Amfanin Lalle Guda Goma Sha Uku Ga Mata:
Lalle wata karamar bishiya ce da ke da matukar muhimmanci wajen samar da magunguna baya ga kwalliya da mata kan yi da ganyenta. Ana kiran bishiyar da lalle, hakanan ake kiran ganyen, kuma ko da kuwa an shanya shi ya bushe sannan aka daka ko nika ana kiran garin da lalle.
A wannan rana shafinku mai farin jini na "Lafiyar Iyali" ya kawo mu ku fa'idojin da lalle ke da su ga mata. Da zarar an ambaci lalle farkon abin da zai zo zuciyar mai karatu shi ne, yadda mata ke amfani da shi wajen kwalliya musamman a hannaye da kafofinsu. To baya ga wannan bincike ya gano ya na da tasiri wajen warkar da matsalolin lafiya
Sai dai ya na da matukar muhimmanci mai karatu ya fahimci cewa, a nan mu na nufin lalle na hakika, ba wai na zamani da ake sayarwa a kantuna ba, wadanda mafi yawansu daga kasashen ketare su ke, saboda haka ba mu san asalinsu da sahihancinsu ba. Ta iya yiwa lallen ne ko kuma wani hade-haden kemikal ne.
Ba tare da wani bata lokaci ba, bayan gudanar da zuzzurfan bincike shafin, ya gano amfanin lalle guda goma sha uku wajen inganta lafiyar mata, yadda za su samu kyakkyawar zamantakewar aure a gidajen mazajensu. Da fatan a sha karatu lafiya.
1. Maganin Cututtukan Mata.
Kwararrun likitoci a fannin cutukan da kan shafi al'aurar mata sun tabbatar da cewa, mata sun fi maza saurin kamuwa da cutuka da ake dangantawa da jima'i ko rashin tsaftar bayan gida, kamar ciwon sanyi, wannan kuwa saboda yanayin halittar al'aurarsu ne, kamar yadda masanan su ka bayyana.
Saboda haka 'yar-uwa za ta iya amfani da lalle domin samun waraka ko riga-kafi daga irin wadannan cutuka.
Karanta Wannan: Yadda Ake Rabuwa Da Kurajen Fuska
Domin samun wannan fa'ida ta lalle, sai a samu ganye ko garinsa a zuba cikin ruwa a dafa, sai mace ta shiga ciki bayan ya huce, za ta zauna ciki tsawon mintuna 15, idan Allah ya so za'a ga amfaninsa matukar aka jarraba. Wacce ta kamu da wata cuta ta mata za tai haka tsawon mako biyu.
2. Maganin Matsi Ga Mata.
Albishirinku Amare da iyayen gida, duk matar da ta bude kuma ta ke son ta matse don mai gida ya ji ta kamar sabuwar amarya, sai ta samu lalle ta kwaba shi da ruwan dumi sannan ta cusa shi a gabanta ta jira tsawon sa'o'i biyu sannan ta cire ta wanke da ruwan dumi, in sha Allahu ango ko mai gida zai yi mata bayani.
3. Karin Ni'ima Ga mata.
Hakanan, ga wani labari mai dadin ji ga 'yan uwa mata, amarya, uwar-gida kai har da 'yan mata, don kuwa su ne amaren gobe. Hausawa na cewa, idan kina da kyau ki kara da wanka. Ko da kina da ni'ima a matsayinki na 'ya mace, ya na da kyau ki ci gaba da kare kanbunki. To lalle na da wannan tasirin.
Idan kina da ni'ima kuma ba ki son wannan ni'ima ta gushe, sai ki dimanci yin kunshi da lalle saboda yana dawwamar da dumin mace, abin nufi anan shine, mace za ta kasance mai ni ima a ko da yaushe matukar ta lizimci kunshi da lalle.
4. Kariya Daga Sihiri Da Shafar Aljanu.
Mai karatu zai yadda da ni, idan na ce, yadda mata ke haduwa da shafar aljanu ya ribanya abin da aka sani a shekaru baya. Akwai kyakkyawan zaton yawan amfani da lalle na ainihi da matan waccen lokacin su kai, ya taimaka kwarai da gaske.
An tabbatar da cewa yawaita kunshi da lalle na matukar taimakawa wajen hana shafar aljanu, sannan ya na hana asiri yin tasiri ga jikin dan-adam. Anan ba wani hadi za ki yi ba, a'a abin bukata kawai, ki lizamci yawaita kunshi sau da kafa, za ki ga tasirin lalle, in sha Allahu.
5. Maganin Karyewar Gashi.
Garin lalle na da matukar amfani wajen hana karyewar gashi. Wasu matan na fama da wannan matsala, inda za ka ga ba wahala gashinta ya karye kuma hakan kan hana mace yawan gashi a kanta.
Idan ki na fama da wannan matsala sai ki samu garin lalle kwatankwacin 1/4 na Kofi, ki samu garin habbatussauda babban cokali guda 3, sai ki kwaba da ruwan dumi ki shafe kanki da shi, bayan haka sai ki jira tsawon awanni 3 ko 4 sannan ki wanke da ruwan dumi, da sannu za ki huta da karayar gashi.
6. Gyaran Gashi.
Baya ga maganin karayar gashi hakanan matan da ba sa fama da wannan matsala da mu ka ambata a sama, ba'a bar su a baya ba, domin kuwa ko da gashinki ba ya karyewa, ba shakka za ki so ace kina da gashi mai sheki, tsawo da kuma laushi.
Idan haka ne, sai ki samu zumarki mai kyau marar hadi, da garin lallanki na ainihi sai ki cudanya su, su hadu sosai, sannan ki shafe gaba dayan kanki da shi. Za ki sha mamaki.
7. Gyaran Fata.
Ba shakka Lalle na da matukar tasiri wajen gyaran fata, don haka amarya da uwar gida sai a karanta da kyau sannan kuma a jarraba, kai kuma 'yan mata ba'a bar ku a baya ba. Babban abin farin ciki game da wannan hadi na lalle shi ne, ba shi da illa kamar yadda mayukan shafe-shafen irin na bilichin ke haifarwa.
Shi lalle ya na sanya fata ta yi haske mai kyau sakamakon goge dattin fata da yake yi. Ga mace mai bukatar gyara fuskarta domin ta yi haske da laushi to sai ki samu lallenki mai kyau, sannan ki samu kwai sai ki fasa ki cire, kwaiduwar. Da ruwan Kwan za ki kwaba lallen amma ya kasance ruwa ruwa amma ba sosai, sai ki shafe fuskarki da shi. Za ki jira har tsawon mintuna talatin sannan ki wanke. Za ki sha mamaki in sha Allahu.
Ga amarya, uwar gida, ko budurwa masu son fatarsu ta kasance mai haske, sai su sami lallensu mai kyau na ainihi su kwaba da ruwa, sannan sai a shafe duk ilahirin jiki da shi,a jira har sai ya bushe, sai a dirje da man zaitun. Bayan kun jarraba ku dawo ku ba mu labari.
Hakanan, za ki iya amfani da wannan hadin domin gyaran fatar jikinki gaba daya. Ki na bukatar lalle mai kyau, sai sabulun salo, sai kuma zuma marar hadi. Za ki hada su waje guda ki kwaba, sannnan ki lizamci yin wanka da wannan hadi. Ba da jimawa ba za ki ga canji cikin yardar Ubangiji.
8. Maganin Warin Baki.
Warin baki ba karamar illa ke haifarwa ba ga duk mai fama da shi. Saboda ya na hana saakewa cikin jama'a, da zarar ka yi magana warin baki zai sanya mutane kawar da kai, shi kuma mai fama da shi ya ji kunya, saboda haka akwai matsala kwarai ga mai warin baki da kuma jama'ar da yake hulda da su.
Domin magance wannan matsala, sai ka samu lallenka/ki mai kyau ki dafa shi da ruwa sannan ake kuskure baki da wannan ruwan lallen, zai gusar da matsalar warin baki, Insha Allahu. Amfanin wannan hadi bai tsaya iya nan ba, domin kuwa ya na maganin ciwon hakori da tsatsarsa.
Idan kuma ana son a kara karfin hakora ne, sai a samu garin lalle da kanunfari da gawayi a hada waje guda sannan a dake su yadda za'a sami garinsu, bayan an sami garin sai a juri goge baki dashi yana kara karfin hakora sosai in Allah ya so.
9. Maganin Cin Ruwa Na Kafa.
Mutane na ganin cin ruwa karamin ciwo ne, sai dai duk mai fama da shi ya san ciwo ne mai matukar takurawa, musamman yayin tafiya ko hana mai fama da shi sanya wani nau'i na takalmi sannan ga fama da ciwo duk lokacin da aka fama shi, yayin wani motsi ko wajen alwala. Ga duk mai fama da wannan matsala sai ya kwaba lalle da ruwan kal ya sanya a wajen ciwon.
10. Gyaran Jiki
Shi wannan ya banbanta da gyaran fata. Wannan wani hadi ne dake dawwamar da jikin mace cikin kamshi. Saboda haka idan mace na son jikinta ya kasance cikin kamshi a kowanne lokaci sai ta yi wannan hadin.
Ki tanadi lallenki mai kyau, sai turaren ruwa dan duri, ki zabi mai kyau wajen dadin kamshi gwargwadon bukatar. Kafin ki shiga wanka sai ki zuba isasshen ruwa a baho ko bokiti ki zuba garin lalle a ciki har sai ya jika yay já zir sai ki tsiyaye ruwan, sannan ki zuba turaren ki mai kamshi cikin ruwa. Zaki shiga bayan gida da wannan ruwan mai kamshi, da zarar kin gama wankan sabulun sai ki dauraye jikinki dashi. Matukar ki ka lizimci haka, ba shakka jikinki zai kasance cikin kamshi da'iman, Idan Mai duka Ya yarda.
11. Maganin Kurajen Fuska (Finfus).
Wadannan kurajen fuska da ake kira, 'Finfus' wasu kuma na kiran su kurajen balaga, na da matukar sanya rashin jin dadi saboda su na bata fuska, musamman fuskar matasa maza da mata.
Domin samun waraka daga wadannan kuraje, sai a samu lemon tsami a hada da garin lalle a kwaba, sai dai ba'a son ya yi ruwa-ruwa, an fi bukatar ya yi dan tauri kadan. Za a juri shafa wannan hadi a fuska, za a rabu da wannan kurajen don kuwa za su mutu. Baya ga haka wannan hadi na gyara fuska ta wajen dusashe tabo sannan ya sanya haske da laushin fuska. Sai a gwada.
12. Maganin Warin Kashi.
Wadansu mutanen sun samu jarrabawa daga warin kashi, abin nufi da zarar sun shiga cikin jama'a sai ka ji jikinsu na fitar da wani wari marar dadin shaka. Su kan su dake fama da wannan matsala ba sa jin dadi, hakanan kuma suna takurawa jama'ar da su ke mu'amala da su.
Saboda haka an tabbatar da cewa, lalle na maganin warin kashi da ke haifarwa mutane wari da tsami. Yadda za'a magance wannan matsala shine, sai a dafa lalle, a tace ruwan. Bayan ya kammala wanka da sabulu sai ya sake wanke jikinsa da wannan ruwan lalle, za a rabu da warin kashi idan Allah ya so. Ko kuma duk mai fama da wannan matsala ta warin kashi ya yi amfani da hadi na 10 dake sama ya lizamci wanka da shi.
13. Daidaita Jinin Al'ada.
Yawaita yin kunshi da lalle mai kyau musamman a kafa yana budewa mata kofofin jini, musamman ga matan da jinin al'ada ya ke yi mu su wasa. Ba shakka matukar mace za ta dimanci kunsa lalle a kafarta, to bi iznil Lahi za ta samu waraka, saboda an jarraba ba sau daya ba, ba sau biyu ba, kuma an dace da samun kyakkyawan sakamako
Post a Comment