Maganin Amosanin Baki Dana Infection

Maganin Amosanin Baki Dana Infection 


_Assalamu alaikumu MlM  Maganin amosarin Baki,nakeso agayamin amma Irin mai kama bakinnan


AMSA

_Wa'alaikumussalam warahmatulla...

_akwai amosanin ciki wanda kan rikide daga karshe yake komawa warin baki ga mace ko namiji.

_Hakan bakaramar baraxana yakan haifarwa wurin duk wanda yake dauke da wannan larurarba.

_Dankuwa yakansanya adinga kyarar mutum ko kuma yi masa kallon wanda baya kula da tsaftar bakinsa.Wanda axahirin gaskia ba hakan bane ciwone wanda babu yadda mutum ya iya.

_Don haka duk wanda yake fama da irin wannan larurar ta amosanin ciki ko nabaki sai yanemi⤵

MAGANIN AMOSANIN BAKI

A nemi

_KANUMFARI kamarguda bakwai [7] daidai lokacinda xaki kwanta barci kidinga taunawa kina hadiye ruwan.


_Kokuma kinemi man kanumfarin kidinga shan karamin cokali kafin kwanciyar barci.

_Insha Allah xai rabu dawannan matsalar.


_A samu zuma tatacciya mai kyau mara hadi a dinga brush da ita safe da yamma tsawon sati 2 insha Allah za'a rabu da warin baki.

Allah ta'ala yasa mudace

Post a Comment

Previous Post Next Post