Amfanin Mangoro Ga Lafiyar Dan Adam.

Amfanin Mangoro Ga Lafiyar Dan Adam. 



Mangoro itace ƴaƴan itacen dutse da ake ci da bishiyar Mangifera indica ke samarwa wanda aka yi imanin ya samo asali ne a yankin da ke tsakanin arewa maso yammacin Myanmar, Bangladesh, da arewa maso gabashin Indiya

A duk duniya, akwai nau'ikan mango da yawa. Dangane da shuka, 'ya'yan itacen mango sun bambanta da girma, siffar, zaƙi, launin fata, da launin nama wanda zai iya zama rawaya, zinariya, kore, ko orange. Mango shine ce 'ya'yan itace na kasa a Indiya, Pakistan da Philippines, yayin da bishiyar mango ita ce bishiyar ƙasa a Bangladesh .

Darajar abinci mai gina jiki Daya kunsa a kowace g 100 (3.5 oz)

Makamashi 250 kJ (60 kcal)

Carbohydrates 15 g ku

Sugars 13.7

Abincin fiber 1.6g ku

Kiba ( Fat) 0.38g ku

Protein 0.82g ku

Vitamins Yawan%DV †

Vitamin A daidai. beta-carotene lutein zeaxanthin

7%54g ku

6%640g ku

23mg ku


Thiamin ( B1 ) 2%0.028 mg

Riboflavin ( B2 ) 3%0.038 mg

Niacin (B 3 ) 4%0.669 mg

Pantothenic acid ( B5 ) 4%0.197 mg

Vitamin B6 9%0.119 mg

Folate ( B9 ) 11%43g ku

Choline 2%7.6 mg

Vitamin C 44%36.4 MG

Vitamin E 6%0.9 mg

Vitamin K 4%4.2g ku

Ma'adanai Yawan%DV †

Calcium1%11 mg


Copper 6%0.111 MG

Iron 1%0.16 mg

Magnesium 3%10 mg

Manganes 3%0.063 mg

Phosphorus 2%14 mg

Potassium 4%168 mg

Selenium 1%0.6g ku

Sodium 0%1 mg

Zinc 1%0.09 mg

Sauran abubuwa Yawan Ruwa 83.5g ku

Shekaru aru-aru da suka wuce, al'ummar kasar Indiya ke amfani da shi don samun waraka, ko riga kafin wasu cututtuka. Ba banza ba suke masa kirari da sarkin kayan marmari, saboda fa'idarsa a jikin dan-adam. Ba wani abu ya sa suke ma sa wannan kirari ba, illa yawan sanadaran da yake kunshe da su, da suke da matukar muhimmanci ga lafiyarmu.

Misali wani bincike akan mangwaro da aka gudanar ya nuna cewa, Kofi daya na ruwan Mangwaro yana dauke da giram 225 da kuma sanari 105 na 'calories', da kashi 25 bisa dari na Bitamin A da kashi 76 na Biitamin C da kashi 9 na sanadarin 'copper' da kashi 7 bisa dari na sanadarin 'potassium' da kashi 9 bisa dari na sanadarin 'fibre'. Turkashi, kai da jin yawan wadannan sanadarai da mangwaron ke kunshe da su, ba sai an fada ba, lalle yana kunshe da abubuwan da za su taimakawa Lafiyarmu.

Saboda yawan wadannan sanadaran da Mangwaron ke da su, shan guda daya a wuni na iya bada kariya ko riga kafin kamuwa daga cututtuka irin su basir, matsalolin da kan shafi zuciya, da samar da kyakkyawar fata da sauran su.

Saboda wannan dalili ne muke bada shawara ga al'umma yawan yin amfani da Mangwaro ba wai kawai shan sa a matsayin kayan marmari ba, a'a har ma a matsayin magani.

Don haka ga wasu daga cikin irin magungunan da ake samu daga mangwaro, saboda amfanin masu karatu.

1. Kara Karfin Ido.

Mangwaro na kunshe da sanadarin Bitamin A mai yawa, kuma a iya cewa mutane da yawa sun san amfanin sanadarin game da yadda yake taimakawa wajen samar da karfin ido. Wani Binciken da aka gudanar ya nuna cewa, shan kofi daya na ruwan Magwaro yana samarwa da jiki kashi 25 cikin dari na Bitamin A, da ake bukata a kullum.

2. Rage Hadarin Kamuwa Da cutar daji.

Akwai wasu sinadarai da ake kira 'kuercetin' da 'isokuercitrin' da 'astragalin' da 'fisetin' da kuma na 'gallic acid' da turanci, wannan yasa mangwaro taimakawa wajen baiwa jiki kariya daga kamuwa da cutar daji.

3. Maganin Cushewar Ciki.

Shan Mangwaro na taimakawa mutum wajen saurin narkar da abinci wanda hakan ke bayuwa da magance cushewar ciki ga mutum. A wani bincike da wata kungiya mai rajin taimakawa masu fama da cutar daji, a nahiyar turai ta fitar ta nuna yadda mangwaro ke dauke da sanadaran dake magance cushewar ciki.

4. Rage Hadarin Kamuwa Da Cutar Mafitsara.

Kamar yadda mangwaron ke rage hadarin kamuwa da cutar daji, hakanan kuma yana irin wannan aiki akan cutar mafitsara. Su dai wadancan sanadaran da aka ambata a sama dake kare jikin dan adam daga kamuwa daga cutar daji, haka ne kuma suke taimakawa wajen ba shi kariya daga cutar mafitsara musamman ga rukunin mutanen da suka fara manyanta.

5. Kara Sha'awa da Kuzarin Jima'i.

 Bincike ya nuna cewa mangwaro na karawa namiji kuzari yayin jima’i, sannan saboda yawan sanadarin Bitamin E, da yake da shi masana sun ce baya da karin kuzari da yake ga namiji yayin jima'i, haka kuma yana motsa sha’awar ma'auratan a lokacin da aka nimmatu don biyan bukatar aure.

6. Lafiyar Kwakwalwa

Binciken masana na wannan zamani ya nuna cewa Mangwro na karawa kwakwalwa lafiya. Ba don komai ba, sai don dimbin sanadaran Bitamin B6 . Shi wannan sanadari na taimakawa kwakwalwa gudanar da ayyukan ta. Hakanan Wannan sanadari na taimakawa wajen samar da yanayin barci mai kyau kuma ba shakka mun san cewa, akwai kyakkyawar alaka tsakanin barci da kuma kwakwalwarmu.

7. Kara karfin Garkuwar Jiki.

 Mangwaro na kunshe da sanadarin Bitamin C, da Bitamin A , da kuma sanadarin 'carotenoids', wannan ta sa shi taimakawa wajen bunkasa garkuwar jikin dan adam. 

8. Saurin Narkar da Abinci.

Yana taimakawa kwarai da gaske wajen narkar da abinci, ba don komai ba sai don yana kunshe da sanadarin 'enzymes' wanda ke da tasiri matuka da gaske wajen narkar da abincin da muka ci.

9. Karawa Mutum Sha'awar Cin Abinci.

Bincike ya nuna cewa sanadarai irin su ‘esters’ da ‘terpenes’ da 'aldehydes' na taka muhimmiyar rawa wajen kara sha’awar cin abinci ga dan-adam, to shi kuma mangwaro Allah Ya albarkace shi da wadannan sanadarai. Ke nan duk lokacin da ka ji sha'awar cin abincinka ta ragu sai ka nemi mangwaro don magance wannan matsala.

10. Gyaran Fata.

Mangwaro na gyara fatar jikin dan adam ta yi sumul da sheki. Yawan sanadaran da yake kunshe da su, ya sa shi aikata wadannan ayyuka, kuma idan akai amfani da shi, ciki lafiya baka lafiya, in ji ma su iya magana.

11. Rage kiba Sakamakon kasancewar sinadarin ‘pectin da vitamin C’ a cikin mangwaro da kuma bawon mangwaron kansa, yasa mangwaro na hana mutum kiba ta hanyar narkar da kitse a jikin mutum.

Post a Comment

Previous Post Next Post