Abubuwan Da Yakamata Kiyi Domin Kulawa Da Farjinki A Lokacin Zafi

 Abubuwan Da Yakamata Kiyi Domin Kulawa Da Farjinki A Lokacin Zafi



A wannan lokacin zafi maccen da bata kulawa tana rage ni'ima da kuma karfin sha'awa, a saboda haka akwai abubuwan da yakamata ki kula da su domin gujewa wannan matsala. Da farko dai ki kasance mai saka pant mai tsafa kuma kada kina saka mai kauri. Na biyu kada zafin yanayi ya hanaki yin tsarki da ruwan dumi. Na uku kada kina saka ragga ko wani abu sosai a ciki 


Bayan wannan kuma ga wasu abubuwan kulawa a wannan lokacin zafi

Kamar yadda mutum kan ji zafi ya nemi ruwa mai sanyi ko kuma ya nemi wuri mai inuwa ya kwanta a wannan lokaci na zafi haka wasu dabbobi da kwari kamar su macizai, kunamu, tsaka da sauran su ke fitowa domin samun dan ni’ima.


Wasu masana kiwon lafiya sun bayyana cewa a wannan lokaci na zafi mutane sun fi kamuwa da cutuka kamar zazzabin cizon sauro, saran maciji, kunama da makamantan su.


Masanan sun ce kamata ya yi duk lokacin da aka shiga yanayi na zafi a wayar wa mutane kai na yadda zasu kiyaye da ka kamuwa da irin wadannan cutuka kamar haka:


1. A daina barin tagogi da kofofi a bude ba tare da a na kula da duk wani mosti ba. Za a iya saka murfin kofa mai raga, kafin ainihin kofar shiga saboda kiyaye wa.


2. A tabbatar an duba rassan itatuwa da kuma tarin ganye dake karkashin itatuwan da suke domin macizai za su iya zama a irin wadannan wurare.


3. A tabbatar ana tsaftace muhalli ana rufe kayan abince don guje wa kamuwa da cuta.


4. A yi amfani da maganin sauro domin gujewa kamuwa da Zazzabi.


5. A yawaita shan ruwa.


6. A kula da tsaftace yara.

Post a Comment

Previous Post Next Post