna matse yara suna musu ‘dure’, wato ciyarwar dole, yaro na kuka haka za a matse shi a dura masa abinci. A lokuta da dama wannan hanya ba ta biyan bukata, tunda da dama in sun ci dawo da shi suke ta hanyar amai, idan ma ba su kware ba ke nan, wato abincin ya bi hanyar iska ya jawo musu matsala. Ke nan ‘dure’ ba shi ne mafita ba.
Babbar mafita ita ce ta karanta halayyar yaran ta bangaren abinci, me ne ne suke so, me ne ne ba sa so. Duk da cewa yara da dama sun fi son abubuwan da ba kowa kan iya jure saya ba, kamar kifi, nama, kwai, da sauransu. Kamata ya yi a tabbatar a kullum sun same shi ko makamancinsu kamar wake ko alala, awara, gyada/kunun gyada da ire-irensu. Ana iya tambayar yaran kai tsaye a ji irin abincin da suke so, wanda shi ma kan taimaka.
Kayan ganye kuma irinsu zogale ana iya musu kwadonsa da kuli-kuli da suga wanda zai kara masa dadi da dandano, irinsu latas da lansur da ire-irensu kuma akwai man kwadonsu na musamman wato ‘salad cream’ mai kara wa kayan ganyen dadi. Wasu masanan magunguna kuma sun ce ruwan sinadaran bitaman wato multibite banda kara wa yara marasa cin abinci sinadarai da yake yi, yakan iya sa su cin abinci ta hanyar washe musu ciki. Don haka idan duk wadannan hanyoyi ba su yiwu ba, to yana da kyau a je a tuntubi likitan yara musamman idan nauyi da tsayin yara baya karuwa.
Nau'in abinci 7 da ke kara karfin kwakwalwar yara:
Wani bincike da masana suka gudanar ya bayyana irin nau’in abinci da ya kamata a dunga ba yara kanana, saboda ya tallafa masu wajen kara kaifin kwakwalwa da tunani.
A cewarsu karancin wadannan abinci na hana yara fahimtar abin da ya kamata da wuri musamman a bangaren karatu.
1. Ba yara dafaffen kwai domin ya na dauke da sinadarorin Vitamin A, B12, D, B6 wanda ke taimakawa wajen kara karfin garkuwan jiki yara musamman ‘yan kasa da shekaru 5
2. Ba kananan yara kayan lambu kamar su lemu kankana, ayaba da dai sauransu na taimakawa matuka wajen kara masu kaifin kwakwalwa
3. Yawaita ba yara kifi suna ci.
4. Ciyar da yara naman kaza ko na talotalon da aka cire fatan saboda kiba na taimakawa sosai.
5. Cin alkama da abincin da aka yi da alkama.
6. Ba yara ayan gayyayaki kamar irin su alayyaho, karas, tumatur, da sauran dangin kayan lambu.
7. Madara(musamman wanda aka rage kitsen da ke jikin shi) domin yana dauke da sinadarin ‘Vitamin B’ wanda ke taimakawa wajen bunkasa kwakwalwan yara.
1
Apples.
2
Breakfast Cereal.
3
Eggs.
4
Milk.
5
Oatmeal.
6
Peanut Butter.
7
Sunflower Seeds.
8
Tuna Fish.
9
Vegetables.
10
Yogurt.
Post a Comment